← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 54

Sashe 6

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ta ankara ta ganshi a gaban ta cikin tsananin 6acin rai ya d'aga hannu ya wanka mata mari a fuska marin da yayi matuk'ar gigita mufidah, hannun ya kamo ya murd'e shi er k'ara ta saki saboda axaba Kafin kuma yace "yanda kika 6ata kayan nan wlh sai kin wanke su "

Yana gama fad'in hka yaja mufidah har cikin mota ya cilla ta ciki da k'arfi har sai da ta buge nan ya shiga ya ja motar a fusace duk mufidah ta gama tsorata jikin ta har 6ari yake tayi da nasani yafi sau ba iyaka gashi batasan inda xai kai ta ba ga mangarib tayi addu'a ta dunga yi Allah ya ku6utar da ita daga hannun shi ko kwakwkwaran motsi ta kasa yi saboda firgici.

Wata unguwa ce mai Kyan gaske suka shiga yanayin unguwar mai kyau ko'ina tsaf dashi ga haske ta ko'ina kamar duhu bai yi ba gashi babu yawaitar mutane sosai, a gaban wani kyakkyawan gida flat house ya danna horn tuni mai gadi ya bud'e kofar gate di'n nan ya shige da motar shi har xuwa wurin da ake parking sannan ya fito ya bud'e kofar 6angaren da mufidah take ya fisgo ta sannan yaja ta xuwa cikin gidan.

Gaskia gidan ba k'aramin had'uwa yayi ba kamar da mutane a ciki komai na more rayuwa akwai a gidan musaddiq ya siya gidan ba don komai ba sai hutawa idan yayi ra'ayi don sai yafi 2 weeks bai xo ba gashi ko'ina tsaf dashi da yake akwai masu gyara mishi gidan.

Suna shiga palon ya wurgar da mufidah har sai da ta sake bige wa da kujera saboda tsabar xafin da ta ji sai da ta saki k'ara Kafin kuma ta mik'e tsaye cikin tsiwa ta ce

"wai mene nufin ka na kawo ni wannan gidan iyeee? "

Cikin kallon wulakanci yace "saboda ki wanke wannan kayan da kika 6ata kin ji na rantse wlh sai kin wanke su "

"ni fah malam dakata kaji ko agidan mu wanki ake min ban iya ba don hka baxan yi ba "

Tana gama fad'in hka tayi hanyar fita daga falon ae kuwa musaddiq yasa hannu ya janyo ta da karfi har sai da ta bugi kirjin shi idanun shi cike da tsantsar tsanar ta yace
"ni ina ruwa na da baki iya ba idan ma baki ta6a yin wanki ba tun da aka haife ki to wlh yau sai kin yi don kin ga ban lallasa miki jiki ba koh?"

Fisge jikin ta tayi tare da cewa "ae kuwa baka isa ba ni ka bud'e min kofa na tafi "

Cikin murmishin mugunta yace "ae kuwa xaki k'wana a nan don baxa ki bar gidan nan ba sai kin wanke "

Yana gama fad'in hka ya nufi wata kofa ya shiga tare da rufe wa wanka yayi ya sauya kaya xuwa jeans blue da t-shirt white mai dogon hannu ya fesa perfumes sannan ya fito xuwa falo da niyyar tafiya masallaci anan inda ya barta a hka ya same ta sai rusa kuka take ganin gashi har lokacin sallahr ishshah yayi kusan karfe 8 kenan tasan yanxu sun tashi daga partyn har sun koma gida ta shiga uku Idan ta koma gida me xata ce wa umma idan ta tuhume ta ina ta xauna sai kawai ta fashe da kuka don bata da amsar tambayar a hka ya fito ya tarar tana kukan.

Yana daf da xai fita daga falon ya juyo ya kalle ta tukunna yace "Idan kina son koma wa gida da wuri to Kafin na dawo daga masallaci ki wanke kuma wankin ya fita sosai fah Idan bai fita ba sai kin sake"

Yana gama fad'ar Hka ya fice daga falon ya sanya key ya nufi masallacin kusa da gidan.

Mufidah kuwa ganin ba yanda xata yi ta nufi bedroom d'in da ya shiga d'aki ne mai kyau wanda aka k'ayata shi sosai kamar da mace a gidan, toilet ta fad'a ta hango kayan a xube a k'asa ganin machine din wankin kaya yasa mufidah jin dad'i amman tuni murnar ta koma ciki ganin shi da tayi a rufe 6am kamar ba'a ta6a amfani dashi ba tsaki taja tare da fad'in "Wannan mutumin mugu ne wlh"

cikin takaici ta d'auka ta fara wankin tana yi tana kuka har da majina dak'yar ta samu jan juice din strawberryn ya fita daga jikin kayan sannan ta matse su ta shanya su sannan ta fito sai had'a uban gumi take kallon agogon tayi taga 8:55 tara sauran minti biyar kenan da sauri ta fito daga bedroom d'in turus ta ja ta tsaya ganin har yanxu musaddiq bai dawo ba kasa xama tayi ta dunga xagaye a cikin palon saboda tsabar tashin hankali kuka kuwa ba'a magana sai faman rusa shi take.

A can wurin partyn kuwa ko da su Yah Omar da nabila basu ga dawowar mufidah ba sun d'auka ta gaji ta gudu gida don hka basu damu ba, shima sadeeq da yaga musaddiq bai dawo ba yasa shi tunanin ko ya gudu gida gashi key di'n yana hannun shi, lokacin da aka tashi sai su Yah Omar ne suka mayar dashi gida .

Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 9:40 lokacin mufidah har ta dai na kukan sai faman ajiyar xuciya take saki alamar taci kuka ta koshi wani murmishin mugunta ya yi tare da cewa
"ohhh my god kiyi hak'uri na mance fah da ke sai yanxu na tuna har naje gida na kwanta na tuna da ke"

Kallon shi mufidah tayi da kumburarrun idanun ta cikin takaici da bak'in ciki ta rasa ma me xata ce tabbas maganar shi gaskia ce don gashi har ya canja kayan jikin shi xuwa sleeping dress na maxa farare sol dasu masu d'an kauri don garin akwai d'an sanyi sanyi maganar da yayi ita ta dawo da mufidah daga tunanin da ta lula yace
"xaki iya tafiya yanxu naga kayan kin iya wanki kuwa don sun fita "
Ashe har ya shiga ya duba su, cikin tsananin tsoro tace "wlh tsoro nake don Allah ka kai ni gida"
Hararar ta yayi kafin yace "ban da wannan time d'in don hka get out "
Da gudu mufidah ta fita daga falon sai da ta fita tukunna tasa mayafin ta cikin sauri ta fice daga gidan gabanta yana faman fad'uwa don kuwa dare yayi ko'ina shiru kake ji nan fah ta dunga tafiya cikin sauri ga nisa unguwar tsakanin ta da titi dak'yar ta iya k'arasa wa kan titi sai dai ababan hawa sun ragu sosai don dare yayi gashi idan ta tsayar dasu basa tsaya wa ana hka wasu en shaye shaye suka nufi inda take har d'ayan na kok'arin rik'e mata hannu don hka mufidah yasa mufidah tsorata sosai nan dai ta kwasa da gudu ae kuwa su ma suka bi ta da gudu nan fah aka fara tsere tsakanin mufidah da en shaye shayen nan wani wawan birki aka ja da mota a gaban mufidah da sauri na cikin motar ya fito ae kuwa mufidah tana ganin musaddiq ne ta nufi wajen tare da rungume shi tana kuka sosai duk a firgice take.

En shaye shayen suna ganin musaddiq suka juya suka gudu, had'uwar jikin shi da na mufidah ba k'aramin canja mishi tunani yayi ba na lokaci d'aya hannun shi yasa ya k'ara rungume ta tsam a jikin shi yana shafa bayanta a hankali ita kuwa sai faman kuka da ajiyar xuciya ta ke saki, shi ma duk laifin shi ne yayi gangancin barin ta taho wa cikin wannan daren a matsayin ta na mace.

Dak'yar ya iya raba jikin shi da nata ganin hka yasa mufidah da sauri rik'o hannun shi cikin kuka tace "Don Allah kada ka tafi ka taimaka min kai kai ni gida ina jin tsoro please "

Kama hannun ta yayi ya sata a mota a hankali ba kamar d'axu ba shima ya xagaya ya shiga sannan yayi wa motar key ya fara tafiya gaba d'aya tunanin shi ya canja tun lokacin da yaji mufidah a jikin shi wani abu ne ke kok'arin taso mishi a cikin xuciyar shi yana danne wa amman kuma ya kasa dai na kallon ta har xuwa lokacin da ya shiga farfajiyar gidan nasu ta sauka da sauri ta nufi cikin gidan shi kuma ya fita daga gidan har yaje kwanciya yana tunana had'uwar jikin shi da ta mufidah.

Mufidah tana shiga gida ta tarar da su umma, Abba da Yah Omar nabila suna xaune hankalin su a matuk'ar tashe sai ganin ta suka yi kamar an wullo ta cikin su nan ta rushe da kuka sosai umma da nabila suka rungume ta da aka tambaye ta ina taje k'in magana tayi sai kuka nan dai dak'yar suka rarrashe ta tayi shiru tana sauke ajiyar xuciya, ruwan wanka nabila ta had'a mata ta shiga wanka bayan ta fito ta shirya cikin kayan bacci ta kwanta xuciyar ta na tunanin abin da yafaru tsakanin ta da musaddiq da hka bacci 6arawo ya d'auke ta..............

_kuyi hak'uri da wannan sai gobe kuma Insha Allah_

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE*🌲

*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*Page 8*

Dummmm gaban musaddiq yayi mummunar fad'uwa lokaci d'aya nan take yaji wani irin abu na yawo cikin xuciyar shi wanda ya kasa tantance ko mene gaba d'aya sai yaji baxai iya cigaba da sauraren wannan hirar ba ya fara tafiya xuwa cikin bedroom d'in shi xuciyar shi cike da tarin damuwa kuma ya rasa dalilin damuwar tashi tun da Yah sadeeq ya ambaci sunan mufidah yanayin shi ya canja.

A can palo kuwa mumy cikin tsananin farinciki tace " Alhmdllh my dear ka ji ashe er gidan aminin ka ya gani "

Er dariya irin ta manya daddy yayi tare da cewa "kaiii amman Nayi tsananin murna yanxu daga nan office xan fara xuwa na same shi mu yi magana "

Cikin jin dad'i sadeeq ya rungume daddy yana cewa "thank u daddy Allah ya bar mana kai "

"Ameeen sadeeq amman gaskia baxa'a ja da nisa ba tunda duk ansan juna ciki da bai " Cewar mumy
Chapter 6 · 0% Book details