← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 54

Sashe 18

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mumy ma tana k'aunar mufidah saboda hankalin ta da nutsuwar ta gashi tana matuk'ar kulawa da d'anta shi yasa duk abin da ta samu xata nemi mufidah ta bata.

Saboda kwanciyar hankali mufidah tayi wata er k'iba kad'an ta k'ara haske da kyau abin ta, tana samun kulawa sosai a wajen mijin ta da iyayen shi, bata da wata matsala a yanxu sai wadda ba'a rasa kowanne d'an adam da ita ba.

Tsawon watannin su biyu da aure bata fita ko'ina ba amman a yau tayi niyyar tambayar shi tana son taje gida daga can xata wuce gidan Yah Omar wajen nabila don ita nabila xuwan ta biyu gidan tana yi mata yini, a xuwa na biyun ne tace baxa ta k'ara xuwa ba sai ta je, shi yasa ta yanke shawarar fita gobe.

Wajen K'arfe biyar da rabi ne ta shiga kitchen don yi musu girki dare, abinci mara nauyi tayi niyyar yi musu don hka jeelop na taliya take son yi, nan ta fara aikin ta cikin kware wa ta yayyanka su vegetables da yin blending d'in kayan miya.

Cikin tsawon mintuna ta kammala jeelop d'in ta xuba a food Flak's sannan tayi musu chicken pepper soup, sai coconut juice wanda yasha coconut and pineapple aciki sosai tare da milk ta ruwa tana gama wa ta sanya a frige bayan ta juye shi a jug.

Food Flak's d'in ta d'iba ta kai dinning area ta jera tukunna ta dawo ta kitchen ta d'auki plate's, spoon da glass cup's ta kai su dinning bayan ta gama sannan ta gyara kitchen d'in tare da yin wanke wanke, bayan ta gama da kitchen ne, ta gyara falo tare da sa mishi turaren wuta mai k'amshi tuni ko'ina a falon ya d'auki k'amshi, sannan ta wuce bedroom's d'in su ta gyara, tana gama wa sai ta fad'a toilet tayi wanka tare da d'aura alwala don mangarib tayi.

Bayan ta idar da sallahr mangarib ne ta xauna tana karatun Qur'an har xuwa lokacin sallahr isha'e, bayan ta idar tayi shafa'i da wutiri ne tare da addu'o'in ta tukunna ta tashi ta cire abayat d'in da tasa tayi sallah.

Wajen dressing mirror ta k'arasa ta shafa wani cream tare da yin light make up, tukunna ta k'arasa wardrobe ta bud'e 6angaren English wear's ta d'auko wani jeans white ne da t-shirt pink colour mara hannu bayan ta gama wa kayan ne sai ta gyara gashin kanta ta gefe tayi parking d'in gashin nata tayi kyau sosai kamar wata er baby, perfumes ta fesa tare da shafa humra mai tsananin k'amshi a jikin ta, falo ta fito ta xauna tana kallon film d'in thor a mbc 2.

Ko mintuna bakwai bata yi da xama ba sadeeq yayi sallama tare da shigowa palourn, d'ago kai tayi ta kalle shi tare da amsa mishi sallamar cikin muryar ta mai dad'i.

K'arasa wa yayi tare da xama kusa da ita yana kallon ta yace " my wife kin yi kyau sosai"

Cikin murmishi ta amsa da "thanks my dear, yau ka dad'e fah lafia?"

Yana kamo hannun ta yace " lafia my wife after an idar da sallah ne na tsaya yin waya da musaddiq kiyi hak'uri idan baki ji dad'i ba"

Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai dear dafatan yana nan lafia?"
"Qlau yake yana gaida ke ma"

Kallon shi tayi tare da cewa "Hmmm ina amsawa ", ba don ta yarda da abin da yace ba, nan ta jashi bedroom yayi wanka tukunna suka fito dinning table don yin dinner.

Bayan sun kammala cin abincin ne suka dawo cikin parlour, yana xaune kan kujera 3siters mufidah tana kwance tayi matashin kai da cinyar shi suna er hirar su da kallo, can mufidah tace

" Don Allah dear ina son ka barni gobe na je gidan mu da gidan Yan Omar please"

Murmishi yayi tare da shafa mata kai yace "kada ki damu my wife na bar ki Allah ya kai mu goben"

Cikin tsananin farinciki tace " Ameeen ngde dear"

"Kin wuce komai a waje na my wife, Allah ya sa ki Haifa min 'ya mace ma kama da ke, kafin na mutu naga d'an kai na nima"

Lokacin da ya fara maganar murmishi ne shimfid'e a fuskar mufidah don ita ma tana tsananin son baby's tana son ta ganta da ciki kamar nabila k'awar ta don ita ta harbu tuni, k'arshen maganar da sadeeq yayi shi yasa mufidah ta 6ata fuska cikin shagwa6a tace

"Kai koh dear xaka fara koh, insha Allah xamu rayu tare na haifa maka 'ya'ya da yawa"

Murmishi yayi tare da cewa "haba my wife ae ita mutuwar nan ba sallama take da mu ba, lokaci d'aya xata xo ta d'auke mutum, kuma ana son ko da yaushe bawa ya dunga tuna ta"

Tuni idanun mufidah sun fara taruwa da ruwan hawaye har sun fara xuba, ganin hka yasa sadeeq ya rungumo ta jikin shi tare da rarrashin ta yana gwada mata soyayyar shi mai sanyi wadda take mantar da mufidah damuwa, ae kuwa bai kyale ta ba sai da ya ga babu sauran damuwa a tare da ita sai farin ciki tukunna ya kyale ta.

