Sashe 42
Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tana gama fad'in hka ta juya xata cigaba da tafiya ai kuwa ya janyo ta jikin shi ya sanya d'aya hannun shi ta bayan ta ya rik'e ta gam, d'aya hannun kuma ya rik'o fuskar ta 6ata fuskar shi tare da cewa
"ba dai don kin ganni da wata ba ne kika shiga toilet kina kuka, kin fara sona kenan? idan hka ne kuwa ki bawa xuciyar ki shawara ta fitar da sona daga ciki idan kuwa ba hka ba xaki cutar da kanki, don ni musaddiq ba sa'an auren ki ba ne na aure ki ne don cika burin d'an uwa na sadeeq"
Yana gama fad'in hka ya cika ta ya fice daga bedroom d'in, kusan suman tsaye mufidah tayi da jin abin da musaddiq ya furta mata daman ba sona yake ba?, xuciya ta mai yasa kika yi min hka, kika kar6i son mutumin da baya sona, wasu hawaye ne masu xafi suke fita daga idanun mufidah.
Shi kuma musaddiq bedroom d'in shi ya wuce tare da rufe kofar ya jingina bayan shi jikin kofar wasu hawaye ne masu rad'ad'i suka fara xubo mishi dafe kan shi yayi yana cewa
"me... me yasa baki na ka furta wannan furucin wajen masoyiya ta, kamata yayi nayi farinciki mufidah ta fara sona bai kamata nayi mata hka ba, yanxu ta ina xan gyara kuskure na, na rasa yanda akayi na fad'a mata hka nasan xuciya ta da kwakwalwa ta ba hka suke son na furta ba, baki na ne ya furta hkan, I'm so sorry mufidah, ta ina xan fara nuna miki soyayya ta bayan ke matar d'an uwa na ne baxan iya ba baxan iya mufidah ji nake kamar xan ci amanar sadeeq"
Hka ya dunga maganganu cikin mayen son mufidah har xuwa lokacin da bacci ya dauke shi a k'asan carpet d'in d'akin.
Yinin ranar kusan mumy ce da afnan suka yi shi a parlour musaddiq yana bedroom hka mufidah ma har xuwa karfe 5 na yammacin ranar tuni mumy ta gama had'a komai nata ta xaunar da mufidah da musaddiq tana sake yi musu nasiha sosai wanda kowannen su baya kallon d'an uwan shi kansu a sunkuye suna kallon k'asa.
Bayan ta gama yi musu nasihar ne suka fita rakata airport, tun da suka fara tafia mufidah idanun ta suna kan window tana xubar da hawayen bak'in ciki abin da musaddiq ya gama yi mata d'axu gashi mumy xata tafi ta bar su, da hka suka k'arasa airport d'in mumy dai bakin ta bai daina furta musu wad'annan kalaman ba
"kuyi hak'uri da junan ku don Allah ku xauna lafia ban da fad'a da tashi hankali ana yin hak'uri ana kai xuciya nesa, mmusaddiq ga mufidah da afnan nan ka rik'e su amana don su amanar d'an uwan ka ne, ka kula su don kai ne babba kuma namiji a cikin su "
Lokacin da mumy xata shiga jirgi mufidah kasa jure wa tayi ta rungume mumy tana kuka sosai ita ma mumyn kasa rik'e hawayen ta tayi sai da suka fito afnan ma kukan take ganin yanda mumy da mameen ta suke kuka musaddiq ya dauke ta yana rarrashin ta, dakyar mufidah ta cika mumy ta wuce xuwa cikin jirgi ko k'ara waiwaye su ba tayi saboda kada su karyar mata da gwiwa, suna kallo har aka rufe jirgin ya fara tafia kafin ya tashi sama kuma da gudu mufidah ta shige cikin mota tana kuka..............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻£xclusive writers forum
Like and comment's fb page 👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
*PAGE 49*
shima musaddiq jikin shi a sanyaye ya shiga motar ya fara driven, sai da ya tsaya a hanya yayi musu takeaway na abincin da xasu ci da dare tukunna suka nufi gida,yana gama parking mufidah ta fito ta shige ciki kai tsaye bedroom ta wuce ta xube kan bed tun tana kukan har bacci ya sace ta tana faman ajiyar xuciya.
Lokacin da musaddiq ya shigo d'akin ya dad'e yana kallon ta kafin ya kwantar da afnan a gefen ta wadda ita ma tayi bacci, shima nashi bedroom d'in ya nufa ya kwanta duk jin shi yake wani iri gidan ko kad'an bai yi mishi dad'i ba a hka shima bacci yayi awon gaba da shi.
Firgigit mufidah ta tashi da addu'ar tashi daga bacci a bakin ta bin d'akin take da kallo kamar wadda yau ta ta6a ganin shi, duhu yayi sosai duk da kuwa hasken bulb d'in da ya haske d'akin kuwa.
A hankali ta sauko da kafafun ta toilet ta wuce wanka da alwala ta d'aura ta fito wata jallabia irin ta mata ta sanya tare da hijab tayi sallahr mangarib da ishsha kafin ta d'ora da Shafa'i da wutri ta dad'e xaune tana addu'o'in ta kafin ta mik'e ta canja kayan jikin ta da na bacci.
