← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 50

Sashe 41

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zuciyar Dr. khalifa da son fatima sai dai mutuwa idan ransa yabar jikinsa amma ba dai wani boka ko malam ba. A DAREN FARKO 34 Abokansa suka tsare su dtambayar ina amarya tunda an ce tana gdan dole suna son ganinta, khalifa ya marairaice fuska yace "to ya zanyi !? Mama ta yi ruwa ta yi tsaki ta ce fatima ba za tazo dakin nan ba, ni ban taba ganin irin wannan tsarin ba mutum da matarsa a dauki ido a dora mai ko kallon fatima nayi mama sai ta hau fada na rasa dalili bata san jin zuciyata nake kamar za tafashe ba idan tana hanani ganin mata ta. " Wani a cikinsu mai suna Nura yace "Ai mama tayi min daidai sanin halinka ne yasa tayi ma haka,idan aka kyaleka za ka iya kwana da fatima a dakin nan da safe kuma kayi mirsisi kana kallon idon mutane. Khalifa yakara fusata yace "Kai da Allah kar ka dada batan rai haramun ne dan na kwana da matata. Dr. Bashir yabushe da dariya yace "Wannan ihu ne dai bayan hari in ka isa katafi dakin mama kayi mata wadannan fadace fadacen karshe tace sai bayan wata uku za a kaima amaryar in ga kuma yadda za kayi. Khalifa yayi dariya yace "Tabdijam ai kuwa da na basu mamaki nima in ga yadda za ayi dani. Nura yace "Uhum ka bisu dai a sannu idan kai baka ba su mamaki ba su subaka mamaki. ***** Mama tayi tsayuwar daka gun gyara amarya da abubuwan da za sukawo mata ni'ima a jikinta, ita dai burinta hankalin danta yakwanta,. Fatima ta cika ta batse ta kara wani irin kyau kyaun ma mai ban sha'awa, tayi fresh babu abinda ke damunta. Mama ta hanata fita ko ina don kar ta shiga dakin khalifa sai dai shi in ya shigo su gaisa iya fali. Ya yi fushin ya yi mitar har ya gaji ya zuba ido shi kadai yasan damuwar da yake fama ita a zuciyarsa, a ranar da fatima tayi kwana biyu a gdan ana ya jibi za a kaita gdan Dr. Khalifa aka kai kayan lefenta gdansu, lefen da aka dinga surutun karya tayi yawa, wannan ai almubazzaranci ne da dukiya kamar ba masu neman taimako da za a kashe dukiya irin wannan a lefe,? Abinda 'yan'uwan abba sukayi ta fada knan, daga bisani wannan yazamo ba abin surutu ba lokacin da aka kaisu ganin gdan dr. khalifa da fatima za su zauna wanda yake court road, da irin kayan alatun da aka dankara a gdan abin sai ya wuce ayi magana da baki sai gani da ido, duk wani abinda za a kawata gda dashi a kalla asan ya yi kyau sai da akasa a cikin wannan gda, komi ya kammala amarya kawai ake jira. Washegari ranar asabar wanda yakasance saura kwana daya akai fatima gdanta tatashi da ciwon kai abisa dole mama tace khalifa yashiga dakinsu ya dubata, shi bai ma san ba ta da lfya ba svda hushi yayi yadaina shiga harkar mama da ita kanta fatin, idan ma yashigo falon ta gayar dashi fuska a tsuke yake amsawa sbda ya gaji da jan ran da ake masa kawai don an ga ya damu. Lokacin daya shiga falon suka gaisa da mama yawuce kan tebur zai ci abinci ta dubeshi tace "Yau baka tambayi matar ta ka ba. Ya dan tabe baki kamar bai damu ba yace "Oh tana ina ne ? Tace "Tna daki ba ta da lfya. Yaji wani irin abu ya dakar masa zuciya duk da haka yashare bai bari mama ta fahi ; ci halin da zuciyarsa tashiga ba, yayi zamansa yafara tsiyaya tea a kofi yana fadin "Me ya sameta ? Ta amsa "Tashi tayi da ciwon kai da amai idan kagama kashiga kaduba ta. To kawai yace yaci gaba da cin abincinsa, da ya gama din ma maimakon yashiga dakin au fatima sai yadauki hanyar fita. Mama tace "Ba za kaduba fatiman bane ? Yace "Af har na manta. Yamurda kofar dakin tana kwance bisa gado nannade da bargo, idanuwanta a rufe, yazauna kusa da ita yayaye bargon data rufe, ya taba wuyanta zafi sosai, yace "Subhanallahi. Nan da nan yaji tsigar jikinsa ta kama tashi, yakira dr. hafiz a waya ya gaya masa irin magungunan dazai aiko masa dasu, yafita dan yadan hada mata abinda za taci sbda allurar da zai mata. Mama tace "za su fita da anty sadiya yanzu za su amso dinkunan fatima tunda ba kowa a gdan yazauna yalura da ita. Zuciyarsa tayi mai fari kal 6au ya sami dama amma sai yadan kanne yaduba agogo yace "Da fita zanyi kuwa. Tace "Kadan jira mudawo bai dace a barta gda ita daya ba sai 'yan aiki alhali ba ta da lfya. Bayan fitar su mama yahada mata shayi ba madara yazuba mata dankali shi kadai yanufi dakin, yazauna gefen gadon yajawota jikinsa yana lallabata kamar kwai yarungumeta yana bata shayi tana dan sha a hankali tace ita dai ta koshi. Wata daga cikin ma'aikatan asibitinsu dr. hafiz takawo magungunan yabata tasha yayi mata allura guda daya tana zuba shagwabarta yadda taga