Washe gari da safe bayan sun gama breakfast ne suka shiga wajen mumy da daddy mufidah tayi musu sallama mumy har da bata perfumes ta kai wa umman ta daddy kuwa kud'i ya bata sadeeq ya kai ta mall ta yi musu tsaraba, sosai tayi musu godia tare da addu'ar fatan alkhairi, sannan suka fito suka tafi.

A sahad store ya tsaya yayi musu tsaraba ko kud'in wajen mufidah bai kar6a ba wanda daddy ya bata, lokacin da aka gama xuba kayan a boot ne ya shiga har yayi wa motar key sun fara tafia mufidah ta mik'a mishi kud'in da daddy ya bata, girgixa kai yayi yana murmishi cikin sanyin muryar shi yace

"My wife ba kud'in ki ne fah, ni wannan wanda nayi niyyar baki ne don hka ki rik'e abin ki"

"A'a ni dai ka rik'e sun yi min yawa ne please"

"Duk da hka ki rik'e xasu yi miki amfani wani lokacin kin ji"

Kasa ce mishi komai tayi, da hka suka k'arasa gidan su mufidah yana gama parking ne ta bud'e kofar motar tare da fita da gudu tayi cikin gidan tana kwalla Kiran umma, sosai abin da tayi ya bashi dariya lallai mufidah akwai sauran yarinta a tattare da ita, fita shima yayi tare da bin bayan ta.

"Umma na kina?" umma wadda ke xaune kan kujera a palour ta d'ago kanta da sauri ta kalli kofar shigo wa don jin muryar er autar ta, kafin ta ankara har mufidah ta fad'o kanta tana dariya, cikin tsananin farinciki umma ta rungume mufidah kafin kuma ta cika ta tace

" ohhh ni mufidah bakya girma ji yanda kika fad'o min kamar wata karamar yarinya"

Cikin shagwa6a tana turo baki tace " toh umma ae ni k'arama ce a gaban ki"

Suna cikin hka sadeeq yayi sallama sai da umma ta amsa mishi tare da bashi ixinin shigo wa sannan ya shigo har k'asa ya tsugunna ya gaida umma, cikin farinciki umma take amsawa ta cigaba da cewa

"Ohhh ashe tare kuke shine ta gudo ta barka a waje"
Shi dai sadeeq murmishi kawai yayi yana kallon mufidah wadda take jikin umma tak'i tashi har yanxu, gaba d'aya sadeeq da umma er suruka ake yi ita kunyar shi take shima hka don hka ba wata hirar kirki da suka yi yayi musu sallama tare da fita daga palour mufidah sai a lokacin ta bishi a baya tana fito wa yasa hannu ya d'an ja kunnen ta kad'an tare da cewa

"Shine kika haye jikin umma duk kin bi kin danne ta koh?"

"Toh ae duk murnar ganin ta ne dear kuma nayi kewar ta sosai"

Murmishi yayi tukunna ya shige mota bayan yasa mai gadi ya fitar da kayan boot ya shiga dasu gidan, sallama yayi mata sannan ya tafi ta koma cikin gidan.

Yinin ranar sun sha hira da umma sosae don anjima ba'a had'u kamar hka ba sai a waya, sai da yamma sadeeq yaxo daukan ta, amman sai da ta jira Abban ta ya dawo suka gaisa sannan suka tafi, gaf da Kiran sallahr mangarib suka k'arasa gidan Yah Omar a lokacin shima Yah Omar dawowar shi kenan daga office nan suka wuce masjid yayin da mufidah ta shiga da sallama cikin palourn, wani ihu nabila ta saki tare da yin tsalle ta rungume mufidah tana cewa " wayyo my friend kece a yanxu?"
"Ni ce kuwa my sister, kina ta tsalle sai kin wahalar mana da babyn mu"

Hararar wasa nabila tayi mata tare da jan ta xuwa bedroom don yin sallah, bayan sun idar ne suka bud'e shafin hira sosai sai da yah Omar yaji shiru basu fito ba ya biyo bayan su nan yaga sai xuba suke, hararar mufidah yayi tare da cewa "kin xo kina ta xuba mata surutu ko tar6ar da aka sabar min ba'a yi ba, gashi da yunwa na dawo"

"Kaiiiiiiii Yah Omar kasan dai nabila ta fi ni surutu ko?" Ta fad'a cikin shagwa6a

"Bana son wani surutun kuma ki tashi ki tafi wajen mijin ki, sweetheart ke kuma mu tafi kitchen a bani a abinci"

Ya k'arasa fad'i yana kama hannun nabila suka fita daga bedroom d'in, mufidah tashi tayi ta bisu ita ma tana dariya ta wuce cikin Palo wajen sadeeq.

Basu bar gidan Yah Omar ba sai wajen 9 na dare, lokacin da suka k'arasa gida bayan sun shiga wajen mumy ne sannan suka wuce part d'in su, wanka kawai suka yi tare da neman makwanci don agajiye suke kuma sun riga da sun ci dinner gidan Yah Omar don hka baccin su suka yi hankalin su a kwance............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

_kuna ina k'awaye kirki wannan shafin naku ne Queen mermue dear and Ameerah (Amnoor), wannan shafin sadaukar wa ne gare ku, hak'ik'a ina matuk'ar alfahari da ku abokanan kirki, Allah ya bar mu tare ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝❤

*PAGE 24*

*AFTER ONE YEAR*
Chapter 18 · 0% Book details