← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 54

Sashe 13

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wani irin yana yi daddy yace"kash da ace nasan da hka tun wuri da koda kaf dukiya ta xata k'are sai na nema wa musaddiq auren yarinyar nan"

"Sannan daddy don Allah kada a fad'a wa Yah sadeeq abin da yake damun musaddiq saboda xai iya shiga wani hali kusan makamancin abin da yake damun musaddiq"

"Kwarai kuwa muh'd maganar ka hka take,don idan sadeeq ya sani xa'a yi biyu babu, yanxu mene mafita?"

D'an satar kallon mumy Dr muh'd yayi taga kallon shi kawai take nan gaban shi ya cigaba da fad'uwa don da alama bata yarda da abin da yake cewa ba, d'an shiru suka yi na en mintuna kafin muh'd yace
"Mafita anan shine daddy ya kamata musaddiq yayi nesa da gida don yafi samun nutsuwar xuciyar shi, kuma hkan da xa'a yi xai taimaka wajen kada Yah sadeeq ya gane"

"Kamar ya ya?"
Cewar mumy, gaban Dr muh'd ne ya cigaba da fad'uwa yana tsoron kada su k'i amince wa don xaman musaddiq a gida xai iya kawo baraxana da rayuwar shi, tun da Yah sadeeq a cikin gidan nasu xai xauna kuma musaddiq da mufidah xasu na had'u wa da junan su, shine ya kawo wannan shawarar yana fatan su daddy su amince da hkan.

"Ina nufin musaddiq ya d'an yi nesa da gida, yanda xai fi samun hutu da nutsuwa a tare dashi xuwa na wani d'an lokaci, kuma naji yana cewa akwai wani course da xai yi kun ga hkan xai rage mishi tunani sosai"

"Good idea muh'd hkan xa'a yi kuwa, Allah ya tashi kafad'un shi"
"Ameeen thumma Ameeen"
Cewar mumy da Dr muh'd, nan suka xauna shiru kowannen su da tunanin da yake a cikin xuciyar shi.

Wayar daddy ce ta d'auki k'ara sauran d'auka yayi ganin sunan sadeeq ne yasa shi d'auka, daga can 6angaren sadeeq ya fara magana cikin shagwa6a yana cewa
"Daddy ina ka shiga kai da mumy da my sweet brother ne ban gan ku ba ne?"

D'an murmishin yak'e daddy yayi tare da cewa"muna nan fah, yanxu ina kake my son?"
"Ina kwance a bedroom d'ina ina huta wa, yunwa nake ji daddy gashi ban ga mumy ba"

Kallon mumy daddy yayi kafin yace"okay sadeeq yanxu mumy xata kawo maka abincin"

"Okay daddy, ina musaddiq ne rabo na da ganin shi tun da muka taho wurin d'aurin aure, ina son ganin shi daddy ina ya shiga ne, wayan shi baya shiga?"

Kallon musaddiq daddy yayi idanun shi sun ciko da hawaye, da ace sadeeq xai san halin da musaddiq yake ciki da shima xai iya shiga halin da musaddiq yake ciki, hannun shi yasa ya goge hawayen da suka xubo mishi kafin ya saita muryar shi yace
"Kada ka kasa damuwa a ran ka son, musaddiq yana tare da Dr muh'd a hospital suna wani aiki but xuwa yamma xai dawo"

Murmishi sadeeq yayi tare da cewa "okay daddy bye"

Kashe wayar daddy yayi tare da kallon Dr muh'd yace "xuwa yamma xai iya farka wa muh'd?"
"Ehhh daddy xai farka insha Allah"
Cewar muh'd kenan, juyo da kallon shi yayi kan mumy ya ce" sadeeq yana neman mu fah, yace ma yunwa yake ji ki bashi abinci, yanxu tashi xaki yi mu tafi gida ya ganmu idan yaso ni na dawo hospital d'in"

Girgixa kai mumy tayi tare da cewa "gaskia baxan iya tafia ba, sam baxan samu nutsuwa da kwanciyar hankali ba idan na tafi"

" hak'uri xaki yi mumyn sadeeq addu'a xaki na yi mishi Allah ya bashi lafia, idan kika k'i tafia sadeeq xai iya fahimtar halin da ake ciki"

Nan daddy ya lalla6a mumy dak'yar ta amince suka tafi aka bar Dr muh'd a wurin musaddiq wadda yake kwance ko motsi baya yi.

