Sashe 48
Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"wash! da zafi ni ka bari zai warke fah "
Ta fad'a tana k'ak'alo hawayen dole.
"kinsan bazan jure ganin ki cikin ciwo ba don hka oya ki tsaya na gani "
D'ago kanshi yayi ya kalle ta sai yaga tana hawaye cikin rud'ewa ya saki k'afar ya zauna tare da janyo ta jikin shi yana bubbuga bayanta yana cewa
"sorry habibty na bari ki daina kukan nan kin ji? "
Ai kuwa ta 6are baki ta saki kukan shagwa6a gashi tana kiran wayyo k'afar ta, kuma idan ya sanya hannu zai ta6a ta dad'a k'arfin kukan tana girgixa kai kada ya ta6a da zafi.
Nan Musaddiq ya sake rud'ewa sosai shi yanzu ya zai yi mata ne idan zai ta6a k'afar zafi gashi bai ta6a k'afar ba tana mishi kukan zafi kuma shi bazai jure jin kukan ta ba, ganin tak'i shiru duk ta d'aga mishi hankali ne yasa shi had'e bakin shi da nata.
D'an tutture shi ta fara yi ya sake matse ta a jikin shi d'if tayi da ita tana kar6ar sak'onnin Musaddiq daman ai kukan na k'ak'ale ne, sai da ya tabbatar ta had'iye kukan nata tukunna ya cikata suna had'a ido ya sanya d'an yatsan shi d'aya ya dungure mata kai yana cewa
"rigimammiya ko Afnan bazata yi rigimar ki ba "
D'an hararar shi tayi tana turo bakin ta tace
"Duk rigima ta dai wani yafi ni "
Kallon ta yayi yana cewa
"dawa kike? "
D'an kad'a idon ta tayi tana cewa
"da wanda ya tsargu "
Nuna ta yayi yana cewa
"lallai yarinyar nan kin rainani da yawa xanyi maganin ki yanzu "
Kafin ya k'arasa fad'i ta mik'e da sauri zata gudu ya kawo hannun shi zai kamata sai ta goce tana mishi dariya har da gwalo, nan ya biyo ta suka fara gudu tuni su Mufidah an mance ciwon k'afar karyar da aka yi ta fara gudu tana dariya.
Bata yi wani nisa sosai ba ya cafkota suka zube cikin farin yashin da yake k'asan wajen suna dariya tare da sauke numfashi da sauri da sauri, kallon junan su suke kafin Musaddiq ya sanya hannun shi ya d'an lankwasa d'an yatsan ta d'aya har yayi k'ara cikin jin zafi tace
"wash ni me nayi maka ne da zafi fa?"
Yana kallon face d'in ta yace
"tunawa nayi da ciwon da k'afar ki take yi yanzu naga kuma kina gudu "
"bata warke ba na dai na jin zafin "
Ya bud'e bakin shi zai yi magana wayar shi ya fara k'ara alamar kira zaro wayar yayi ganin sunan Muh'd ya sanya shi picking d'in wayar, d'aya hannun shi kuwa ya janyo Mufidah ya kwantar da ita saman chest d'in shi don yau jin shi yake cikin wani irin farinciki da nishad'i.
Muryar Muh'd ce ya tsinkayo yana cewa
"Hey lover boy kana ji na?"
Murmishi Musaddiq yayi yana cewa
"ina jin ka mana ya akayi guy? "
"Qlau jin ka nayi wajen 2 day's baka kirawo ni ba na kirawo ka kuma baka yi picking ba "
"sorry guy abubuwa ne suka yi min over "
Cikin zolaya Muh'd yace
"ko kuma an tsaya cin soyayya ba an mance da ni "
Er dariya Musaddiq yayi yana kallon idon Mufidah yace
"kusan hkne fah guy kasan mutum idan yana moment d'in nan sai a slow "
Wata dariya Muh'd ya kwashe da ita yana cewa
"Ohhh sake maimaita min ban ji sosai ba "
"kai fa d'an air ne wani lokacin nasan ka ji abin da na fad'i "
"lallai guy kace kana nan kana fanshe soyayyar ka ta tsayin shekaru, hkan yayi kyau Allah ya kawo mana baby boy ko girl "
Hannun Musaddiq yana kan Mufidah yana shafawa yace
"Amin aboki tare da kai "
"tabd'ijam an fad'a maka zan jira ka ne ai ni an kusa juye min "
"Ah haba aboki da gaske? "
Musaddiq ya fad'a cikin farinciki, cikin tabbatar wa Muh'd yace
"wallahi aboki da gaske na ke "
"wowww na taya ka murna sosai guy "
Jin d'an hayaniya yasa Muh'd yace
"kana ina ne Musaddiq ?"
