Sashe 27
Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan ya fito ne ya shirya jikin shi cikin wani lallausan yadi sky blue wanda yayi matuk'ar kar6ar shi yana cikin fesa perfumes ya hango wani pix d'in su da suka yi shi da sadeeq ta mirror suna dariya pic d'in yayi matuk'ar yin kyau sosai, hawaye ne ya cicciko a idanun shi bai bari sun xuba ba ya d'aure ya rik'e su hannun shi yasa ya shafa mirror d'in tare da cewa
"Yah sadeeq ka tafi ka bar ni, ina matuk'ar kewar ka "
Ya k'arasa fad'i muryar shi na rawa sosai kamar xai fashe da kuka, yana cikin hka mumy ta shigo bedroom d'in da sauri ya dai dai ta nutsuwar shi don yayi mata alkawarin daina sa damuwa a xuciyar shi.
Dad'i ne sosai ya kama mumy ganin d'an nata ya fito fes dashi ya dawo musaddiq d'in shi rungume shi tayi tana shafa kanshi tana cewa
"Naji dad'in ganin ka a hka musaddiq Allah yayi maka albarka ya jik'an sadeeq"
"Ameeen mumy na"
"Yanxu sauran ka breakfast kasha magani sai ka mu fita palour daddy yana jiran mu"
Cewar mumy kenan idon ta akan shi tana son ganin yanayin yanda ya kar6i maganar ta ta.
Murmishi ya d'an yi kafin yace " okay mumy"
Nan ta fara bashi abincin a baki har yaci ya K'oshi wanda rabon da yayi wannan cin abincin har ya mance bayan ya gama ci ta bashi maganin shi ya sha tukunna suka fito xuwa palon daddy.
Ba k'aramin dad'i daddy yayi ba ganin musaddiq a hka nan shima nasiha sosai yayi mishi nan suka xauna hira har xuwa lokacin tafiya masallaci yayi don yau juma'a tare suka tafi da daddy.
Mufidah ce na hango a bedroom tana k'okarin sanya hijab a jikin ta tana sanye da wata atampha tayi kyau kam don ma har yanxu bata ciko daga ramar da tayi ba, sauri take tana shirya wa don yau gida take son xuwa tuni ta gama shirya Afnan tana Palo hannun mumy.
Bayan ta fesa perfumes mara k'arfi a jikin ta ta fito xuwa falo, ko make up bata yi ba but duk da hka tayi kyau don kyanta natural ne.
A nutse ta fito tana tafiyar ta har xuwa Palo nan ta kar6i Afnan a hannun mumy suka yi mata sallama ta jiyo tana k'okarin bud'e kofar palon adai dai time d'in musaddiq ya sanya hannun shi kan handle d'in kofar ya bud'e gware suka yi da kan su saboda shi musaddiq ya d'an rakwafo kanshi gwaren nan irin na unexpected ne shi yasa suka ji xafin sosai har sai da mufidah ta d'an saki k'ara tana dafe goshin.
Wanda hkan yasa Afnan ku6uce wa daga hannun ta tayi k'asa sauran kad'an ta fad'i cikin xafin nama musaddiq ya taro ta da hannun shi lokaci d'aya Afnan ta tsandara ihu don ta tsorata sosai ta fara kuka, wani kallo musaddiq yayi wa mufidah wanda ya d'an tsorata ta tare da ja da baya don kada ya kawo mata bugu sai wani huci yake.
A tare mumy da daddy suka k'araso wajen suna tambayar su lafia, cikin fusata musaddiq yace
" mumy wajen sakacin ta ne yasa ta kusan fad'uwa"
" anya kuwa musaddiq sai dai tsautsayi?"
Mumy ta fad'i hkan tana kar6ar Afnan tana rarrashin ta har sai da tayi shiru.
"Ina xasu je ne?"
Cewar daddy, " gida mufidah xata je"
Mumy ta bashi amsa, kallon musaddiq yayi wanda yake k'okarin barin wajen yace
"Musaddiq ka kai ta gidan ni yanxu xan sake fita da driver "
Kafin yace komai daddy ya bar wajen, mumy ma mik'a wa mufidah Afnan tayi tare da cewa
"Sai kun dawo ki gaida min su xan shigo anjima da dare sai mu dawo tare"
Tana gama fad'in hka ta wuce ita ma, aka bar mufidah da musaddiq a tsaye, wanda shi tsabar mamakin abin da daddy ne yace ya hana shi kwakkwaran motsi, ita ma mufidan taji babu dad'i don sam bata so daddy yace ya kai su ba haushin musaddiq take ji sosai wai ya wani ce saboda sakaci na xan yarda Afnan kamar wata 'yar shi.
Kwafa tayi tare da jan d'an siririn tsaki, shima tsakin yaja har ya bud'e baki xai yi magana ko mai ya tuna sai yayi shiru tare da fita daga palon a fusace.............
Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/27, 11:24 AM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
*PAGE 35*
A fusace ya fita daga palon xuwa farfajiyar gidan motar da suka fita masallaci da daddy Ita ya shiga ya xauna yana jiran ta gaba d'aya ranshi yayi masifar 6aci akan abin da daddy yace yana nan xaune sai faman doka tsaki yake shi kad'ai.
