← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 54

Sashe 46

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tura kofar bedroom d'in yayi ya hango ta kwance kan bed ta kudundune cikin mamaki yace
"Mamin Afnan lafia? "
Jin tayi shiru bata bashi amsa ba ne yasa shi k'arasa wajen da take da sauri, hannun shi ya sanya tare da yaye blanket d'in da ta lullu6a da shi, hannun shi ya sanya saman wuyan ta da sauri ya janye saboda xafin da jikin ta ya d'auka, sake runtse idon ta Mufidah tayi gam ita a dole bacci take batasan hawayen da suke xuba a idanun ta sun fallasa ta ba.

Cikin gigice wa Musaddiq ya ce
"Mufidah xaxxa6i ne yake damun ki? "

Ya sake tambayar ta a karo na biyu but tayi tsit ta kyale shi, ganin hkan da tayi kuwa ba k'aramin sake hargitsa Musaddiq yayi ba, baisan lokacin da ya xauna ba ya sanya hannun dukka biyun ya d'ago ta tare da yi mata maxauni cikin jikin shi lokaci d'aya suka saki wata ajiyar xuciya.

D'ago kanta yayi yana kallon innocent face d'in ta yace
"Mufidah nasan ba bacci kike ba ki bud'e idon ki ki kalle ni, ki fad'a min matsalar ki please "

Wasu hawayen su suka sake xubo wa cikin xuciyar tana cewa Musaddiq babu abin da yake damuna sai halin da kake ciki ciwon da sona ya haddasa maka shi ya sanya ni shiga cikin wannan yanayin, a fili kasa magana tayi saboda yanda bakin ta yayi mata nauyi sosai.

Muryar shi kamar xai fashe da kuka yace
"na rok'e ki Mufidah ki sanar da ni "

"daddy mai ya samu mami na? "
Yaji muryar Afnan cikin tsakar kanshi, wayance wa yayi da k'ak'alo murmishin yak'e yace
"Afnan babu abin da ya sami mamin ki bacci take yi "

"toh daddy I'm hungry "
Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, ya rasa yanda zai yi Afnan zai je ya bawa abinci ko kula ya tsaya kula da Mufidah, ganin Afnan zata fara yi mishi kuka ya sanya shi ajiye Mufidah suka fito parlour yana waigen Mufidah.

Sai da ya zuba wa Afnan abinci a plate tare da drink a cup ya zaunar tare da kunna mata tv channel d'in cartoon ya ce
"babyn daddy kiyi xaman ki anan idan kin gama cin abincin ki kalli cartoon yanxu xamu fito da mamin ki, kin ji? "

Afnan wadda take kai spoon na abinci baki ta gid'a mishi kanta tana murmishi, shima murmishin yayi yana jan kumatun ta na gefen dama kafin kuma ya wuce bedroom d'in Mufidah da sauri.

A yanda take lokacin da ya fita a hka ya same ta da sauri ya k'arasa inda take tare da hawa saman bed d'in ya yaye blanket d'in da ta rufa tare da d'ago ta gaba d'ayan ta ya zaunar da ita cikin jikin shi yana tatta6a jikin tare da duba ta don ya fahimci abin da yake damun ta.

Ganin bashi da kayan aiki cikin bedroom d'in ta yasa shi daukan ta ya nufi bedroom d'in shi da ita, yana bud'e kofar wani sassayan K'amshi mai dad'i ya fara ziyartar hancin kafin ya shimfid'e ta saman bed d'in shi da yasha gyara.

Jiki na 6ari ya fara duba ta bai ga wani babban ciwo fiye da damuwa tare da kukan da tayi ne ya janyo mata xaxxa6in da ciwon kai, zuba mata ido yayi yana kallon ta cikin xuciyar shi yana tunanin wacce irin damuwa ce ta haddasa mata ciwo hka, gashi tak'i magana kuma har yanzu idon ta a rufe suke sai dai hawayen da yake zubo mata.

Nan ya fara lalla6a ta don ta fad'a mishi abin da yake damun ta amman kamar da dutse yake magana, ganin baza ta kula shi ba yasa shi tashi bathroom ya nufa ya samu wani bowl mai kyau ya tari ruwa a ciki sannan ya d'auki towel k'arami ya fito xuwa inda take.

Ajiye bowl d'in yayi saman bedside sannan ya fara kok'arin zame kayan jikin ta, ai kuwa da sauri ta mik'e zaune tare da bud'e idon ta tana rarraba su kamar wata mara gaskiya hkan da tayi ba k'aramin sanya Musaddiq dariya yayi ba amman sai ya gimtse ta.

Ya cigaba da cire wa cikin tsoro Mufidah tace
"Musaddiq mene haka kuma? "
D'an murmishi yayi tare da cewa "jikin shi ya d'auki xafi da yawa ina son xan goga miki ruwa ko xafin ya ragu "

Cikin rawar murya tace
"ni.... ni gas.....gaskiya a'a zai daina "

Wani murmishin gefen kumatu yayi tare da girgixa kanshi yace
"bazai yiwu ba Mufidah idan baki damu da rashin lafiyar ki ba wasu sun damu "

D'ago kanta tayi da sauri ta kalle shi cikin mamaki wato bama xai ce ya damu ba sai wasu da akwai aiki a gaban ta kuwa wajen tankwara zuciyar Musaddiq ya sakko su gyara zaman auren su.

Gira ya d'aga mata kafin ya fara cire kayan runtse idon ta tayi gam har ya gama cire wa sai iya underwears kawai ya bar mata, sake runtse idon ta tare da k'ank'ame jikin ta tana jiran saukar ruwa a jikin ta amman taji shiru har tsayin wasu en mintuna.

