← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 54

Sashe 38

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idanun ta cike taf da hawaye tace "tohhh umma "
Nan umma ta dunga yi mata nasiha tare da bata shawarwari masu amfani wanda tasan xai taimaka musu wajen kwanciyar hankali da xaman su lafia (wanda wasu iyayen sam basu damu da hkan ba, ace 'yar ki xata yi aure ko kuma tayi auren baxa ki xauna da ita ba a matsayin ki na uwa ki bata shawarwari masu amfani wanda xai taimake ta a rayuwar auren ta, kina nuna mata mahimmancin miji kina nusar da ita abubuwan da ya kamata wanda ya dace da tayi da wanda bai dace ba, ki janyo 'ya'yan ki jikin ki su Saba da ke sosai ta yanda duk wata shawarar ta ke xata tunkara ba sai k'awa ba wadda mybe k'awar ta d'ora ta kan wata hanyar ba mai 6ille wa ba, don hka iyayen mu mata a kula mu kiyaye wajen kula da yaran mu, tarbiyyar su, tsabta, koya musu girki, girmama na gaba dasu, uwa uba basu ilimi na addini dana boko, Allah yasa mu dace Ameeen.)

Bayan umma ta gama yi mata nasiha tare da bata shawarwari ne daga karshe tace
"ki je dining table akwai abinci sai ki xa6i abin da kike so "

Tashi mufidah tayi tana d'aukar bag d'in ta tana cewa "Yawwa umma na kamar kinsan yunwa nake ji "
Da kallo umma ta bi ta cikin mamaki kafin tace
"wannan jakar fa ta me ce? "
D'an waro idanun ta tayi tare da cewa
"laaa umma na dawo nan sai su mumy sun dawo xan koma "
"shi kuma mijin na ki wane xai kula dashi tun da hajia khadija bata nan? "
Tsit mufidah tayi kafin daga bisa ni tace "umma ni wlh tsoro nake ji ni kad'ai, don Allah ki bar ni na kwana anan "
Ta k'arasa maganar da shagwa6a, Kallon ta umma tayi kawai tana girgixa kai sam mufidah idan tana gaban ta nuna wa take kamar Er k'aramar yarinya.

Ganin umma bata ce komai ba yasa da sauri ta bar wurin bedroom d'in ta ta nufa ta ajiye bag d'in da cire hijab d'in ta, fito wa parlourn tayi a dining ta xauna ta had'a tea tana sha gefe d'aya kuma ta d'ebi plantain and egg tana d'auka da fork tana ci hankalin ta kwance, sai da ta gama ci tukunna ta nufi kitchen wajen nabilah wadda take kok'arin had'a kunun gyad'a don tun da ta samu ciki bata da wani abin so sama da ta sha kunun gyad'a.

D'an bugun ta a kafad'a mufidah tayi tare da cewa
"ke wannan cikin da son kunun gyad'a ya xo miki, abin da bakya son shi ma"
"uhm ke dai bari kawai Mrs musaddiq yanxu idan ban sha wannan kunun gyad'ar ba hka xan yini babu cin abinci don ji xanyi sam bana sha'awar wani abin "

Girgixa kai mufidah tayi tare da cewa "wayyo k'awata Allah dai ya raba lafia, amman cikin muhibbat bai baki wahala kamar hka ba "

"gaskia kuwa don ban sha wahala ba sai kwad'ayin tsiya don har my dear sai da ya fara yi min tsiya akan kwad'ayin, don bini bini nace abu kaxa nake so sai kuma yaje ya nemo min hankali xai kwanta "

Nan dai mufidah ta kar6i aikin kunun gyad'ar nabilah ta samu waje ta xauna suna er hirar su har ta gama dama shi ta xuba acikin flaks Bayan ta xuba wa nabilah a cikin cup ta had'a mata da sugar and milk.

"ke baxa ki sha ba? "
Cewar nabilah suna kok'arin fita daga kitchen d'in, girgixa kai mufidah tayi tare da cewa
"na k'oshe yanxu mybe sai xuwa anjima"
A cikin parlour suka xauna hira suke sosai tsakanin su har da umma.

*** *** ***

Musaddiq bai dawo gidan ba sai wurin 12 na rana don hospital suka fita, yana dawo wa gidan jikin shi ya bashi mufidah bata gidan, kuma yasan gidan su ta tafi don hka bedroom d'in shi ya shiga xama yayi tare da bud'e laptop d'in shi ya fara aiki a jikin ta, sai da ya d'auki a k'alla tsayin mintuna 60 yana aikin kafin ya gama, alwala yayi ya tafi masallaci yayi sallahr axahar, kafin ya dawo gida.

Bedroom d'in shi ya koma yunwa yake ji sosai ko breakfast bai yi ba, frige ya bud'e ya lalubo fresh milk mai sanyi yasha kafin ya kwanta a gajiye daman bai samu cikakken bacci jiya ba da dare don hka nan da nan bacci ya dauke shi mai nauyi.

Ya dad'e yana bacci don sai wurin 5 na yamma ya tashi wanka ya fara yi agurguji ya xura jallabia sallahr la'asar yayi ya fara gabatar wa a makare ya dad'e yana addu'o'in shi kafin ya tashi ya fara shirya wa.

