Sashe 6
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
fatima.. Fati tarushe dakuka mai tayar da hankalin mai imani tace "kaicon rayuwata na yi nadamar zuwa wannan duniya ace an wayi gari a rasa wanda zai kashe Dr. khalifa sai ni ni fatima me xanyi da rayuwa.. me zan tsinta a cikinta, wane farin ciki zanyi a gaba? Don Allah kudaina yun'urin kareni kuyarda ni nakashe Dr. khalifa a kashe ni in huta da wannan ba'kin cikin rayuwata ba ta da amfani. Wannan bayanin da nayi iyakarsa zan iya fd'a ba zan ta'ba bud'ar bakina a kotu ince wani abu ba game da ranar da dr. khalifa ya bar duniya, hukunci kawai nake jira kuyi ha'kuri kuyafe min. Barristr Abbas yace "to shikenan munji ke kika kashe Dr. khalifa gaya mana meyasa kika kashe shi? Ta amsa "ni ma bansan dalilin dayasa na kashe shi ba. Ba wani laifi dayayi miki? Bai min komi ba sai alheri, ba komi tsakanina dashi sai alheri, ban sani ba ko alkairin ne yasa nayi masa sakayya da kisan kai. [5:08PM, 7/13/2017] +234 706 196 7803: DAREN FARKO 5 TSAKIYAR dare ne za mu iya kiran lokacin 'karfe biyu da rabi nadare, fatima na zaune kan dandayyar siminti ana muku mukun sanyi ne a lokacin amma ita ta ji'ke sharkab da gumi sakamakon matsanancin halin tashin hnkalin da gararin darayuwarta ke fuskanta. Ita kanta yadda alamuran suka faru suna matu'kar ba ta mamaki, koyause tambayar datake wa kanta itace waye yakashe Dr. khalifa? Me yayiwa wanda yakashe shi? Meyasa ba'a kashe shi ba sai a daren su nfarko A DARAN FARKO na amarcinsu aka biyo shi har cikin gida akan gadonsu aka kashe shi, tabbas duk wanda yakashe Dr. khalifa ya isa azzalumi, ita da Dr.khalifan ne baya so shi yasa aka kashe shi a sigar da duk wanda yagani zaice itace takashe shi. Ita da Dr. khalifa mesuka yiwa wani daya daidaici irin wannan dare a gunsu yakashe mata miji? Wannan itace tambayar datake wa kanta tun lokacin da aka kulleta a wannan guri, itace tmbayar da ciwon dayake mata a zuci ke barazanar sa zuciyarta tabuga ta tadda mata ajalin sbda tsananin damuwa, Allahu akbar ashe ko kwana d'aya ba za tayi a gidan miji ba, bala'i zai fad'a musu A DARANSU NA FARKO. Sai kace ana tariyo mata rayuwarta da abinda yagudana a tarihin rayuwarta gaba d'aya haka yarin'ka wanzuwa a zuciyarta da 'kwa'kwalwarta kamar shirin fim. *******************************,****** Malam haruna shi ne mahaifin malam musa wanda yakasance shi ne mahaifi ga su fatima. Asali malam Haruna bafullatanin gombe ne yawon neman karatu yakawo shi kano kasancewarsu fulani ne na jame inda yazauna a hannun wani shahararran malami mai babbar tsangaya anan kano, Allah ya yi malam haruna mutum ne mai tsananin ha'kuri da biyayya malamin nan da iyalinsa suna matu'kar jin dad'in zama dashi inda a sanadin haka ne suka d'au d'iyarsu Maryama suka ba shi auranta ita kuma tahaifa masa 'ya'ya maza har bakwai, malam musa ne autansu. Bayan rasuwan malamin, malam haruna shi yazamo magajinsa don duk acikin almajiransa na wannan lkcin ba wanda yakaishi sha'kuwa dashi, ga kaifin basira yaci gaba da jagorantar tsangayar kuma shi yari'ke iyalan malam har zuwa shima lokacin da Allah (SWT) ya kar'bi ransa sai d'ansa malam musa yagajeshi a lokacin ma bai dade da auran fari ba inda matarsa zainab