Mufidah sai da ta kwashi tsawon mintuna tukunna ta fara k'okarin fito wa daga palon, kallon ta yake tana taho wa ranshi ya k'ara 6aci sosai ganin yanda ta shanya shi sai da tayi ra'ayi sannan ta fito kau da kanshi yayi daga barin kallon ta yana jan tsaki.
A nutse ta sanya hannun ta ta bud'e kofar motar ta xauna babu wanda yayi wa wani magana a tsakanin su yayi wa motar key ya fita daga gidan kowannen su fuskar shi a d'aure, har suka karasa gidan su mufidah a kofar gate d'in ya yi parking ba tare da ya kalle ta ba ko yayi magana.
Haushi ya sake turnik'e mufidah wato a waje ma xai ajiye ta baxai shigar da ita d'an tsaki taja tare da bud'e kofar motar ta fita sannan ta buga mishi murfin kofar da k'arfi har sai da musaddiq ya d'an tsorata ya kallo inda take amman wayam bai ganta ba har ta shige cikin gidan.
"Lallai yarinyar nan ashe har yanxu akwai raini atsakanin mu da ita ae kuwa xan koya mata hankali"
Ya fad'a yana jan tsaki can kuma har yayi wa motar key ya fara tafiya sai kawai ya furta a fili
"Xan kyale ta saboda darajar Yah sadeeq, but dole na kar6e Afnan daga hannun ta kada ta koya mata tsiwa da rashin kunya".
Mufidah kuwa cike da jin haushin musaddiq ta k'arasa cikin palour tare da kwalla wa umma kira tana cewa
"Umma na kina ina?"
Da sauri umma ta fito daga kitchen jin muryar mufidah ae kuwa tana ganin ta suka rungume junan su cikin tsananin farinciki sai mufidah taji duk 6acin ran ta ya kau sai farinciki.
Sakin ta umma tayi tana kar6ar Afnan tace
" Masha Allah Afnan sai girma take ga kamannin ta da mahaifin ta sak kamar yayi kaki ya xubar"
Tuni idanun mufida sun ciko da hawaye jin umma ta ta6o mata wani abun, ganin yanda lokaci d'aya mufidah ta canja yanayin ta cikin damuwa daga farincikin da take yasa umma ta rik'o ta suka xauna cikin sigar rarrashi da nasiha tace
"Haba mufidah bana son ganin ki cikin wannan yanayin ke har yanxu baki sa wa xuciyar ki hak'urin sadeeq ba ya kamata ki hak'ura kina mishi addu'a kin ji"
"Toh umma shikenan"
Ta fad'i hka muryar ta na rawa.
"Wane ya kawo ku kuma?"
Cewar umma don tana so ta bagarar da wancen xancen, d'an ta6e baki mufidan tayi tare da cewa
" Hmmm musaddiq ne daddy yace ya kawo mu"
"Okay, yasu hajia khadijahn?"
"Suna nan Qlau tace na gaida ke anjima xata shigo"
D'an shiru umma tayi ta fad'a tunani jin tayi shiru yasa mufidah d'ago kanta tace
"Umma lafia, me ya faru?"
" uhm mufidah wai so suke mu bar miki so ae sun xo da ita daddyn su sadeeq na nuna gaskiya ni ban amince ba tun da nima ba wasu 'ya'yan ne da ni ba da yawa nima ku biyu kad'ai Allah ya ba mu, yanxu kuwa da nayi tunani sai naga kema d'in ba wani dad'e wa xaki yi da wajen su ba aure xaki yi, kuma Omar da abban ku sun ce na hak'ura na bar ki saboda mutanen suna da karamci sosai"
Tun da umma ta fara magana mufidah take bin ta da kallo hankalin ta a tashe sam ita xama gidan su sadeeq bata so yanxun ma a dole take xaune saboda tana yawan tuna wa da sadeeq, kunyar mumyn ce ta hana ta dawowa gida, sannan ita ma sam bata da ra'ayin aure gaba d'aya a tsarin ta.
"Kin ga Omar ya fara yin gini acan 6angaren xasu dawo nan saboda kawai don na barki wajen su kuma yanxu na amince da hkan, ke dai ki cigaba da yi mishi biyayya ki d'auke su tamkar iyayen ki kuma ki cigaba da tsare mutuncin kan ki har xuwa lokacin da Allah xai fito miki da wani mijin na gari".
Gaba d'aya hirar ta gunduri mufidah jin yanda umma take mata xancen aure kawai sai ta silale ta gudu bedroom d'in ta, da kallo umma ta bita tun ba yanxu ba ta fuskan ci mufidah bata son ayi mata maganar aure sam, girgixa kai tayi tare da tashi ta goya Afnan a bayan ta don tayi bacci ta shige kitchen tana cigaba da ayyukan ta.
Sai yammaci bayan la'asar mufidah ta fito daga bedroom d'in xuwa Palo kallo d'aya umma tayi mata tasan tayi kuka, nan ta xauna tana cin abinci suna er hira da umma har daga k'arshe kuma suka shiga kitchen tare don shirya abincin dare.
Sai bayan wurin 8 na dare mumy taxo da sallama ta shigo palon umma da mufidah wadda take shayar da afnan suka amsa mata kafin su rufe bakin su muryar musaddiq ta doki kunnen mufidah yana sallama, fuskar nan tashi a d'aure da gani kasan dole aka yi mishi ya shigo.