Sashe 16
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
littafanta za tafara karantawa inna tadubeta ta ce "Ajiye littafin nan za ki yi ki kaiwa hajiya maijidda wamcan man shanun na soyashi tun daren jiya naso akai mata. Ta dan bata rai tace "nikam inna ba na son shiga wannan godan. Inna tarike baki tace "me mutanan gdan suka yi miki mutane masu kirki da mutunci wai ke meyasa ba kya son mutane ne fatima? Tace "ba haka bane inna kin sani duk abinda mutum yakeyi ana kallonsa idan ina yawan zuwa gdan karshe ace kwadayi ne yake kaini. To a fada din mana "inna tafada a fusace sannan tadora da fadin "idan har za kibiyewa surutun mutane ba abinda za ki aikata a rayuwarki dan duk abinda ka aikata din mutane ba fasa magana za suyi ba. Fatima ta dakko hijjabinta tasa ta dauki bokitin man shanun tanufo gdan abba. Hannu bibbiyu mama ta amshe ta suna zaune ita da ummi a falo suna hira, ta tsuguna ta gayar dasu tamika mata bokiti tace "Gashi inji inna. Tace "Oh Allah sarki inna da hidima take na gode Allah saka da alheri zauna sai anjima kya tafi ke in kin shigo gidan nan sai kace ana korarki na rasa sanda za kisaba da mutane fatima. A haka ta dan zauna a darare sai kace akan kaya tazauna, ummi tadubi ta da fara'a tace "fatima kin iya kitso ko rannan naga na kan kanwarki Aysha tace ke kikayi mata yaushe zanzo ki min irinsa? Tace 'idan kin shirya yanzu ma sai in miki. Tace "yawwa kamar kin san kan yadameni da yawa ina kuiyar saloon, tadkko kibiya da mai da komi tace "xo mu shiga daki kimin ma yi hira ma. Mama tayi murmushi tace "Ayi hira ko gulma idan ba gulma ba me zai hana a yi kitson a nan falon sai an shiga daki. Ummi tace "mama wannan hiran ai ta sirri ce. Tace 'gulma dai knan. Fatima na mamakin jin dadin da ake a wannan gida ita kanta ummi ace an shirya mata kasaitaccen daki irin wannan, tfara mata kitso suna hira tana ba ta labarin makarantar ta wadda saura shekara daya ta kammala, ummi tace "fatima amma idan kin gama za kici gaba da karatunki ko? Tace "a'a aure za ayi min in barda ma inna ta so inyi candy ai da yanzu anyi bikina da malam musbahu. Ummi tace "ba dai malamin ajinmu na islammiyr yamma ba. Tace "shifa ai dan gidan mu ne. Ummi tasake kallon fatima tana rayawa a zuciyarta yaya za ayi yarinya tanada kyau na garari irin wannan takare gun wani malamin islamiyya.,kwata kwata fati ba ajin malam musbahu bace, domin kyaunta yasa wasu har ce mata suke beauty, dukda cewa ba ta da sakin jiki da mutane ba ta ayyanar da tsabar kyaunta ta fi zama da nikab a fuskarta amma dukda haka kallonta ake ana zuzuta kyaunta, sbda zahiri Allah yayi mata kyakyawar sura tadaukar hankali da ace fati irin wayayyun 'yan matan nan ne masu budaddan ido ba karamin kudin maza zataci ba sbda in dai batun kyau ake fati ta fi gaban kwatance abin sai wanda yagani, ita kanta ummi aduk sanda tadubi fatima ji take kamar takwace kyaunta, tabbas ace tanada kyaun fati khalifa bai isa yace ba ya sonta ba, hankalinta bai kara tashi da fati ba sai watarana dataje gdansu fatima ta isketa ba dan kwali ta fito daga wanka tana taje gashin kanta, ummi taga yadda bakin gashin nan ya kwanta lanban a bayan fatima yana daukar ido kamar irin yammatan indiyawan nan, ga kirar jikinta abin sha'awa irin wadda ake cewa coca cola shape, ita kanta ummi datake mace saida taji tanason fatima sbda kyaunta kyaunta yayi mata ga tadai yar talakawa ba wani kayan ado dazai fiddo da itatake samu ba hakanan ta ki tawayar da kanta ,duk da haka fati ta isa abar kallo, kyaunta gdan wani hamshakin maikudi inda za ta jiku da jin dadi lallai za ayi kallon mace anan. Bayan ta gama mata kitson ummi taja hannunta zuwa kan dressing mirror tarike kugu tana kallonta tace "fatima kinga acikin kayan kwalliyarmu mata babu nau'in kalar da babu anan na baki dama ki zabi duk abinda kikeso wanda za ki dinga kayatar da kanki dashi gun ado, don Allah fati ki sani jikinki domin inason kizamo wayayyar mace mai ado za ki zama abar kallo fati, Allah ya yi miki baiwar kyaun sura wadda duk wata diya mace za taso ta mallaki sura irin wannan, dan banga abinda kika rasa ba fatima. Fatima tace "Nagode ummi da kaunar da kike nuna min, sai dai ina son kiyi hakuri ba zan dauki komi ba anan dan idan nadauka narabaki da abinki ba zan yi amfani dasu ba. Ummi tagyada kai tace "fati na fahimci kyamar dukiyar nan gdan kike yi. Fatima tace "haba ummi kada kiyi min muguwar fahimta mana. Ta tareta dasauri tace "me zai hana in fadi haka ba muguwar fahimta bane gskiya nafada miki. Ta girgiza kai tace "kiyi hakuri ba haka bane. Tace "to in dai ba haka bane zan hada miki kayan kwallia dakaina dan Allah kidaure kidinga amfani dasu. Tayi