← Book details A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 50

Sashe 34

A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nake so, ba ina fadin hakan bane don a gabanku ne ina son shi ne kawai don shi ne ra'ayina na amsa wa iyayena auran musbahu a lokacin da ban san meye so ba, yanu na fahimci inda rayuwa ta dosa don Allah mama kutaimaka ku fahimtar da iyayena kada su dauran auran da ba na so xan iya shiga ko wani hali idan ban auri khalifa ba. Aka yi tsit dakin kukan fatima kadai ke tahi, ummi kallon iyayan khalifa da fati kawai take tana girgiza kai ta ji dadi da hawayenta basu zuba ba domin ta gaji da kuka lokacin kuka ya wuce a gunta illa neman mafita, son kai ba musbahu kadai ake naman yi mawa ba har ita gara ma musbahun da yake so ake kwace masa matr ana ta nanata yadda za ayi dashi ita kuwa ba wanda yadamu da damuwar ta idan ma mutuwa za tayi tayi ta mutu, wai fati ce ke kuka a gaban iyayan khalifa tana rokonsu ita dai tana son khalifa, takallesu gaba daya tagirgiza kai tare da cije lebe. Anty sadiya tace "mama kinga abinda nake gaya miki wai meye amfanin yin shirun da akayi alhalin an san halin da zuciyoyin yaran nan ke ciki. ya kamata ayi musu adalci, shi musbahu bai san aure nufi ne na Allah ba, a zaunar dashi a yi mas bayanin kudubi halin da khalifa ke ciki daga ganin fa katin daurin auranta yashiga wannan halin ina ga idan an wayi gari yasan an kaita gdan musbahu? Tagirgiza kai. Gaskiya mama a san abin yi kada fa azo ana nadamar da ba ta da amfani gara tun kafin lokaci yagama kurewa a yi wani abin. Abba yace "maganarki haka take sadiya tabbas a yau din nan zan bi hanyar data rage tarage don ganin ankawo karshen wannan matsalar wannan lamarin na khalifa ya fi karfin a sa ido dole a yiwani abin a kai. Kofar dakin tabude dr. mansoor yashigo tare da wata nurse a bayansa ya isa gaban gadon dr. khalifa yace "har yanzu bai farka ba. Abba yace "ai ko motsin kirki ba ya yi nifa in banda ina ganin numfashinsa da yanzu na ce khalifa ya mutu. Dr. mansoor yadaga hannun khalifa ya mayar ya ajiye, yadakko wata karamar na'ura yadaura mai akan kirji yana latsawa tare dasa wani abu a kunnansa, zuwa can yacire yajuyo yadube su gaba daya yakira sunan nurse din da ke tare dashi mai suna jamila yace "ki lura dashi sosai. Tace "ba damuwa sir. Yamaido ido ga abba yace"kuyi hakuri Alhaji insha Allahu khalifa zai samu lafiya ni yanzu xan tafi gida. Abba yace "haba dr.yaya za kace za ka tafi bayan har yanzu ko farkawa khalifa baiyi ba. Dr. mansoor yace "Alhaji kada kadarra cewa samun lfyar khalifa yana hannuna wannan hukunci ne na Allah,Allah yahore mana taimakon al'umma ta hanyar ilimi daya azurta mu dashi a bisa yardarsa muke yin komi ,nan da dan lokaci kadan likitan daya karbi aiki zai shigo yaci gaba da kula dashi, Allah shi ne me ba da lafiya, kafin dai in tafi inaso idan da hali ayi duk kokarin da za ayi a nemo abinda zai sanya khalifa farin ciki yayin daya farka ma'ana da zarar ya bude idonsa yakasance ya ga wani abu dazai faranta masa rai, wannan zai taimaka gun sanya natsuwa a zuciyarsa. Abba ya waiwayo yadubi fatima sannan yamaida kallonsa ga likitan yace dashi "ka ga wannan yarinyar? Dr. mansoor yadubi fatima dake tsugune gefe tana sharar kwallah abba yace "to itace yarinyar da khalifa ke so kuma iace silar fadawarsa cikin wannan halin. Dr. mansoor yace "Alhaji kana nufin itace fatima. Dasauri Abba yace "itace kuwa likita ina kasan sunanta? Yace "a jiya da kuka kawo khalifa lokacin da numfashinsa yafara dawowa bayan salatin Annabi da yayi sunanta muka ji yana ambata tun daga nan muka kaddara cewa a dalilin mace yafada ckin wannan damuwar, to tunda ga ta meye abin tashin hankali ba sai a bashi auran na ta ba kowa yahuta. Abba yayi murmushin takaici yana girgiza kai yace "Likita wannan yarinyar tafi karfin khalifa, kudi ba sa sayan mutum da ace kudi na sayan mutum ko nawa fatima takai sai na siyawa khalifa dan in rabashi da wannan damuwar dayake fama da ita, saura kwanaki biyu kachal awa 48 fatima tazama matar wani ban san halin da khalifa zai shiga ba, Inalillahi wa inna ilaihir raji'un. Dr. mansoor ya jinjina kai yace "gaskiyar magana abba tunda halin da khalifa yashiga ya kai haka to kanemi iyayan yarinyar nan ku daidaita magana su zo suga halin da danka yake ciki su taimaka kowa yataimaki wani Allah zai taimake shi, kada kabari wani ya auri fatima alhali khalifa na ckin wannan halin. Akayi shiru gaba daya har Dr. mansoor yafita bbu wanda yasake magana. A DAREN FARKO 29 Karfe daya daidai Abba yace zaije gida yayi wanka yayi sallah yadawo. Mama ta biyo shi har mota tana rokon yadaure yaci abinci. Ya