← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 54

Sashe 11

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A cikin wannan lokacin ne iyayen musaddiq suka fahimci bashi da lafia don ganin yanda yayi matuk'ar rame wa sosai hankalin su yayi mugun tashi da ganin halin da d'an nasu yake ciki Hka shima Yah sadeeq ba k'aramin tsorata yayi ba gashi sun yi tambayar duniyar nan ya fad'i abin da yake damun shi, amman musaddiq fad'a musu Yayi ciwo ne kawai daga Allah, Sam basu yarda da abin da ya fad'a ba sun tambayi Dr muh'd don sun san abokin shi ne xai sani amman musaddiq bai bashi umarnin fad'a ba nan fah mumy, daddy da Yah sadeeq suka sama musaddiq ido aduk wani motsin shi don su karanci abin da yake damun shi, yana sane dasu shi dai yayi alk'awarin baxai ta6a fad'a wa kowa ba bayan Dr muh'd.

Ranar Tuesday suka shirya yin kamu sosai sun tsara abin gwanin sha'awa, ranar friday kuma arabian night suka yi asabar kuma umman mufidah da umman nabila suka shirya yin mother's day nan ma sun k'ayatar sosai amare sun sha kyau ba irin mufidah ma an ci ansha an watse cikin farin ciki.

Rana sunday da safe wajen karfe 10:20 Yah sadeeq ya shigo palon cikin shigar wata tsadaddiyar shadda fara sol da ita yayi matuk'ar yin kyau ya fito a ango sak nan en uwa suka fara tsokanar shi shi dai murmishi kawai yake yi xuciyar da tsantsar farin ciki yau xai mallaki mufidah a matsayin matar shi ta sunnah.

Adai dai lokacin musaddiq da Dr muh'd su ma suka shigo cikin falon sun sha ankon shaddar su cikin shadda sky blue da bak'in takalmi har da hula ba k'aramin kyau suka yi ba musamman musaddiq da bai saba sa manyan kaya ko wajen d'aurin auren bai yi niyyar xuwa ba sai da muh'd ya matsa mishi dakyar ya iya shirya wa bai ma san da kayan ba sai da muh'd ya bashi, fuskar shi ba yabo ba fallasa mumy kuwa kallon su ta dunga yi kamar ta mayar dasu ciki don tsabar son yaran nata.

Nan suka rungume ta cikin k'aunar mahaifiyar tasu d'an hawayen farinciki tasa hannu ta goge su tare da dafa kan su tace "Allah ya raya min ku 'ya'ya nah, Allah ya albarkaci rayuwar ku Allah ya kare min ku "

"Ameeen thumma Ameeen muna godewa Allah da ya bamu ke a matsayin uwa mumy '

Kallon su take cikin so da k'aunar su tana murmishi, Dr muh'd kuwa shi ma kallon su yake cikin sha'awar su wani 6ari na xuciyar shi yana cike da fargaba don baisan yanayin da musaddiq xai shi gaba idan yaji sanarwar d'aurin auren yasan ya rabu da ita na har abada wani tausayin musaddiq ne ya k'ara kama shi sosai, ana cikin hka daddy ya fito shi ma yayi shirin shi cikin manyan kaya na wata milk colour d'in shadda nan suka rungume shi tare da bashi peck a kumatun shi kafin daga baya su dunguma xuwa wajen farfajiyar gidan suka shiga mota d'aya Dr muh'd ne wajen driving musaddiq a gefen shi wanda ya tsurawa waje ido lokaci xuwa lokaci xuciyar shi tana wani mugun fad'uwa, Yah sadeeq da daddy a baya sai sauran en uwa da abokanan arxiki suka rufa musu baya xuwa wajen d'aurin aure............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

*PAGE 14*

Bayan sun isa wurin d'aurin auren mutane sosai sun taru manya manyan kusassun gwamnati da en kasuwa xuwa abokanan ango sai manyan lecture's da likitoci en uwa da abokan arxiki gasu nan birjik, jama'a ta ko'ina gasu nan karfe sha d'aya dai dai aka d'aura auren mufidah da Yah sadeeq akan sadaki mafi cancanta saboda neman albarkar aure, xuciyar Yah sadeeq ta cika da farinciki sosai ayau Allah ya mallaka mishi masoyiyar shi, son ta daban yake a cikin xuciyar shi yana mata wani irin so baxai iya rabuwa da ita ba sai dai k'addarar ubanjigi ko mutuwa ya rabasu.

Musaddiq kuwa yana xaune cikin mota ya kasa fito wa saboda baxai jure tsayuwa ba, jikin shi ba k'arfi ga kuma gaban shi yana mugun fad'uwa sam baxai iya shiga cikin mutane a hka ba saboda baxai iya k'ak'alo murmishi a fuskar shi ba, kallo d'aya xaka yi mishi ka hango tsantsar damuwa a fuskar shi, yana dafe da kanshi wanda yake mishi ciwo kamar xai cire.

"Alhmdllh hukuncin ubangiji ya tabbata a yau aka d'aura auren Abubakar sadeeq Abubakar da amaryar shi mufidah El hussaen"

Abin da kunnuwan musaddiq suka juyo shi kenan daga bakin wani marok'i ma'abocin xak'in murya, wani irin tari ne ya kama musaddiq tari yake ba kakkauta ba daga bisa ni kuma ya fara aman jini hannun shi yana dafe da saitin xuciyar shi, numfashin shi ne ya fara kok'arin d'auke wa gaba d'aya gaban rigar shi da bakin shi ya 6aci da jini.