dariya tace " to na ji ummi amma dai zan tunasar dake abu daya wanda kwalliya ana yinsu ne dan afita kinga dai ni babu inda nake zuwa in banda makaranta,kuma ba wasu maza ke zuwa guna ba kinga dai ba su da amfani a gareni. Ummi tace "to in banda abinki fatima shi malam musbahun ba ya da bukatar yaga kwalliyarki, gskiya kanki a duhu yake dayawa kibani hadin kai in wayar miki dashi kada kiyi aure a cikin wannan yanayin dukda kasancewar malam musbahu malami ne amma xa ku iya samun matsala acikin zaman auranku idan kika cigaba da tafiya a wannan tsarin na ki, namiji dakika ganshi ko wani iri ne yana bukatar matarsa tayi masa ado yana bukatar matarsa takasance wayayya mai iya lura da abubuwa na jan hankali, idan akace mazan suke waje kadai za ayiwa ado banda na mazajen aure hakika kwalliya bata biya kudin sabulu ba knan, mace in har ta amsa sunan mace to tattalin rayuwar mijin auranta take domin shi ne na ta, wata kila kina ganin misbahu malami ne kuma dan gdanku ne ba ya bukatar sai kin masa wata kwalliya ta jan ra'ayi, wannan kuskure ne idan ma ra'ayinki ne haka to kisauya domin misbahu namiji ne kamar kowa rayuwar da zakuyi ta aure tanada banbanci mai yawa da wadda kukayi a gida, dole sai kin ajiye wannan kunyar da kke fama da ita domin tuni na fahimci kunya itace tahana ki sakin ranki ki zama wayayyiya mace, idan nace wayewa ba ina nufin kizamo mara kunya ba a'a kizamo mai wayewa ta fuskar rayuwa, matukar baki bin wannan hanyar dana ke son doraki a kanta ba, za kisamu matsala ba za kiji dadin zaman auran ba. Fatima tayi shiru tana tunanin abinda ummi tafada mata, ummi taci gaba da fadin "kiyi nazari sosai za kiganoinda nasa gaba, kinada kyau fatima kyaunki kadai ya isa yamallaka miki da namiji to amma fa masu iya magana kan ce in kanada kyau ka kaara da wanka,, dan Allah kisaki ranki da misbahu kidinga tsala ado sosai kina tsayawa kuna hirar soyayya za kiga yana dada rudewa akanki, a tunanina babu wani abun Burgewa ga mace wanda yawuce mijinta na aure yayi ta sonta ya kasance kullum hankalinsa na kanta, matukar kuwa bata bi hanyoyin dazata rike shin ba ba zata samu yadda takeso ba daganan sai kiga anata samun matsalar rayuwar aure a dalilin a dalilin hakan za kiga aure ba ya danko kiyi taganin kananan zawarawa a gari, wadannan abubuwan da matan mu na hausa ba sa kulawa dasu suna taka muhimmiyar rawa gun lalacewar zamantakewar aure. ****** A DAREN FARKO 13 Har fatima tadawo gida tana tunanin maganganun ummi wadanda suka jefata a wasi wasi amma tana karfafa kanta dacewa gaskiya ne mamakinta shi ne yadda ummi tasan wadannan abubuwan ba tare da ta yi rayuwar auren ba ballantana tasan matsalolinsa da abubuwan da ke haifar da matsalolin, koda yake kallo daya inkayiwa ummi za kasan kanta a waye yake sosai ta fuskar rayuwa haka karance karancen datake na littafin hausa suna taimaka mata sosai nagano abubuwa da dama da suke ckin rayuwar auren. Fatima na zaune a dakin da suke kwana ne a wannanlokaci da bai wuce karfe takwas na dare ba sallar isha'i ta idar tadauko kayan da ummi tahada mata na kwalliya tana dada kallonsu har da kayan sawa materail ne kala biyu da mayafinsu da fashions da agogi ga turarruka har kala uku, kuma taroke ta idan gari yawaye tadawo daga makaranta tazo zata rakata saloon u gyara mata gashin ta, a dazun da wayo da wayo sai da ummi taja hankalin fatima takai la'asar a gdansu tana cusa mata maganganu na jan ra'ayi don dai ta samu ta aminta da maganganunta har sai da taci nasarar da fatin tasaki jikinta take ba ta labarin yadda shi kansa malam musbahu yake nacin son tadinga sakin jikinta suna hirar soyayya tadaina gudunsa, tace wani lokacin har tausayi yake bata idan yafaye mata magiyar tayi mai hirar soyayya ko kaka ne dan yaji sanyi a zuciyarsa, amma ina tsabar kunya yasa ba ta iyawa, ko hada ido ba ta yi dashi, ummi tace "kinji ko ? " Tace "wannan idan baki bar wannan halin ba idan anyi auran yagaji zai dinga kula wasu yammatan ko yadaina baki kulawar dakike bukata kema. Lokacin data dawo gida innarta rike baki tayi tace "Tabdijam kece kika yini yau a gdan hajiyar ? Tace "uhm ummi ce tatsareni da magana kinga kayan ma data ba ni. Inna taduba tayi godiya. Fatima ta san cewa ummi na kaunarta kawai don Allah, don haka tasaki jikinta da ita sosai tana kokarin kwatanta abinda take gaya mata, tadaina dari dari da ummin zama take suyi hira sosai tazamo tazamo kamar irin aminan nan dasuka jima da shakuwa da juna, ita kanta fatin ko dayaushe idan takalli irin alherin da ummi take mata da yadda tadamu da ita tana nuna mata tsantsar kauna sai ta dinga mamakin kaunar da take mata, yakasance ko yaushe ummi na gdansu fatima