← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 54

Sashe 35

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Face d'in ta ya tsurawa ido yana kallo wani abu ne yaji yana ratsa shi tun daga kanshi har xuwa kafar shi, yakai wajen mintuna 5 yana kallon ta sai kuma lokacin yaji wani uban kishi don yasan mutane da yawa sun gane mishi mata, kallon picture's d'in kawai yake ji yake kamar yayi tsuntsu ya ganshi a gaban mufidah, sai da ya kalli picture's d'in son ranshi kafin ya turawa da muh'd Cewar

" _Aboki nagode sosai amman ka tabbatar ka goge picture's d'in nan a wayar ka_"

Ya tura mishi ba jima wa muh'd ya turo mishi da reply na dariya kafin yace

" _Hhhh sarkin kishi ae tuni na goge tun lokacin da na turo maka ba sai ka fad'a min ba, ya kamata ka dauki matar ka ko ka dawo nigeria gaba d'aya yaro don wlh aure da dad'i na baka labari yanxu hka gani rungume da sweetheart dina_"

Ya turo mishi hkan tare da alamar gwalo, wani yarrr musaddiq yaji a cikin jikin shi gaba d'aya ya dauke wuta ji yayi wani abu yana ratsa shi wata kasalar ce ta sake lullu6e shi wanda dakyar ya cewa muh'd

" _kai fa wani lokacin d'an air ne kai abin ya dama ni bai dame ni ba_"

Ganin muh'd yana yin typing alamar akwai abin da turo ya sashi kashe datar gaba d'aya don kada ya hargitsa mishi tunani don shi kad'ai yasan abin da yake ji a yanxu dakyar ya iya tashi ya shiga toilet yana cewa
"Muh'd yana neman hargitsa min tunani xuwa wani 6angare na daban wanda bai kamata ace na kasan ce cikin yanayin yanxu ba"
Da hka ya sakarwa kanshi ruwa idanun shi a lumshe mufidah kawai yake hangowa.............

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

LIKE AND DROP UR COMMENTS FB PAGE

#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

_Happy Birthday my billy ladan dear ina taya ki murnar k'arin shekara, Allah ya k'aro shekaru masu albarka, na sadaukar da duk wannan page d'in don murnar wannan ranar, ina miki fatan alkhairi tawan_😍

*PAGE 43*

Daren ranar mufidah bata samu cikakken bacci saboda tunanin auren ta da musaddiq da aka d'aura a yau, ji take kamar a mafarki yau ita ce matar musaddiq mutumin da basa shiri da junan su, me yasa sadeeq ka furta hkan baka san ba ma shiri da juna da k'anin ka ba, taya xamu iya had'a kanmu mu yi xaman aure irin na mata da miji.

Da irin wad'annan tunane tunanen mufidah bacci yayi awon gaba da ita ba tare da ta shirya yin shi ba, musaddiq kuwa ana shi 6angaren ya samu cikakken baccin wanda rabon da yayi irin shi tun lokacin da sadeeq ya furta yana son mufidah, ranar baccin shi yayi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali.

Washe gari en uwa suka tattafi gida ya rage daga mumy, daddy, mufidah da afnan sai en aiki, duk wani motsin mufidah akan idon mumy don tana son karantar yanayin da take ciki, sai kuma aka ci sa'a mufidah ta fito xuwa parlour fuskar ta wasai da ita sai dai kumburi da d'an ja da idanun suka yi mata, wasa take wa afnan suna dariyar su sosae hkan ya faranta wa mumy rai tana mai fatan wannan auren ya dawwama cikin amincen Allah da farin ciki.

Bayan sati d'aya da auren mufidah da musaddiq ne daddy yayi mata magana da ta cigaba da xuwa hospital kafin musaddiq ya dawo, ae kuwa tayi farinciki sosae da hkan a ranar kuma da dare Dr muh'd yaxo gidan tare da matar shi nafisat.

Mufidah bata wani kula shi ba sai nafisat d'in suke yin hira tsakanin su har mumy ta tashi ta shiga kitchen ta barsu bayan sun gama gaisa wa.

Alama muh'd yayi wa nafisat da hannu kan ta bi mumy kitchen, d'an murmishi tayi tare da Kama hannun afnan suka shige kitchen.

Cikin sanyin muryar shi yace
"mufidah kiyi hak'uri nasan ni mai laifi ne a wajen"

D'an ta6e baki tayi kafin tace "uhm muh'd me yasa lokacin da sadeeq yake bar maka wasiyyar na auri musaddiq baka kirawo ni ba, wlh ba don sadeeq ne ya nemi da ka had'a auren mu da musaddiq ba, da tun ranar da aka d'aura auren xaka sanya a warware shi"

Kallon ta muh'd yake cikin zuciyar shi yana cewa da kinsan son da musaddiq yake miki da baxa ki furta wad'annan maganganun ba, kinsan adalilin ki ya kamu da cutar da bata warke wa ina addu'a da fatan Allah ya kaimu lokacin da musaddiq xai furta miki abin da yake cikin xuciyar shi.