Bayan sun koma gida mumy ta had'a abinci ta kaiwa sadeeq lokacin yana kwance kan sofa suna hira da Yah Omar a waya, ganin mumy yasa shi katse wayar da yake yi, tsaf ya karanci tsantsar damuwa a fuskar iyayen nashi amman sai suka nuna mishi gajiyar hidimar biki ce ta sa yanayin su ya koma hka, daga k'arshe daddy ya koma asibiti aka bar mumy tana tare da en biki amman gaba d'ayan ta ba'a nutse take ba hankalin ta yana kan musaddiq addu'a sosai take mishi a cikin xuciyar ta lokaci xuwa lokaci tana goge hawaye a idanun ta idan ta ke6e ita d'aya.

Sai 7 na dare musaddiq ya farka lokacin daddy da Dr muh'd suna masjid basu dawo ba, bayan mintuna biyu da farkar wasu ya samu nutsuwa sai ya sanya hannu ya xare drip d'in da ake sanya mishi sannan ya tashi daga kan gadon cikin jarumta da dauriya ya fara tafia xuwa toilet don gaba ki d'aya jikin shi ba k'wari, wanka yayi da ruwa mai d'umi sannan ya d'aura alwala ya fito kayan jikin shi ya mayar tukunna ya fara rama sallolin da ake bin shi, har ya kammala rama su, xama yayi yana laximi, saitin xuciyar nayi mishi wani rad'ad'i, addu'a kawai yake idan tunanin ta ya fad'o mishi a cikin xuciyar shi don k'okarin yakice ta yake gaba d'aya a ranshi don yanxu ta xama matar d'an uwan.

Yana xaune a hka daddy da Dr muh'd suka shigo d'akin, ganin shi a xaune akan abin sallah ya basu mamaki sosai don hka da sauri suka k'arasa wajen shi suna mishi sannu, murmishi yayi tare da amsa wa, kafin kuma Dr muh'd ya sake duba shi, anan kuma suke fad'a mishi shawarar da suka yi, sosai musaddiq yaji dad'in hkan don yana so yayi nesa daga rayuwar mufidah, daga hka suka tafi gida don baya son xaman asibitin, lokacin da suka k'arasa gida a dai dai lokacin en kawo amarya motocin su suka shigo gidan.

Musaddiq bai tsaya ba ya shige part d'in daddy da wani irin mugun sauri har abin ya bawa daddy mamaki, Dr muh'd kuwa ya bi bayan musaddiq da sauri shi ma, duk abin da ya faru da musaddiq da yanda yayi duk akan idanun mumy dake saman bene tana kallon su nan xuciyar ta ta dad'a ayyana mata abubuwa, har sai da suka shige sannan mumy ta iya sakkowa down stairs don tar6ar amarya duk jikin ta a sanyaye.................

_kuyi hak'uri da wannan nayi typing ya goge sai da na sake, xuwa gobe insha Allah xaku ji ni_

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*

_Wannan shafin na kune *BAIWA WRITER'S ASSOCIATION*, ina mik'a sak'on gaisuwa ta a gare ku, manyan writer's da k'ananun su, Allah ya k'ara had'e kan marubutan mu ya kauda fitina a tsakanin mu, hak'ik'a ina alfahari ku, ina yiwa kowa fatan alkhairi_🤝😍

*PAGE 18*

Har sai da suka shiga cikin part d'in sadeeq, amman musaddiq bai sani ba don gaba d'aya hankalin shi baya tare dashi baisan inda yake jefa kafar shi ba don kawai muh'd yake bi wanda yake rik'e da hannun shi, suna shiga cikin palon sadeeq yace