dubeta da jajayen idon sa yace "cikin nawa ne bbu dadi tun dazun nake jin zuciyata na tashi kamar zan yi amai ga kaina na juyawa. Tace "kayi hakuri ka kwantar da hankalin ka komai na Allah ne, duk wadannan abubuwan dake fruwa idan Allah ya yi fatima matar khalifa ce zai aureta, za kaga yadda Allah zai juya al"'amarinsa daga damuwa izuwa farin ciki, babu abinda ya gagari Allah shi ne me yadda yaso a lokacin daya so, yayin da duk damuwar da za ayi da duk halin da za a shiga idan Allah bai kaddara matarsa bace sai dai mutari muyi hakuri muyi fatan alkhairi. Abban yadora kansa a kujerar da yake kai idonsa na kallon sama ,sun samu shiru daga bisani yace "Hakane sai na dawo. yaja motar ita kuma tadawo ciki. Tace "Fatima ku ci abinci kutafi gida ku huta don Allah ki daina yawaita wannan kukan ba zai yi mana maganin komi ba sai addu'a da hakuri. Cikin shashekar kukan tace "ni kam mama a idanuwa na ba za su taba daina zubar da hawaye ba sbda tashin hankalin da take ciki. Mama tace "kiyi hakuri fatima kada ki ja abin da za ki bata da iyayanki bayan a baya kuna zaune lfya kullum inna tana yabon halayyarki, iyaye suna da kima sosai a gun dansu in dai da yana son a gama da duniya lfya to yabi iyayansa, na tabbatar ba za su so ace ba ayi auranki da musbahu ba sbda shi ne xabinsu, hakan ba yana nufin suna kin khalifa ba, idan muka ce iyayanki ba sa son khalifa ba muyi musu adalci ba tundamuna sane da yadda al'amuran suke. Fatima duk da cewa ni na haifi khalifa na fi kowa jin ciwon da tashin hankali halin nan dayake ciki, idan a son raina ne izuwa yanzu yakasance kina dakin khalifa a matsayin matarsa sbda son da yake miki kowa ya san bashi dawani farin ciki wanda yawuce ya mallae ki, yanayi ne wanda kowa yasan khalifa bai taba samun kansa a ciki ba, ai wannan dalilin ne yasa kowa yake tabbatar da son da yake miki na gskiya tun yana fada da baki har gashi yau a gadon asibiti bai san waye a kansa ba, to amma duk da haka ba zan rufe ido a kan abinda ba ma gskiya da adalci ba na hakura na zubawa sarautar Allah ido idan Allah ya yi khalifa zai rayi zai tashi, ni dai na san rayuwa cike take da jarabbawa iri iri, komi lokaci gare shi duk yadda tsanani ya tsananta insha Allahu akwai sauki da zai biyo bayansa, a ckin alkur'ani mai girma ma Allah (SWT) yana fadin, dukkan tsanani suna tare da sauki. A wannan lokacin fatima dora kanta tayi bisa cinyar mama tana kuka har sai da hawayenta suka jikawa mama zaninta, lamarin dayasa itama mama takama sharar da kwallah duk kokarin data dinga yi gun hadiye hawayenta tun safe abin ya ci tura, wannan karon kuka take sosai, sai anty sadiya da ummi ke basu hakuri. Mutmryar khalifa tasa suka mike gaba daya a rude suna kallonsa, idonsa yabude yana fadin "Lahaula wala kuwwata illa billahil azim. Gaba daya suka iso kanaa suna masa sannu. Bai fahimci a inda yake b kansa a rude yake don haka yamaida idonsa yarufe, rudewa tasa Fatima ta manta tana tare da mahaifiyar khalifa takamo hannun khalifa tana fadin "Don Allah katashi daga barcin nan ya isa haka. Kamar a mafarki yake jin muryar fatima, sai yayi saurin bude idonsa, ai kuwa fatin ce a kansa ya zuba mata ido har yanzu dai a tunanin sa rayuwar mafarki yake, yace "Fatima. Ta amsa "Na'am khalifa. Ya matse hannunta yace don Allah fatima kada ki auri wani ba ni ba mutuwa zanyi idan na rasaki, mafarki nayi wai na ga katin daurin auranki fatima bai dace ki yi min haka ba ko so ki ke in mutu? Ni kadai iyayena suka haifa, ko su ya dace ki tausaya wa. Fatima tarufe me baki tace "ka kwantar da hankalin ka insha Allahu za ka mallakeni kasan nima ina sonka. Bayan khalifa ya yi sallolin dake kansa yana zaune kan darduma fatima thada mai ruwan shayi shi kadai yace zai iya sha gaba daya jikinsa yayi sanyi kallon kowa yake kadan kadan yake iya bude idonsa, kowa yazamo dan kallo, fatima ce ke da bakin magana a gun, shayin ma ita ta matsa masa tace sai ya sha gudun kada tayi masa hushi yasa ya hakura zai sha, amma bbu abunda yake sha'awa. Kofar dakin tabude, abba da malam musa mahain fatima da musbahu da inna suka shigo. Fati tatashi zumbur daga gaban khalifa domin zaune take sosai a gaban na sa tana rokon ya daure ya dan ci abinci ko kadan ne, kunya ce takamata sosai musamman ganin kallon da iyayanta ke mata duka fuskokin su ba walwala, ballantana musbahu wanda yake jin kamar ita kanta fatin ya shaketa kowa yahuta. Bayan sun gama gaisawa da tambayar jikin khalifa, musbahu yadubi malam da Abba yace "Don Allah ku yi hakan baba a kawo karshen wannan damuwar a yau, har abada hankalina ba zai taba kwanciya ba idan ya kasance dan uwana musulmi yana
Chapter 34 · 0% Book details