tafito itama daga zuri'ar tsohon malamin marigYi malam Yakubu, an ce na ji dad'i shi ne gari ba na saba ba. Malam musa yayi kyakyawan gadon hali na hakuri datsananin juriya irin na mahaifinsa, mutum ne mai matukar saukin kaida sanin yakamata, hka itama matarsa zainabu bbu abinda yadameta da zafafawa kanta game da rayuwar duniya. Suna zaman su lfya a dan karamin gidan da yake haya kusa da makarantarsu basu dogara da kowa ba sai Allah mutane ne dako kadan va su da kwadayi, mutanan unguwar sunajin dadin zama dasu sosai ana zaune lfya. Aliyu shi ne d'a na farko da goggo Abu tafara haifawa malam sai mai sunan malam Yakub suna cewa dashi malam, sai rukayya sai fati sai mai sunan malam Haruna suna cemasa baban gida sai muhammadu nazifi sai nuraddeen ba su da wadata da dukiya rayuwa ce tarufin asiri amma akwai wadatar zuci da son juna, rayuwarsu tana yawan ba wa mutane sha'awa yadda suke kamun kak da tarbiyya da girmama jama'a da 'ya'yan gidan masha Allahu hka suke amma ba kamar fatima, itace tafi fad'a kowa d'auko halayyar mahaifinsu kamar yadda tafi kowa kama sak da mahaifinsu don hkane tafi kowa kyau a gidan. kaf zuri'ar marigayi malam haruna kyawawan gaske ne har kwatance ake dashi a garin sbda kyaunsu ga uwa uba farin jini dukda cewa ba masu kud'i bane ba su da komi sai rufin asirin Allah. Tun fati tana 'yar mitsitsiyarta ake mata shaidar hkuri dasau'kin kai duk inda fatima tashiga sai an yaba halayyarta, balletana biyayya ga iyaye wad'anda takeji kamar tayi musu numfashi don tsananin so da 'kauna ko kuma takwanta sudinga bi ta kan ruwan cikinta don biyayya. Hka a makaranta malamanta ke ji da ita bayan maida hankali akan karatu da gudun fitina ga biyayya da tsafta. Fatima kyakyawar gaske ce daga ganinta ka ga bafulatana sak zai wahala mutum yagaji da kallonta sbda Allah ya yi mata baiwar kyau mai tsayawa a zuci. Bayan auran yayarta rukayya da shekara biyu wata rana da daddare malam musa yana zaune kan tabarmarsa goggo Abu tana gefe itama kan tata tabarmar yayin da fatima ke zaune kusa da su tana yi masa firfita. Yace "zainabu yaya batun d'an gidan rukayya ya warware ko? Ta ce "Alhamdulillah jiki kam dasau'ki yau danaje na iske shi yanata wasa da yara. Yace "Masha Allah, sannan yagyara zama yadubi fatima yace "fati yaya batun haddarki ta jiya kin haddace" Tace "na haddace har d'azun na ba da a gaban malam musbahu ya dad'a min wani. Yayi murmushi yace "Alhamdulillah yana daga cikin ni'imar da Allah yake yiwa mutane shi ne yabasu 'ya'ya na gari salihai wad'anda zasu zamo farin ciki a gareka, fatima ina matu'kar alfahari dake sbda kinada hankali da biyayya ban ta'ba shakku akan biyayyar da kike mana ba wannan shi ne dalilin dayasa kai tsaye ko shawara banyi dake ba na daukeki nabawa malam musbahu auranki sbda na fahimci halayyarku ta zo d'aya. Shi ma mutum ne da Allah yahore masa ha'kuri dasanin yakamata tunda nake dashi bai taba aikata min wani abu na assha ba, sai dai ajizanci irin na d'an adam wanda yake kai mutum ga kuskure. Amma dukda hka ina neman yardarki, idan kin yarda ba wani abune mai girma agareni ba don ina da ya'kini da kwanciyar hnkali akan hakan, idan kuma kin ce baki yarda ba ma'ana ba kya son shi ina mai yimiki rantsuwa da girman