← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 54

Sashe 41

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Musaddiq wanda hankalin shi yayi kitchen inda mufidah take sai kawai ya mik'e tsaye yana cewa
"mumy bari na d'auko ruwa a kitchen "
Yana gama fad'in hka yayi gaba da d'an saurin shi, yayin da mumy ta bishi da kallo tana murmishi tare da girgixa kai tun xuwan shi ta gama karantar shi yanda yake rawar jiki da irin kallon da yake bin ta dashi.

Yana shiga kitchen d'in ya jingina bayan shi jikin bangon kitchen d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi yana aikin kallon ta jin shi yake kamar yaje ya rungume ta a cikin jikin shi ko ya samu relief acikin xuciyar shi da gangar jikin shi, sai da ya kalle ta son ranshi ya more kafin kuma ya bud'e bakin shi yace
"sannu da aiki malama idan kin gama ina buk'atar gyaran bedroom d'ina da bathroom "

Kunnen uwar shegu mufidah tayi dashi ko jiyo wa ba tayi aikin da take ta cigaba kamar batasan da wani mutum a kitchen d'in ba, ganin hkan da musaddiq yayi ne ya sanya shi nufar inda take tare da sanya hannu ya janyo jelar gashin kanta wata er k'arar axaba ta saki tare da runtse idon ta tace
"malam lafiar ka qlau ne da xaka ja min gashi "
Ta k'arasa fad'in hka tana kici kicin kwatar gashin ta da ya rik'e, sai kawai ya janyo ta cikin jikin shi lokaci d'aya ya saki ajiyar xuciya daman abin da yake buk'atar yi kenan shi yasa ya dad'a tsokano ta.

D'aure fuska yayi tare da cewa "ke kina jin ina miki magana ki rabu da ni saboda kin raina ni koh ?"

"ni malam ka cika ni idan ba hka ba xan..... "
Bata k'arasa fad'in maganar ba ya sanya hannun shi ya rufe bakin ta tare da cewa
"me xaki iya yarinya ji yanda kin kasa kwatar kan ki kina wani ma......."

Wata er k'ara ya saki kad'an wadda ta hana shi k'arasa maganar shi ashe mufidah ce ta cije shi a hannun ba shiri ya sake ta kafin yayi wani yunk'urin rik'e ta har ta fice daga kitchen d'in da gudu..............

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM

LIKE AND COMMENT'S FB PAGE 👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

*PAGE 48*

Wani kyakkyawan murmishi ya saki tare da bin hannun nashi da kallo wurin da ta cije shi har wajen ya d'an yi ja, bakin shi ya kai a hankali ya sumbace shi kafin ya fita daga kitchen d'in.

Suna xaune da dare a parlour kallo suke jefa jefa mumy da musaddiq suna er hirar su yayin da mufidah kuma ta fara gyangyad'in bacci a wurin saboda gajiyar da tayi afnan ma tana jikin musaddiq tana bacci.

"mufidah tashi ki tafi bedroom ki kwanta "
Cewar mumy da ta kula da gyangyad'in da take, ai kuwa da sauri ta d'an mik'e ta wuce xuwa bedroom musaddiq ya bi ta da kallo cikin tsantsar kaunar ta.

Maganar da mumy tayi mishi ita ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tana mai cewa
"musaddiq na gaji da maganar da nake maka don ka xo ka d'auki mufidah kak'i tsayawa kana yi wa mutane hanya hanya, dalilin da yasa ni da daddyn ka muka yanke hukuncin kawo maka ita nan, Sauran kuma k'i kula dasu yanda ya kamata ga amanar su nan na baka kada ka wulak'anta min 'ya kaji na fad'a maka "

D'an murmishi ya saki cikin xuciyar shi yana cewa mumy dan bakisan irin son da nake yiwa mufidah ba shi yasa kike fad'in hka, na tabbatar da kinsan irin yawan son da nake mata da baxa ki fad'i hka ba, baxan iya wulak'anta mufidah ba ko wani ne naga xai wulak'anta min ita sai inda k'arfi na ya k'are bare ni, a fili kuma sai yace
"mumy ki kwantar da hankalin ki kada ki damu xan yi duk yanda kike ce "

"Yawwa Alhmdlh naji dad'i da ka fad'i hkan, Allah yayi muku albarka ya baku xaman lafia"

"Ameeen thumma Ameeen mumyn na "

Murmishi mumy ta saki na jin dad'in ganin d'an nata hankalin shi ya kwanta gashi har er k'iba ya d'an yi alamun ya samu kwanciyar hankali da nutsuwa.

"sannan kuma kayi kok'arin sanya afnan a skul "
"angama mumy na "
Sun d'an jima suna hira kafin kuma kowannen su ya tafi d'aki don yin bacci tun da dare yayi.

Ranar musaddiq yayi kwanan farinciki da jin dad'i tun da ga mufidahn shi a cikin gidan, yana son mufidah so irin wanda ba'a iya kwatan tashi so irin wanda baki baxai iya furta shi ba so irin wanda idan ya kama xuciyar mutum baya ta6a iya yi mishi ta sauk'i kai so so ne irin wanda kafin a samu mutum mai irin wannan son akan mace acikin dubban jama'a sai en k'alilan, da wannan tunanin bacci yayi awon gaba da shi cike da mafarkan mufidah da shi masu dad'i wanda har bai so gari ya waye ba dama xai dawwama a irin hka da yayi farinciki mara misaltuwa.