dama, hankalin khalifa yakara tshi zuciyarsa ta tsimu komi na jikin fatima ya bayyana a gareshi, domin wasu riga da siket ne a jikinta marasa nauyi takara zama fara kal, ko idanunsa bai iya daukewa a kanta ba, itama tana son tadinga kallonsa duk da tanajin nauyinsa, ganin ya fara shafa mata cinya da ciki yasa tadan janye jikinta ta matsa, yayi narai narai da idanuwan nan na sa yana mata wani irin kallo mai daga hankali. Yace "Haba fatima kin san matsayinki a guna bai dace ki biyewa mama kina wahalar dani ba, wai ace fatima tsakanina da ke sai gani da ido daga nesa,. Ni fa mijinki ne ina da hakki akanki ko kin manta ne ? Doguwar ajiyar zuciya tai tace "mama ce ba ta son in zo gunka nikuma ba zanyi abu ? da zai bata mata rai ba. Yace "ai dama ba cewa nayi ki bata mata rai ba, amma ya dace ace ko da daddare ne kina dan fakar idonta kizo dakina kitayani hira ki debe min kewa tunda kin san dole ina fama da damuwa a zuciyata ko ? tunda kika dawo gdan nan dazama kullum dare ba na iya barci sbda kewarki fatima, ina son ko kakane in dinga jin dumin jikinki, ko rungumarki nayi na miki kiss ai zan ji dadi a zuciyata ko ? Amma ke ba ruwanki sai ki biyewa mama ki shareni sai dai in shigo in ganki kyaunki na karuwa zuciyata tayi ta fama da kewarki ya kamata ki tausaya min Fatima. Ya kamo hannunta yakara janta jiki ? sa yarungumeta sosai yaci gaba da cewa "Wallahi fatima ina sonki son da ban taba zaton zan ma wata diya mace a duniya ba, sbda kafin ke ba zan iya tantance miki meye soyayya ba, nidai nasan ina mu'amula da mata amma ban taba damuwa dawata diya mace ba saida nafara ganinki nadin ga jin tamkar zan mutu idan ba na tare dake, duk wata natsuwa takan gushe mini idan ban ganki ba, shi yasa na rikice na gigice lokacin danaga katin daurin auranki da musbahu, Fatima idan ciwon sonki ya tsananta a zuciyata sai in dinga jin kamar ba zan yi doguwar rayuwa dake ba, fargaba takan kama mini zuciya in rasa yadda zanyi da raina, fatina dan Allah,. Yayi shiru yakasa cigaba da magana. Tausayin sa yakamata sosai taji ciwonta ya sauka gaba daya babu abinda ke gabanta sai khalifan tadinga jin wani so da shauki yana ratsa mata zuciya kamar yau ne tafara sanin khalifa, a wannan lokacin da kanta tasa hannayenta biyu tarungumi dr. khalifa kam kam a jikinta tana hawaye. Yasa harshensa yadinga lashe hawayen na ta yana fadin "fatima, fatima kukan me kikeyi. Ta tura bakinta cikin kunnuwansa tace," kukan farin ciki ne kada yadameka. Yadda tayi mai shima haka yayi mata yace "Farin ciki kala kala ne fatima don Allah fassara min yanayin farin cikin daya sa ki kuka. Tace "Babu wani farin ciki ga masoyi wanda yawuce mai sonsa ya soshi, hausawa kan ce son maso wani koshin wahala ne, idan mutum yana son wanda ba ya sonsa ya gamu da wahala idan kuwa mutum yana son wanda yake son sa yana ckin farin ciki da kwanciyar hankali, a yau ban san wanda yafini farin ciki ba shiyasa nake kuka. Khalifa yayi murmushi yace "Allah sarki ashe in dai hakane za kiyi ta kuka tunda ni yanzu nafara nuna miki so da tattali har zuwa ranar da Allah (SWT) zai karbi rayuwata. Fatima ina fatan Allah yasa in mutu in barki sbda nasan insha Allahu za kiyi tamin addu'ar neman gafarar Allah. Bayan haka ina jimantawa kaina halin da zan shiga idan na rigaki mutuwa, mutuwata sutura ce a gareni idan yakasance kin mutu fatima don Allah ki dinga yi min addu'a. Ta katse shi ckin damuwa tace "Don Allah kadaina batun mutuwar nan haka. Yace "kyaleni in yi fatima duk mai rai mamaci ne duk yadda muka kai ga son rayuwar duniya sai mun mutu, tuna mutuwa shi kesa mutum yayi wa kansa hisabin ayyukansa yadinga sanin cewa zai hadu da Allah kuma zai ga abinda ya aikata me kyau ko kishiyarsa. Tace "To nidai na ji don Allah mubar wannan maganar. Yayi murmushi yace "Shikenan na barta, yaci gaba da dan latlatsa mata jiki har sai da yayi nasarar kashe mata jikin gaba daya ya kasance ba ta da wani kuzari, sai yadda yayi da ita, duk zazzabin da take fama dashi sai da taneme shi tarasa sai tsabar tsananin son khalifa da shaukin sa. Ya zare jikinsa yamike yasawa kofar key yakara rufe lavulayen dakin yayi dan duhu duhu, tsoro yacika zuciyar fatima ta tsahi zaune tana rokon don Alla ya taimaketa kada yayi mata wani abin, yace "kiyi hakuri kawai fatima nima ba na son yimiki wannan abin anan gdan sai a gdanmu amma a halin yanzu zuciyata ba xa ta taba iya hakuri ba, kada kijefa nin ckin fushin Ubangiji kisa in je in aikata sabon Allah, kada kijefa kanki kema ckin fushin Allah kuma kinsan matsayin matar datake gujewa mijinta. Jikin
Chapter 41 · 0% Book details