Allah ba zan damu ba na san Allah ne bai 'kaddara musbahu mijinki bane shi yasa kika'ki amincewa dashi. Fatima kanta na 'kasa ta shiga shararar 'kwalla batace komi ba, malam yace "fatima kada wannan magana tad'aga miki hnkali balletana tajefa zuciyarki cikin damuwa. Cikin shashe'kar kuka fati tace "dole indamu baba ban ta'ba tunanin akwai watarana dazakayi tunanin zan bijirewa umarninka ba, har inada abinda zanyi wanda zaisa inyi gaban kaina ba tare da umarninka ba. Wlh idan har akwai watarana wadda za tazo in bijirewa umarninku ba na fata tarismeni ina numfashi a duniyar nan gara in mutu da in ganta sbda haka baba ba na bukatar ka kara neman yardata a bisa wani bu wanda kake nufin zartarwa a kaina. Na amsa malam musbahu hannu biyu biyu kuma zan yi masa biyayya bakin iyawa ta. Malam musa yagirgiza kai yace "Allah yayi miki albarka fatima, Ubangiji Allah yasa kigama da duniya lfya, biyayyar dakikayi mana Allah yasa 'ya'yan dazaki haifa suyi miki wadda tafita, dukda haka ina mai tabbatar miki dacewa hakkinki ne in nemi amincewarki akan auranki da malam musbahu kamar yadda nayi miki bayani a baya ba wai dan ina shakkun amincewarki a gareni ba sai dan in ba ki hakknki a matsayina na mahaifinki. Yadda nake miki wannan magana haka na zaunar da musbahu nace dashi musbahu yau fiye da shekarar ka goma a hannuna tun lkcin dakazo da sassafe kana kuka kana ce min in taimakeka inje in ba wa kawunka hakuri matarsa ta yi maka sharri zai dake ka natambayeka abinda kayi mata kace min cewa tyi dashi na yi mata sata, malam musa yace "fatima a lokacin ne nasa musbahu a gaba har gidan kawunsa wanda yake bayan wannan layin na mu, kasancewarsa maraya, mahaifiyarsa ta rasu tun yana yayayye, yayin da mahaifinsa yarasu bayan shekara d'aya tsakani wannan shi ne dalilin dayasa kanin mahaifinsa yadaukeshi yabawa matarsa wadda ita kuma tadauki tsanar duniya ta dora masa, take wahalar da rayuwarsa. Abunda yasa musbahu yazo guna shi ne "lokaci lokaci kawun na sa yana zuwa dashi nan don daukar karatu da magriba kuma ya san akwai fahimtar juna tsakani na da kawunsa. Lokacin damukaje gdan nayi sallama da kawun yafito yana ganina tare da musbahu ya hau fada ko gaisawa bai bari munyi ba inda yake shiga ba nan yake fita ba, dakyar nasa yayi shiru nace "Alhaji Habibu ba haka ake lamarin duniya ba, idan mace tagaya maka magana saika bincika kafin ka dauki mataki, sha'anin mata idan akace ba su suka haifi d'a ba sai a hnkali ballantana d'an dayake maraya. Albaji habibu yace "duk abinda yagaya maka karya ne don ya ji Kawai ana cewa maraya ne duk abinda aka ajiye a gidan nan saiya sace yasiyar sannan idan nayi masa magana sai ytafi yana hadani da muatane ana cewa muna cutar dashi alhali shi maraya ne don ba mu muka haife shi ba. Ina dalilin wannan, haka kawai an ba ni ajiyar kudade masu yawa yabi dare ya bi rana har dakina ya sace, to ba zan iya ba yan sanda zansa sukama shi su kulle in huta ko kuma in kai shi gidan kangararrun yara ka ga na huta. Na dubeshi tsam sai da yagama fadace fadacensa nace"to ni kam ba zan bari kakai musbahu gidan kangararrun yara ba tunda shi ba kangararre bane, idan kai ba za ka iya rikon shi ba dan kawai ba kai kahaife shi ba ni zan iya, sai dai