Sashe 19
A Daren Farko Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tare da bukatar aure, alherinta yanada yawa a gareshi. Bai jima da fara zuwa makaranta ba yasamu aboki guda daya mai suna Faisal wanda yafito daga gda Nigeria jihar kaduna, Faisal tantirin matashi ne mai budaddan ido yadda khalifa ke da farin jinin yammata haka faisal yayi fice a wannan fannin, sa'ar da akayi shine faisal na da kokarin karatu, wannan shi ne dalilin dayasa khalifa yaji dadin abota dashi bayan haka faisal ba bako bane a kasar germany ya saba zuwa kuma yanada yammata da yawa, tun da suka fara abota khali:a yasaki ransa sosai ko yaushe suna tare sai lokacin barci suke rabuwa anan fa 'yammata suka fara kawo kansu ga khalifa, son karatu dayake yasa bai son su shiga jikinsa sosai don kada su shagaltar dashi. A yammacin jiya bayan sun kammala da makaranta wata budurwar khalifa mai suna shukura dasuke cewa 'shu baby'ta nace akan sai ta biyoshi gdansa yau dai ta tayashi kwana tace in kuma bai sonta yafito yagaya mata, yace "nikam ba na bukatar kwananki a gidana kiyi hakuri. Tace "ni na rasa dalilin dayasa kake min haka ko dai matar aure gareka a gdan. Faisal ya ja tsaki yace "ke ce kika kwallafa ranki kan wannan wahallaln ina mamakin dabi'unka khalifa har yaushe kanada matsayi irin wannan a rayuwa za ka takura kanka. Khalifa yace "faisal na fi shu baby bukatar ta a gidana ina kaucewa hakan ne sbda Anisa. "Anisa ? Faisal yafadi ckin mamaki. Ya amsa mai da fadin "Anisa mana, anisa ta cancanta in kaucewa abinda zai bata mata rai tana hidima dani sosai. Faisal yace "ka ga tunda ba ka iya debe kewar rayuwa da ita kasallameta daga gdan mana kadauki yaron gda wanda za ya dinga maka duk hidimar da Anisa ke maka tunda ba kudin dazaka biya karasa ba, yaya za ayi kazauna kana shakkar sakewa a gdan ka sbda Anisa, gskiya kasauya tunani. Tausayin anisa yakeji sosai a ransa shi kansa yana bukatar mai debe me kewa a gidan ba zai yiwu yadinga kwana shi kadai a gado ba bayan yanada ikon yin hakan. Yayi ajiyar zuciya yamike da niyyar yaci abincinsa yabar gdan, sai yakasa yanufi dakin data shiga yabude tana kwance rub da ciki bisa gado tana kuka, yahaye gadon yakwanta kusa da ita yana shafa bayanta da fuskar ta cikin muryar nan tasa mai taushi da kayatar da zuciya yace da ita "bansan dalilin wannan kukan naki ba Anisa in dai ina da matsayi a gunki na hadaki da Allah ki bayyana min damuwarki. Tabude idonta zuciyarta a karaye tace "Abbakar ba za ka iya min maganin damuwata ba da za ka iya da bamu kawo wannan lokacin cikin wannan yanayi ba. Yace 'haba anisa Allah musuru gareni da zan san damuwarki har in magance miki ita alhali baki sanar dani damuwar ta ki ba. Tamike zaune tana goge hawayen dasuka cigaba da zubo mata tace "Abbakar meye dalilin zamana a gdan nan? Ya amsa "kauna. Me yasa kace kauna? Ya amsa "Na san babu abinda zaisa ka zauna da mutumin da ba ka kauna, dan haka kaunar da kike min ce tasa kika zauna tare dani. Bayan wannan za ka iya rantse min da Allah akan cewa bakasan wani abu a zuciyata ba game da kai. Yace "to in banda abinki anisa akwai wanda yasan abinda ke cikin zuciya bayan Allah? Ya matso jikinta sosai yakamata yarungume yayi mata kiss yace "kidaina sawa zuciyarki komi game dani kidaina bari ranki yana baci duk abinda kike bukata zan miki. Ya yi hakan ne dan yahanata fadin abinda yasan tana daf da fadinsa, yashga shashafa mata bayanta da cinyoyinta nan da nan jikinta yayi sanyi tadinga jin wani irin abu na yi mata yawo a jiki, so ya yiso a zuciyarta kallon kyakyawar fuskar khalifa ya hanata ta hanashi aiwatar da abinda yake mata alhali nasihohin mominta na ta kai kawo a zuciyarta, zuwa can khalifa yadinga fidda numfashi dasauri dasauri yana cakudata yadda yaso, abin yafara ba ta tsoro tayi kokarin janye jikinta daga na sa yayi wuf yakamota yana fadin "kar ki gujeni a wannan lokacin ke ce kika ja ra'ayina ba zan iya hakura dake ba ki daure kibani hadin kai zan maki maki duk abinda kikeso. Ya kwantar da ita bisa gado yadanneta da faffadan kirjinsa yarufe ta ruf yana mata kiss, gabadaya hankalinta ya tashi sosai sai jikinta yake rawa, a haka dai khalifa yasan ta diya mace yayi mamakin yadda yasanta a matsayin sabuwar budurwa wadda bata taba sanin da namiji ba, dama "yammata suna kaiwa wannan lokacin da budurcin su? A DAREN FARKO 15 yamike yayi wanka yafito falo cike da nishadi yaci abincinsa bai koma dakin ba yafita abin da yasawa ransa shi ne ashe yanada abar hutawa a gda tun farko yaki ba ta kai . Anisa tayi kuka tayi kuka har taba uku lada, zazabi da ciwon kai suka rufeta takasa tashi, takira number