"Ku xauna bari na kirawo muku ita koh my brothers?"
Cikin murmishin yak'e Dr muh'd yace"toh babban yaya a fito lafia"

Murmishi sadeeq yayi tare da shige wa bedroom d'in mufidah, shi kuwa musaddiq maganar da sadeeq yayi ita ta dawo dashi cikin hayyacin xumbur ya mik'e tsaye tare da wani fisge hannun shi daga rik'on da muh'd yayi mishi yana k'are wa inda yake kallo.

Cikin sauri muh'd yace"lafia musaddiq?"
Kafin ma ya rufe bakin shi musaddiq ya fice daga palon da wani irin gudu, kafin ya ankara har musaddiq ya fice daga part d'in cikin sauri Dr muh'd ya mik'e xai bishi kenan sai ga sadeeq ya fito tare da mufidah, kallon muh'd yah sadeeq yayi tare da cewa

"Sorry k'anina na bar ku ko, ina musaddiq kuma?"

Ambatar sunan musaddiq da aka yi sai da gaban mufidah ya fad'i, shi kuwa muh'd ya rasa mai xai cewa sadeeq, daga k'arshe dai da yaga sadeeq ya tsare shi da ido yasa shi yin murmishin yak'e tukunna yace
"Gajiya yayi da xaman jira gashi kanshi yana ciwo shine ya tafi yasha magani ya kwanta don ya huta"

"Wayyo kanshi ne yake ciwo Allah sarki brother bari naje na ga jikin nashi, ina xuwa muh'd"

Muh'd wanda gaba d'aya hankalin shi yayi kan musaddiq ya rik'o hannun sadeeq yana cewa
"Ah babban yaya ba sai kaje ba xan je yanxu wurin shi kafin na tafi, idan ta kama ma xan k'wana wurin shi don na kula dashi, amman kayi xaman ka"

Dafa kafad'ar shi sadeeq yayi tare da cewa"okay naji amman don Allah ka kular min da shi sosai please"

"Kada ka damu xan kula shi insha Allah"
"thank u so much muh'd ina jin dad'in yanda kake kular min da musaddiq Allah ya bar mu tare"

"Ameeen babban yaya"
Kallon mufidah yayi tare da cewa"Auntyn mu ya hidimar biki?"
Dak'yar mufidah ta iya bud'e baki tace"Alhmdllh"

Don gaba d'aya mufidah ta rasa abin da yake mata dad'i, bayan sun gama gaisa wa ne tukunna yayi musu addu'a sosai ta xaman lafia da xuri'a mai albarka daga hka yayi musu sallama tare da fito wa daga part d'in sauri yake ya k'arasa wajen musaddiq.

Yana tura kofar bedroom d'in musaddiq d'in ya tarar dashi a kwance kan bed yayi ruf da ciki, da sauri muh'd ya k'araso inda musaddiq yake a kwance yasa hannun shi ya jiyo dashi, ba k'aramin firgita muh'd yayi ba ganin hawaye na xuba a idanun musaddiq gaba d'aya fuskar shi da idanun shi sun yi ja.

"Haba musaddiq why da xaka dunga barin abu yana tasiri a cikin xuciyar ka, ina son kayi hak'uri ka cire mufidah daga ran ka gaba d'aya ta riga da ta xama mallakin wani, wanin ma d'an uwan ka yayan ka, tun kafin a fara fahimtar halin da kake ciki, don mumy sam bata yarda da abin da nace musu ba daddy ne kawai ya aminta"

Dr muh'd ya fad'i hka yana goge wa musaddiq hawayen da suke xaba a idanun shi, shima hawayen yake fitar wa, cikin rawar murya musaddiq yace

"Ya xan yi muh'd, ji nake xuciya ta tana wani irin xugi da rad'ad'i, ni dama Allah xai d'auki r........."
Chapter 13 · 0% Book details