A hka mumy tayi kwanaki ukun ta, ranar da xata tafi ne da safe suka fita dukkanin su domin raka mumy yin siyayya a mall, da yake jirgin su tashin yammaci xai yi don hka suna gama breakfast suka fito.

A wani babban mall suka yi masauki nan mumy ta fara siyayyan abin da take buk'ata, shi kuma musaddiq ya nufi 6angaren wajen sleeping dress dasu underwears xuwa English wears yana xa6ar duk wanda yayi mishi.

Mufidah kuma da afnan suna tare da mumy suna xa6ar abin da suke so, sam mufidah batasan musaddiq ya nufi 6angaren wajen English wears ba sai ta nufi nan tana d'an dudduba wa, kamar ance ta d'ago kanta ai kuwa tayi mummunan gani da idanun ta, wanda lokaci d'aya wani axababben kishi ya turnik'e mufidah lokacin da ta hango musaddiq rungume da wata mace baturiya a jikin shi.

Gaba d'aya sai ta rasa abin yi har wani duhu duhu take gani a idanun ta sam ta kasa dauke idanun ta daga kansu wani bakinciki da takaici ne ya kama mufidah, d'ago idanun shi yayi musaddiq ya hango mufidah a tsaye waje d'aya kamar wadda aka dasa ta, hannun shi yasa ya janye yarinyar gefe d'aya kafin yayi mata magana ta tsayin second biyar ya nufo inda mufidah take.

Ganin har yaxo inda take batasan ma yaxo wajen ba yasa shi yin tafi da hannun shi biyu a dai dai fuskar ta tare da cewa
"hey are u alright? "
Yana wani shegen murmishi mai da idanun ta tayi kan fuskar shi ai kuwa ya kashe mata ido d'aya tare da d'aga gira, wani bak'in ciki da 6acin rai ne ya sake kama mufidah ganin ko ajikin shi abin da ta kamashi yana yi, ta ma kasa cewa komai ji tayi ya kama hannun ta da hannun shi ai kuwa ta fisge da k'arfi tayi gaba yana yi mata magana amman ko jiyo wa ba tayi ba, wani d'an sanyi yaji cikin xuciyar shi idan dai har hasashen da yayi hka ne to mufidah ta fara son shi tun da abin da ta nuna yanxu yayi alama da kishi, juya wa yayi ya d'auko kayan da ya gama xa6a ya nufo inda su mumy suke.

Waje d'aya mufidah ta samu ta xauna har mumy ta gama siyan abin da take so musaddiq ya biya kudin suka fito, ko kallon inda yake mufidah bata yi ba fuskar ta tayi d'an ja saboda 6acin rai har mumy tana tambayar ta lafia kawai sai ta d'an wayance da fad'in kan ta ne yake ciwo sai sannu mumy take mata har suka k'arasa gida.

Cikin bedroom ta shige ta fad'a toilet ta rufe da key kafin ta kunna shower ruwa ya fara xuba sannan ta fashe da kuka sosai tayi hkan ne don kada a jiyo sautin kukan ta, bata ta6a xaton son musaddiq yayi k'arfi hka a cikin xuciyar ta ba sai yau bata ta6a xaton tana da mugun kishi ba sai yau, taji ana fad'ar kishi amman batasan shi ba sai yau, daman hka musaddiq d'in yake d'an iska ne ma nemin mata, to idan ba ma nemin mata ba mai ya kai shi rungume macen da ba matar shi ba a jikin shi daman abin da yake aikata wa kenan shi yasa ya mak'ale a k'asar waje yak'i dawowa nigeria, ae kuwa baxan iya xama da maxinaci ba dole ya sake ni naje na auri kamilin namiji kamar sadeeq.

Sadeeq baka San halin d'an uwan ka ba ne shi yasa kabar wasiyyar na aure shi me yasa kayi min hka sadeeq ina da kishi baxan iya xama da musaddiq ba, gashi son shi yayi min mugun kamun da ban ankara ba sai da lokaci ya fara k'ure min, tayi kuka sosai mufidah a wannan lokacin abin tausayi gashi sai knocking ake yi a kofar toilet d'in wanda ta sani tsakanin mumy da afnan ne suke yi.

Kan ta ne ya fara wani irin ciwo ga idon ta sun kumbura sosai sun ja dakyar ta iya yin wanka ta sanya wata white d'in rigar wanka kan ta kuma wani k'aramin towel ne ta nannad'e gashin ta, tsayin rigar wankan iya cinyar ta ya tsaya da hka ta bud'e kofar toilet d'in ta fito, d'ago kan da xata yi ta had'a ido da musaddiq a tsaye bakin kofar toilet d'in ya hard'e hannun shi a kirjin shi ya tsurawa kofar toilet d'in ido yana tunani, ganin ta fito ne yasa shi sakin wata ajiyar xuciya tare da cewa

"lafian ki qlau kika shiga toilet kika rufe wajen 1:30 hour kina ciki? "
Wata harara ta dank'ara mishi da idanun ta jawur da suka kumbura, tuni musaddiq ya rikice ya nufi inda take yana cewa

"subhanallah mufidah mai ya sami idanun ki hka? "
Hannun ta ya sake rik'o wa saboda ganin tak'i kula shi ae kuwa ta sanya k'arfin ta ta sake fisgewa cikin dushashshiyar muryar ta tace
"malam ka rabu da ni ina ruwan ka da abin da yake damuna? "
Chapter 41 · 0% Book details