Cikin murmishi yace "me ka ji ne? "
"hayaniya na ji kamar ma baka gida "
"ina wurin beach muna hutawa "
Cikin dariya Muh'd yace
"wow lover boy kace kana hutawa, a dai yi a hankali kada ka 6ata mana Afnan don nasan ba hak'uri ne da kai ba ana barin sai bata nan "
"Allah ya shirya ka Muh'd"
"Amin aboki thank for your du'a"
Kafin kuma ya cigaba da magana in seriously yace "Musaddiq ya kamata ka dawo nigeria fah kaga kai d'aya su mumy suke dashi a yanzu duk da basu nemi wani abin sun rasa amman nasan basa son zaman ka a australian, sun fi son zaman ka a tare da su ya kamata ka dawo "
Ajiyar zuciya Musaddiq ya sauke a hankali kafin yace
"nima nayi tunanin hka friend but insha Allah nan da d'an lokaci xamu dawo"
"Yawwa d'an uwa, agaida min da Mufidah nd Afnan, kace wa Mufidah kasa ta mance da ni tun da kuka zo bamu ta6a yin waya ba ina jin zata kirawo k'awar ta (nafisat matar Muh'd),su sha hira amman ban da ni "
Dariya Musaddiq yayi kafin yace " hkan ne dai dai guy "
Shima Muh'd yana dariya yace "kai koh?, shikenan dai sai anjima "
Yana gama fad'in hka Muh'd ya katse wayar lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in Mufidah zuciyar shi tana cikin farinciki.............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:[email protected]
*PAGE 56*
Yana gama fad'in haka Muh'd ya katse wayar, lokaci d'aya Musaddiq ya saki ajiyar zuciya yana sake hugging d'in ta zuciyar shi tana cikin farinciki, gaba d'aya ya mance ma inda suke ya mance yana tare da Mufidah a kusa zuciyar shi ta ingiza bakin shi har ya furta kalmar
"i luv u Mufidah "
Ba tare da ya shiryawa hakan ba, sai da ya gama furta maganar sannan ya dawo cikin hayyacin shi ya tuna su6utar bakin da yayi.
Mufidah kuwa kusan suman zaune tayi saboda jin kalmar da ta fito daga bakin Musaddiq kallon shi take fuskar ta d'auke da tarin mamaki.
Wayancewa yayi ta hanyar hararar ta kafin yayi magana cikin sautin tsawa yace
"malama d'aga ni zan tashi kin wani danne ni "
Girgiza kanta kawai tayi tana tashi daga jikin shi, bata ko kalle shi ba ta nufi inda suka yi parking motar su ta tsaya tare da sunkuyar da kanta tana kallon k'asa zuciyar ta sam babu dad'i, don ta tsani ayi mata tsawa a rayuwar ta.
Bin ta yayi da kallo jikin shi yayi sanyi sosai wani mugun tausayin ta ne ya rufe shi,akan mene zai yi mata tsawa me tayi mishi, dole yayi yak'i da zuciyar shi don samun zaman lafiyar su, bazai yiwu su cigaba da irin wannan zaman ba.
Jikin shi a sanyaye ya fara tafiya zuwa inda take, bud'e motar yayi da key d'in hannun shi, cikin sauri Mufidah ta shiga ta zauna har yanzu still bata kalli inda yake ba, shima shiga yayi ya zauna ya kasa kunna motar su tafi kallon ta yake yi ko zata d'ago kanta ta kalle shi.
Sun d'auki tsayin mintuna bai ga alamar zata yi mishi magana ba ko zata kalle shi, sai kawai yayi wa motar key suka bar beach d'in, tafiya suke shiru kowannen su zuciyar shi da abin da take sak'awa, sam dawowar bata yi musu dad'i ba kamar yanda suka taho ba cikin farinciki da nishad'i ba.
Suna k'arasa wa gida yana gama parking Mufidah ta bud'e murfin motar ta fita tare da bud'e murfin motar na baya ta d'auki Afnan dakyar ta fito tana tafiya har tana kok'arin fad'uwa.
Da kallo ya bita fuskar shi da zuciyar shi d'auke da damuwa yana son yi mata magana but bakin shi yayi mishi nauyi sosai ya kasa yi mata magana, yana kallon ta har ta shige ciki tukunna ya fito daga motar tare da d'ebo shopping d'in da suka yi ya nufi cikin gidan.
Ko da ya shiga bata parlour kayan hannun shi ya zube su tare da zama kan kujera yana dafe da kanshi, tunanin hanyar da ya kamata ya bi don ya rarrashe ta yake, yasan bai kyauta ba da tsawar da yayi mata.
Mufidah kuwa tana shiga d'aki ta kwantar da Afnan kan bed sannan ta wuce toilet ta d'auki tsayin mintuna 5 a ciki kafin ta fito, fitowa tayi daga d'akin zuwa kitchen don ta had'a musu abincin dare.
A parlour ta tarar dashi zaune bata kalli inda yake ba ta wuce kitchen abin ta, da kallo ya bita zuciyar ta gama yanke hukuncin a yau ba gobe ba zai bayyana mata irin tarin son da yake mata.
Lumshe idanun shi yayi sakamakon fara jin k'amshin girkin da take yi ya fara dukan hancin shi, yana nan zaune Afnan ta tashi daga bacci ta fito zuwa parlour, cikin jikin shi ta shiga tana kwanciya, shafa mata kanta kawai yake don baya cikin nutsuwar shi.
Bayan ta gama girkin ne ta jera a saman dining table, duk zirga zirgar da take akan idon shi d'in yana nan zaune a parlourn, bayan ta gama ne ta gyara kitchen sannan ta fito zuwa parlour ta gyara ta fesa air fresheners masu k'amshi.
Tana gama wa da nan ta nufi d'akin Musaddiq ta gyara mishi tsaf, tare da sanya mishi room freshener, sai da taga komai yayi mata yanda take so sannan ta bar d'akin, tukunna ta fito ta nufi d'akin ta gyara shi tayi shima yayi tsaf dashi.
Sannan ta fito zuwa parlour inda Musaddiq yake ta nufa, sai da ta zo gaf dashi sannan ta kalli Afnan tace
"Afnan zo nayi miki wanka "
Tashi Afnan tayi ta nufi inda Mufidah take tsaye, hannun ta ta rik'e suka wuce d'aki, ta bar Musaddiq zaune anan cikin rashin samin mafita.