A fili kuwa cewa yayi "nima mufidah alk'awarin da na d'aukar sadeeq shi yasa na cika shi, tun daga lokacin da aka d'aura auren naji kamar an cire min wani abu a jiki na da kaina lokacin naji hankali na ya kwanta sosae mufidah "

D'an ajiyar numfashi yayi kafin ya cigaba da cewa
" ina sake baki hak'uri ni dai a adaina fushi dani, sannan kuma naji daddy yayi min maganar komawar ki office ranar monday koh ? "

Cikin sanyi tace "ehhh nima d'axu ya sanar da ni"
"hakan yayi kyau Allah ya taimaka, tun da mun shirya a sakar min fuskar mana irin wannan d'aure fuskar ae sai ki sa na dunga rawar jiki saboda tsoro ki sa matata da mijin ki su raina ni "

Dole tasa ta d'an saki fuskar da murmishi wanda har sai da dimples d'in ta suka lotsa kafin kuma ta harare shi jin ya k'arasa maganar da mijin ta musaddiq.

Er dariya muh'd yayi yana fad'in ko ke fah "

Nan kuma suka cigaba da Er hira har xuwa lokacin da su mumy suka fito a kitchen, sun d'an jima a gidan don sai wurin 9:30 na dare suka tafi bayan sun yi dinner har farfajiyar gidan mufidah ta rako shi suka yi sallama suka tafi ita kuma ta dawo gida.

Acikin hka mufidah ta Fara xuwa hospital tana cigaba da aikin ta cikin kwanciyar hankali kuma hkan ba k'aramin d'ebe mata kewa yake ba don ta d'an rage tunani sosai.

Kamar yau ranar weekend ce mufidah babu aiki tana kwance kan bed bata jin dad'in jikin ta tun safe ga wata muguwar fad'uwar gaba da take damun ta tun safe, afnan ma da ta dame ta da surutu korar ta wurin mumy tayi.

Shigowa mumy tayi cikin bedroom d'in hannun ta rik'e da mayafi alamar fita xata yi, Kallon mufidah tayi fuskar ta dauke da murmishi tace

"mufidah na gama shirya wa xamu tafi, na rasa dalilin da ya hana ki bin mu gashi har afnan xamu tafi "

D'an murmishi mufidah tayi tare da tashi daga kwancen da take tace
"kiyi hak'uri mumy kin ga ranar monday ina da aiki na safe kuma xamu yi muhimmin meeting ranar shi yasa "

Da yake london su mumy da daddy xasu je wajen dubiyar wani babban abokin daddy da aka kwantar dashi acan, sun nemi da mufidah ta shirya su je ta k'i yarda kuma kwanaki uku kawai xasu yi su dawo.

"kin fison dai xaman kawai naga alama, xaki xauna anan ko gidan umma xaki je? "
Da sauri mufidah ta girgixa kai tana d'an waro idanun ta tace

"a'a mumy yanxu xan shirya nima na tafi, baxan iya xaman gidan nan ni d'aya ba tsoro nake ji "

Er dariya mumy tayi tare da Cewa ""shikenan 'yata ki kular min da kan ki sai mun dawo "

Tashi tayi ta sanya hijab d'in ta suka fito parlour inda daddy yake xaune,bayan mufidah ta gaida shi ne ya amsa cikin fara'a kamar ko yaushe tukunna suka fito xuwa farfajiyar gidan suka shiga mota driver xai kai su airport.

"ki kula da kan ki 'yata kin ji "
Fad'in mumy a karo na biyu, murmishi mufidah tayi tana jin dad'in yanda mumy take bata kula wa tace
"tohh mumy insha Allah, Allah ya kai ku lafia "

"Ameeen ya rabbi "

Mumy da daddy suka amsa, afnan sai d'ago wa mufidah hannu take alamar bye bye ita ma hannun ta d'aga mata har suka motar su ta fita daga gidan.

Bayan ta dawo cikin gidan ne ta shige bedroom had'a kayan ta tayi wad'anda xata yi amfani dasu, sai ta d'an kwanta don ta huta har kewar afnan da mumy sun fara Kama ta.

Bata ankara ba taji wani bacci mai dad'i yana fisgar ta bata yi wani 6ata lokaci ba ta gyara kwanciyar ta nan da nan bacci yayi awon gaba da ita.

Yini tayi tana baccin idan ta farka ma sai taji wata kasala kafin ta tashi wani baccin ya sake d'aukar ta da yake tana period kawai sai ta koma baccin, har xuwa wajen biyar na yamma dakyar ta iya tashi ta samu tayi wanka ta gyara jikin ta cikin wata arabian abayat ash colour tayi rolling kanta da black veil tayi kyau sosai different perfumes tayi amfani dashi daga body sprays har xuwa na kaya.

Sauri kawai take don ta tafi kada mangarib tayi mata, jakar da ta shirya kayan nata ta dauko tare da car keys sai phone nata, a parlour ta tsaya don jin k'amshin girki cikin mamaki ta nufi kitchen d'in.

Er dattijuwar da take taimaka wa mumy ta hango tana tsaye gaban gas cikin mamaki tace
"Inna wa kike yiwa girki? "
Da yake ko mumy da Inna take kiran ta dattijuwa ce mai kirki, jiyo wa tayi fuskar ta dauke da murmishi tace

"ah mufidah ina xuwa hka gab da mangarib ke da nake yiwa girki ganin yinin yau baki ci komai ba"

"tabbb ae ni Inna nan da kika ganni sai gidan mu kuma "

Rik'e ha6a tayi tare da cewa
"yanxu mufidah baxa ki xauna mu yi xaman mu ba kwana uku kawai xasu yi fah "

Murmishi mufidah tayi tare da cewa
"na kwana biyu ban je naga ummana da abbana kewar su nake gwara na tafi can "

"toh ae shikenan amman sai kin jira na gama miki girkin kici sai ki tafi "
Chapter 35 · 0% Book details