A hankali ta fara bud'e idanun ta suka had'a ido kuwa sake rufe su tayi da sauri ganin ashe zuba mata ido yayi yana kallon ta son ranshi wata irin kunya ce ta gama lullu6e Mufidah.

Musaddiq wanda gaba d'ayan shi ya fara fita hayyacin shi ya kasa dauke idon shi akanta, gaba d'aya idon shi sun fara canja launi ga wani abu da yake ji yana tsirga mishi daga cikin brain d'in shi xuwa gangar jikin shi, wani tunani na daban ya fad'a 6angare guda kuma wani mugun son Mufidah ne yake dad'a ratsa zuciyar shi.

Dakyar ya iya saita kanshi ya fara goge mata jikin nata had'uwar tattausar fatar jikin shi da nashi, shi ya sake haddasa Musaddiq shiga wani mayuwacin hali wanda ba don yana kok'arin danne abin da yake ji ba da xa'a yi mai gaba d'aya a yanxu.

Bayan ya gama ne ya mayar mata da kayan sannan ya had'a mata tea a baki ya dunga bata har ta d'an sha tukunna yayi mata allura wanda yasha fama da ita kafin ta tsaya yayi mata, hka magani ma dakyar ta sha sannan ya kwantar da ita cikin jikin shi har bacci ya dauke ta mai nauyi tana jikin shi yana aikin kallon ta lokaci zuwa lokaci yana sakin murmishi shi kad'ai yasan zuciyar shi yanzu ta samu nutsuwa tunda ta sami abin da take muradin so.............

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:[email protected]

*PAGE 54*

Zame ta yayi daga cikin jikin shi ya tare da kwantar da ita kafin ya tashi ya fito xuwa parlour wurin Afnan sai ya tarar ta 6ingire tana shan baccin ta kan carpet, d'an murmishi yayi tare da daukan ta ya kaita bedroom d'in Mufidah ya kwantar da ita, sannan ya fito ya koma d'akin shi.

Kwanciya shima yayi kusa da Mufidah ya rungumo ta cikin jikin shi k'am kamar wanda xa'a kwace mishi ita zuciyar shi fal farinciki wai yau shine rungume da Mufidah wadda ya fitar da ran samun ta har abada sai gashi Allah yayi ikon shi ya same ta a lokacin da bai ta6a zato ba.

Kallon beautiful face d'in ta yake yana hashashen wasu abubuwa cikin zuciyar shi cikin nishad'i yayi kissing lip's d'in ta yana nan kwance yana faman tunani har bacci mai dad'i yayi awon gaba da shi.

*After 1 hour*

A hankali Mufidah ta fara bud'e idanun ta har ta gama bud'e su gaba d'aya ba inda idon ta ya sauka sai kan kyakkyawar face d'in Musaddiq yana baccin shi hankali kwance, tamkar ba bacci yake ba kamar irin lumshe idanun shi yayi.

Wani smiling tayi kaunar shi tana ratsa ilahirin zuciyar ta da jijiyoyin jikin ta, wani mugun son shi ne yake shiga cikin zuciyar, hannun ta ta sanya saman fuskar shi tana kyakkyawan sajen face d'in shi mai matuk'ar kyau da tsari ga laushi har ta kai saman lip's d'in shi tana zagaye su da 'yan yatsun ta, tana murmishi ita d'aya.

Ba zato taga Musaddiq ya bud'e idon shi ya sauke su kan fuskar ta, suka had'a ido yana mata wani irin kallo mai tattare da ma'anoni daban daban.

"wayyo Allah nah, Allah yasa bai ga abin da nake mishi ba?"
Cewar Mufidah cikin zuciyar ta ga wata azababbiyar kunyar shi da ta rufe, d'aga mata gira yayi da sauri ta sunkuyar da kanta tana mai murmishin jin kunya.

'Yar dariya yayi kad'an yana sake hugging d'in ta a kunne ya rad'a mata
"Mamin Afnan ya kika bari ki cigaba kinsan kuwa yanda nake ji kuwa? "

Nok'e kai tayi tana cusa fuskar ta cikin chest d'in shi tana girgixa kai tare da cewa
"ni fa ba abin da nake maka "

Cakulculi ya fara yi mata tana dariya tare da kok'arin kwace kanta daga jikin shi but ta kasa hkan, cikin shashshak'ar dariya tana jan numfashi tace
"Musaddiq ka bari please".
Yana dariya yace
"ai kuwa sai na rama yarinya tun da kika tashe ni a bacci ko na kirawo Afnan mu had'u mu danne ki kowa ya za6i inda yake so ya ciza "

"wayyo Allah kayi hak'uri baxan k'ara ba "
Ta fad'i cikin yanayin shagwa6a, nok'e kafad'a yayi tare da cewa
"nak'i wayon yarinya "

Nan ya cigaba da yi mata cakulculin sai da yaga tana kok'arin shid'e mishi ya barta tana mai da numfashi, ido suka k'ura wa junan su cikin wani irin shauk'in son junan su suke ke kallon junan su kowanne da irin abin da yake sak'awa cikin zuciyar.

Musaddiq kasa jure wa yayi sai da ya had'a lip's d'in shi da nata ya fara kissing a nutse yana yawo da hannun shi cikin jikin ta, saukar lip's d'in shi a nata ne yasa ta lumshe idanun ta tare da sakin wata ajiyar zuciya ya gama saukar mata da kasala.
Chapter 46 · 0% Book details