Dr muh'd kuwa wanda yake cikin taron mutane jin an d'aura auren yasa shi tafiya inda musaddiq yake don yasan a wannan lokacin yana cikin wani mugun yanayi, tausayin musaddiq fal cikin xuciyar Dr muh'd ya K'arasa inda yayi parking d'in motar da suka xo yana bud'e wa ya hango abin da yayi matuk'ar girgixa shi ya d'aga mishi hankali, musaddiq ya gani a kwance ga jini ya 6ata mishi jiki kuma gashi babu alamun yana numfashi a tattare da shi.

Cikin sauri ya yunkura xai shiga motar yaji an dafa mishi kafad'a a matuk'ar firgice ya jiyo don ganin wane, had'a ido yayi da Yah sadeeq fuskar shi d'auke da farinciki yace
"muh'd ina musaddiq yake? "
Wani uban gumi ne ya tsatstsafo wa muh'd a jikin shi gaba d'aya hankalin shi ya rabu gida da yawa shin xai sanar wa da Yah sadeeq ga halin da musaddiq yake ciki ko kuma ya shiga mota ya kai musaddiq asibiti don a ceci rayuwar shi ko ya tsaya ba wa Yah sadeeq amsar tambayar shi.

Yah sadeeq kuwa tsura wa fuskar muh'd ido yayi don ganin yanda yake a firgice " what happened to you muh'd, kamar akwai wani abin? "
Cikin rawar murya Dr muh'd yace " ba...... ba wani abu Yah sadeeq just an kirawo ni daga hospital ne an kawo wani patient yana buk'atar taimakon gaggawa"

"Ayyah so ina musaddiq? "
"Hmmm yana cikin taron mutane wajen friends d'in mu idan ka duba xaka gan shi "

"alright sai ka dawo "
"Okay Yah sadeeq Allah ya sanya alkhairi "
Cikin murmishi yace "Ameeen muh'd thank u "

Yana gama fad'in hka wani cikin abokanan Yah sadeeq yaxo ya janye shi daga wurin suka shiga cikin mutane, da sauri Dr muh'd ya fad'a cikin mota ya ja ta cikin wani irin gudu don gaba d'aya a rikice yake.

Cikin kankanin lokaci Dr muh'd da wasu lokaci guda biyu wanda muh'd ya kirawo su, suka duk'ufa akan musaddiq suna kok'arin ceto rayuwar shi.

Sun d'auki tsawon lokaci akan musaddiq Kafin numfashin shi ya dawo amman duk da hka da taimakon oxygen tube yake numfashi gashi nan a kwance kamar wani matacce ba inda jikin shi yake motsi a jikin shi, abin da mutum xai san yana raye numfashin da yake fitar wa ne sai buguwar xuciyar shi, kallon musaddiq Dr muh'd yake yana wani irin kukan tausayin abokin nashi dole ya sanar da iyayen shi abin da yake damun shi don kuwa aka cigaba da hka wataran xa'a samu matsala kuma shi xasu xarga da laifin sakaci da lafiar d'ansu mybe akwai wani taimako ma da xasu iya wajen kwantar mishi da hankali.

Wayar shi ya d'auko ya nemo number d'in daddy don shine namiji sai yafi nutsuwa ya saurare shi fiye da mumy don ita mace ce akwai rauni yanxu sai ta k'ara hargitsa shi, wajen 2 missed calls yayi but daddy bai d'auki wayar ba watak'ila bai ji kiran ba saboda hayaniyar jama'a.

Yana xaune ya xuba wa musaddiq ido tare da yin tagumi lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen da yake xuba daga idanun shi.

Daddy kuwa yana cikin jama'a hayaniyar su yasa bai ji kiran muh'd ba sai bayan an d'aura auren Yah Omar da nabila ne sun shiga mota suna kok'arin tafiya wajen walima din da suka had'a, sai yaji kira a wayan shi d'auka yayi don duba wane ya ke kiran shi ganin sunan muh'd yasa daddy yin mamaki amman sai ya kawar da mamakin shi ya d'auki wayar.

Shi kuwa Dr muh'd har ya fitar da ran daddy bai ji kiran ba sai kuma yaji ya d'auka cikin sauri yayi sallama bayan daddy ya amsa ne sai kuma muh'd ya d'anyi shiru yana tunanin ta inda xai fara sanar mishi da wannan mummunan labarin a ranar farincikin auran d'ansu, gaban shi har wani mugun fad'uwa yake.

"lafia muh'd ka kirawo ni kuma naji kayi shiru ko baka ji ba? "
Jin saukar muryar daddy a kunnen shi ya sa Dr muh'd fara magana cikin rawar murya yana cewa
"daddy da... daman cewa xan yi maka mu.... musaddiq ne ba lafia ciwon shi ya tashi so yanxu muna hospital "

Cikin tashin hankali daddy yace "wanne ciwo kake nufi muh'd? "
Sai lokacin muh'd ya tuna da kato6arar da Yayi shaf ya mance basu san musaddiq yana da ciwon xuciya ba, don hka cikin fad'uwar gaba yace
"am daddy ina son kaxo asibitin musaddiq yanxu xamu tattauna wata magana aka rashin lafiyar musaddiq so bana so Yah sadeeq ya sani ka taho kai da mumy kawai "

Tuni hankalin daddy yayi matuk'ar tashi katse wayar yayi tare da bawa mutanen da suke jiran shi exuse akan yana xuwa akwai abu mai mahimmanci da ya taso mishi yanxu, cikin sauri ya fad'a mota ya nufi gida gumi ne kawai yake tsiyayowa daddy wanne ciwo ne da musaddiq da basu sa ni ji yake kamar ya tashi sama ya ganshi gaban Dr muh'd yana fad'a mishi abin da yake damun d'anshi yaron da yafi soyewa acikin xuciyar shi.
Chapter 11 · 0% Book details