Tana kok'arin sake kwanciya ne musaddiq ya shigo had'a ido suka yi kowanne ya d'aure fuska tare da kawar da kanshi daga had'a idon da suka yi bud'e baki yayi yace
"ki fito abincin ki yana dining table"
Dakyar ta iya bud'e baki tace
"bana buk'atar shi "
D'aga kafad'un shi yayi tare da cewa
"alright hkan yayi kyau "
Yana gama fad'in hka ya fita daga d'akin mufidah ta bishi da kallo yau ko irin tsokanar nan babu, yau a musaddiq d'in shi yake kamar yanda ta san shi tsawon wasu shekaru da suka shud'e, wani hawaye ne ya xubo ta tana mai tausayin kanta, a hka ta kwana bata ci abincin ba, hkan kuwa ba k'aramin damun musaddiq yayi ba har shima ya kasa cin abincin ya kwanta.
Tsawon kwanaki biyar da komawar mumy nigeria wadda ta je gida lafia, tsakanin musaddiq da mufidah babu mai kula wani kowa rayuwar shi yake shi d'aya, gashi ya sanya afnan a skul.
Idan ya tafi hospital afnan ta tafi skul sai ita d'aya a gida duk bata jin dad'in xaman ko irin fita hka ba tayi duk kad'aici ya ishe ta, ai kuwa yau Bayan musaddiq ya fita hospital ne ta yanke hukuncin fita ko da iya layin da suke ne ta d'an wasa kafafun ta, tana sanye cikin wata gown milk colour tayi rolling kanta da green veil mai d'an haske flat shoes ne a k'afar ta sai phone nata a hannu da hka ta fito tana kallon yanayin unguwar da yayi matuk'ar birge ta.
Ita kad'ai take murmishi sai kalle kalle take hankalin ta kwance iya layin da suke ta tsaya a karshen shi kafin ta jiyo ta dawo sai da ta kusan shiga gida ne wani bature ya matso inda take kamar xai rungume ta yana cewa
"hey babe you're so beautiful, what's u name ?"
A d'an tsorace mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi tana kok'arin matsawa taji an taka wani uban birki a wajen, nan mufidah ta k'ara rud'e wa don Sauran kad'an a kwashe ta da mota, d'ago kan da xata yi ta hango musaddiq yana fito wa daga motar kamar wani xaki yanda ya wani fusata fuskar nan a d'aure babu alamar fara'a gashi idon shi sun ja inda suke ya nufa kafin ya k'araso mufidah ta afka cikin gidan a tsorace jikin ta har rawa yake yi ta wuce bedroom da gudu ta rufe tana haki xuciyar ta na bugawa da k'arfi don bata ta6a ganin musaddiq a wannan yanayin ba.
Batasan ya suka k'are da baturen ba tana nan xaune wajen mintuna 15 taji gidan tsit alamun baya gidan wata ajiyar xuciya ta sauke ta kwanciyar hankali kafin ta shiga toilet ta watsa ruwa don tafi jin dai dai tana fitowa taji wata kishirwar ruwa ta kamata ga ba ruwa a d'akin tana d'aure da towel d'in ta fito xuwa parlour ta bud'e frige ta d'auki bottle d'in ruwa rufe frige d'in da xata yi ta jiyo ta ga musaddiq a gaban ta, batasan lokacin da bottle d'in ruwan ta fad'i ba ta dafe kirjin ta a tsorace saboda irin kallon da taga yake bin ta dashi.
Matsa wa baya ta fara yi a hankali yana bin ta a baya har sai da ya k'ure ta a jikin bango ganin bata da wata mafita yasa ta bud'e baki cikin rawar murya tana cewa
"mus......musaddiq ka.....ka tsaya nayi maka ba.... bayani ni wlh ban.....bansan shi ba kawai........"
Kasa k'arasa maganar tayi ganin ya d'aga hannun shi sama da sauri ta runtse idanun ta tana cikin tsoro don tasan marin ta xai yi, gaban ta yana wani mugun bugawa, jin shiru bata ji saukar marin ba yasa ta bud'e idon ta d'aya a tsorace tana kallon shi ganin kallon da yake mata yasa ta sake runtse idon da k'arfi cikin tsoro.
Hannun shi ya sanya a saman fuskar ta sai jin shi tayi yana Shafa fuskar ta tare da gyara mata gashin ta da ya manne mata a fuskar, sake runtse idon tayi da k'arfi jikin ta yana rawa saboda jin yanda yanayin ta ya fara canja wa tana sauke numfashi da sauri sauri, sai da ya gama gyara mata gashin fuskar ta ta fito sosai kafin yace
"waya baki ixinin fita daga gidan nan, har wani ya tsayar da ke? "
Shiru tayi mishi ta kasa magana jin hka ya shi cewa cikin tsawa
"kina jin ina miki magana kin min shiru I'll slap u mufidah idan baki yi min magana ba ?"
Gaba d'aya ta sake rikice wa da tsawar da yayi mata aikuwa ta fad'a jikin shi tare da rukunkume shi tana kuka sosai, lokaci d'aya yaji wani irin shock a jikin shi dif yayi shiru yana sauraren kukan ta da ya fara sanyayar mishi da jiki, cikin kukan muryar ta na rawa tace
"ka...... kayi ha.....hak'uri don Allah ni bani ce na kula shi ba baxan k'ara fita ba "
Baisan sanda ya k'ara rungume ta ba yana bubbuga bayanta tare da cewa
"it's okay kada ki k'ara hkan "
Gid'a kanta tayi tana sauke ajiyar xuciya sun d'auki en mintuna a hka kowannen su yana sak'a abu cikin xuciyar shi kafin kuma su ankara cikin sauri kowanne ya janye jikin shi kamar had'in baki, a tare kuma suka harari junan su mufidah har da murgud'a baki.