ramat tace "ke ni fa ba zanzo gdan wannan abin jin kan tsiyar ba ke dai da kike mayen sonsa kikaga za ki iya zaman gidansa sai kiyi tayi, ni dai ina ba ki shawarar kidauke ranki akan khalifa ba za ki iya mallakarsa ba ke ko kin mallake shi wahala za kisha dan namiji ne me garari da tsada. Anisa ta jefar da wayar taci gaba da kuka sam dawani ido zata dubi mominta ko da ta san cewa ba za tasan abinda yafaru ba abin takaici ne ace ta karya alkawarin datayi wa momin ta ta na cewa za ta rike mutuncin kanta, shin ina makomarta a gun khalifa, shin meye amfanin zuwanta germany ne? **** Bayan tafiyar jiddah london karatu abunda su hajiya sude suka maida kai shi ne yawon gdajen malamai da bokaye wai su burinsu khalifa yaso ummi ko ta halin kaka, mafi yawan malamai na bayyana musu cewa khalifa fitinannen yaro ne mai jarabar kwadayin mace amma bbu batun aure ko kadan a zuciyarsa, haka shi mutum ne da ba ya son raini da ace yanada sausaucin ra'ayi zai iya kula ummi da sunan soyayya tunda da sha'awa mai zafi amma a bisa la'akari da yadda yanayinsa yake bazai iya baiwa ummi fuskar soyyaya ba dan gudun kada tarai na shi tunda yana ganin ta ne a karamar kanwarsa, malamin daya fara shaida musu wannan batu ya tabbatar musu da cewa wannan shi ne hakikanin ra'ayin dr. khalifa wanda yake tafiya akai, hajiya hauwa tace,"to malam ba za a iya tankwasa zuciyarsa yasota ba ko ya ki ko ya so, malam mahaifin yaron nan dan uwanmu ne matarsa ta asirce shi bai jin maganar kowa sai tata duk wannan uwar dukiyar daya tara idan bbu shi ita da khalifa za su mallaketa. Malam yayi murmushi yace "akwai hanyar hakan amma ba zai yiwu ba har sai ya dawo kasar nan dazama sbda za muyi amfani da kasar daya taka ne muyi masa aikin da mukewa lakani da bita zai zai, zaita bin ummi sai yadda tayi dashi, anan ne suka dan yi murmushi hnkalinsu yafara kwanciya. "Yace suyi hakuri nasara sai a hankali da hakuri ake samunta ba da gaggawa ba,. **** Fatima da jiddah daga can london din ke damun ummi akan tadinga neman khalifa a waya da sunan za ta gaida shi bai dace tabar damuwa a cikin ranta haka ba, suna ba ta wannan shawarar ne saboda ganin yadda hnkalinta ke tashi musanman fatima da ke kusa da ita tana ganin yadda ummi ke kuka akan rashin khalifa tun tana boye wa har kukanta ya bayyana ita kanta mama ta fara gane damuwar da ummi take ciki, dukda cewa ba a san abinda ke damunta ba idan ta tambayeta sai tace bakomi, mama ba ta son takurawa ummi sbda tanajin dadin zama da ita. Rannan dai da fatima ta matsa mata akan sai ta kira khalifa a waya tayi murmushi tace "fati idan yabamu amsar da za ta daga mana hankali fa? da muguwar rawa ai gwamma kin tashi, fatima tagirgiza kai tace "wannan hujjar ta ki ba za tasa mi ta zama ckin damuwa ba, idan kin ce da muguwar rawa gwamma kin tashi ai kuma kar ki manta ance a rashin kira karen bebe ya bata kuma a rashin tayi akan bar arha, ummi tajawo wayarta ba tare da ta ce komi ba ganemo nomban khalifa takira ckin sa'a tashiga. Bata jima ba tana ringing yadaga cikin kasaitacciyar muryarsa yai sallama gaban ummi na faduwa tasa hands free dan fatima taji da kunnanta. Ta gayar dashi ya amsa tace "ka gane me magana yayana? Yace "na gane mana ba ummi bace. Tace "ni ce kira nayi dan mu gaisa na ga tun tfyarka kana tmbayar kowa a gdan nan amma ban da ni, bansan laifin da nai maka ba, . Yayi dan jim kamar ba zai amsa ba, daga bisani yace "ina cewa kowa lafiya? idan nace kowa lafiya kina ciki. Ta ce "shi knan nagode yaya karatu.? Ya amsa "karatu Alhamdulillahi. Za takara magana taji dif ya kashe wayar tayi murmushin takaici tace "kin ji ko? Wadannan abubuwan ne suka sa ba na son bugawa khalifa waya, ba wai dan ba na jmson jin muryarsa ba kullum farin cikina ko da a waya ne in dinga hira da khalifa ina jin muryarsa amma ba zan samu wannan hadin kan daga gareshi ba, sbda ba ya bukatar soyayya dani. Hawayen dasuka zubo mata yahana. ta cigaba da magana, hankalin fatima ya kartashi taji tsanar khalifa ya kara kamata, wai wani irin mara imani ne wannan tasa dankwalin ta tana sharewa ummi hawaye, tace "ki yi hakuri insha Allahu khalifa zai zamo mallakinki. Ta ina? Akwai wanda zai yiwa khalifa auren dole? idan har kuwa ba auren dole za a yi masa ba to ba zan same shi ba don baya sona, rokon dazan miki daya neduk yadda mama za tayi miki akan ki gaya mata abinda yake damuna kada kisake tasan cewa khalifa nake so. Fatima tayi mata wani irin kallo tace "matsalarki knan ummi banga ta inda za a samu mafita ba ana wannan boye boyen. A DAREN FARKO 16 .Sai da dare yayi sosai khalifa khalifa yadawo gdan tare da shu baby yau ta yi masa