Tsab ya fito cikin wata kuftan blue black d'inkin rigar irin iya gwiwar nan tsayin ta sosai kayan su kar6e shi abin ka fari kunsan kalar tana yiwa farare kyau, agogo da takalmi bak'ak'e yayi amfani dashi hular shi itama bak'a ce mai ratsin blue and white a jiki ya wani turo ta gaban gashi yana Kallon kanshi a mirror ya tabbatar komai yayi yanda yake so sannan ya fesa different colour's perfumes a jikin shi tukunna ya d'auki car key da phone's nashi ya fito, cikin car d'in shi ya shiga tare da yi mata key ya bar gidan.

Gidan su mufidah ya nufa yana parking a cikin gidan ana kiran sallahr mangarib, a lokacin ya Omar da abba suka fito xasu tafi masallacin kusa da gidan, musaddiq ya fito har k'asa ya tsugunna ya gaida abba yayin da suka yi musabiha da yah Omar daga nan kuma suka wuce masallaci, sai after ishsha suka bar masallacin suka nufi gida.

Da fara'a umma ta tarbi musaddiq suka gaisa kafin a tsunduma hira, mufidah tana bedroom batasan musaddiq ya xo ba, gama girkin daren da suka yi da umma kenan ta taho yin wanka.

Bayan tayi wanka ne ta shirya cikin wata gown mai hannun vest purple colour ce tayi mata kyau ta gyara gashin ta tare da sanya mishi ribbon bata yi wata kwalliya ba daga powder sai wet lips mai k'amshin apple Bayan ta fesa perfumes ne ta fito xuwa parlour cikin takunta na nutsuwa.

Sam bata kula da musaddiq ba tayi wajen dining table tana cewa "abba, umma ku taho mu ci abinci na fara jin yunwa "
A shagwa6e take maganar, har ta k'arasa dining d'in ta fara serving d'in su hankalin ta kwance sai dai sometimes ta d'an jin gaban ta yana fad'uwa.

"musaddiq taso mu ci abinci "
"toh abba "
Ya fad'i hkan yana tashi don Allah Allah yake ya k'arasa wajen da mufidah take don yayi mata Kallon da xai more son ran shi don ba k'aramin kyau tayi mishi ba.

Lokacin da suka k'arasa kan mufidah yana sunkuye tana xuba musu abincin, bayan ta gama xuba wa ta d'ago kanta tana cewa
"umma na abba n........ "
Sauran maganar mak'ale wa yayi a fatar bakin ta dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana yi mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban..............

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻£xclusive writers forum

Like and comment's fb page

#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

*PAGE 46*

Sauran maganar ta mak'ale a fatar bakin ta bata k'arasa ba dalilin had'a ido da musaddiq da tayi yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban, ita ma mufidah sai ta kasa dauke idanun ta a kanshi suka tsaya kallon junan cikin wani irin shauk'in junan su don kallo d'aya mutum xai yi musu ya tabbatar suna masifar son junan shi.

Abba ne ya ta6o umma tare da yi mata nuni da su mufidah suna kallon junan watak'il ma sun manta a ina suke, murmishi umma tayi kawai tana girgixa kai, gyaran muryar da abba yayi ne yasa su dawowa daga duniyar kallon junan su da suka tafi.

Sai kuma musaddiq ya fara sosa kai irin na jin kunya tare da xama, yayin da mufidah ita ma kunya ta Kama ta har sai da ta dalla wa musaddiq harara tare da murgud'a mishi baki, d'aga mata kafad'a yayi irin ko ajikin shi kafin ya rama hararar da tayi mishi.

Mufidah kasa sake wa tayi taci abinci daga karshe ta xame ta tsere bedroom d'in ta, sai bayan ta tafi ne tukunna musaddiq ya iya cin abincin don shi fa idan mufidah tana gaban shi kasa yin komai yake, yana cin abincin yana tuna irin kallon da suka yi junan shi yana murmishi shi kad'ai.

Bayan sun gama ne suka dawo cikin parlour ana er hira har xuwa 9 na dare, kafin musaddiq ya ce

"umma a kirawo mufidah mu tafi na ga dare nayi "
Kafin umma tayi magana abba yace
"ga bedroom d'in ta can shiga ka kirawo ta "

D'an sosa kai tare da cewa "okay abba "
Ya wuce cikin nutsuwa ya nufi stairs d'akin mufidah.

"yaran nan suna son junan su sosai, amman ban san me ya hana su bayyana wa kansu ba suka barshi cikin xuciyar su "
Cewar abba, umma kuma tace
"mybe basu yi shak'uwar da xasu furta wa junan su ba, tun da wannan auren had'a su akayi ba tare da ra'ayin d'ayan su ba"
"baki san saboda son 'yar ki da musaddiq yake ba har ya kamu da ciwon xuciya "

D'an xaro ido umma tayi na mamaki tace "shi musaddiq d'in? "
"kwarai kuwa "
Abba ya tabbatar mata da hkan, kafin ya kwashe labarin komai ya fad'a wa umma wanda shi ma muh'd ne yake sanar mishi, wani tsananin tausayin musaddiq ne ya kama umma sosai, ta kasa ma magana sai jujjuya kai kawai take irin yanda idan labari ya bugi mutum sosai yake yi.
Chapter 38 · 0% Book details