← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 54

Sashe 15

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ya sauke ta daga kan kafafunshi tukunna ya mik'e tsaye yana rik'e da hannun ta suka rufe ko ina sannan suka shige bedroom, toilet suka shiga suka d'aura alwala tukunna suka fito ita dai mufidah bin shi take duk abin da yace mata saboda wata irin kunyar shi take ji, shi ya shimfid'a musu abin sallah ya d'auko mata hijab ta sanya sannan ya fara jansu yin nafila.

Bayan sun kammala nafilar ne ya rik'e kanta da hannun shi yayi addu'a sosai don ba laifi sadeeq akwai ilimin addini, bayan ya gama addu'ar ne sannan ya sauke hannun shi daga kanta,ya dad'e yana musu addu'ar xaman lafia da samun xuri'a mai albarka kafin kuma su shafa, tashi yayi ya fita daga bedroom d'in, ganin hka yasa mufidah mike wa ta ninnike abin sallahr ta ajiye tare da hijab d'in da tayi sallahr tukunna ta shige toilet don yin wanka saboda ta saba Indai xata yi bacci a gida sai tayi wanka take iya bacci mai dad'i.

Ta d'auki tsawon mintuna 15 tukunna ta fito ta shirya cikin wata sleeping dress irin mai biyun nan ta farko iyakar ta gwiwa ta tsaya tana da siririn hannu ta biyun kuma wadda ake d'ora ta asaman dogowa ce har k'asa hannun ta mai d'an tsayi kad'an sai ka d'aure ta da wasu siririn maxagin jikin rigar, bayan ta gama sanya kayan ne ta fesa different perfumes and body spray's masu matuk'ar k'amshin dad'i tukunna ta nufi kan bed don kwanciya wani irin bacci take ji a idanun ta sosai ta k'udundune jikin ta da wani blanket mai matuk'ar laushi saboda yanda garin ya d'auki sanyi sakamakon hadarin da ya had'u sosai ga kuma sanyin ac dana fanka.

Ko mintuna biyar bata yi da kwanciya ba sadeeq ya shigo cikin bedroom d'in hannun shi dauke da wani babban tire shima yayi wankan shi yasha wasu sleeping dress na maxa sky blue ne masu taushin gaske, ajiye tiren yayi tare da hawa kan bed d'in yasa hannu ya cire rufar da mufidah tayi lokaci d'aya tsikar jikin shi ta tashi saboda ganin mufidah da yayi a hka d'aure wa yayi yace

"My wife tashi kici abinci sai kiyi bacci, kada kice min a'a please, don nasan baki ci abincin kirki ba saboda hidima"

Kasa yi mishi musu tayi nan ta fara k'okarin tashi da sauri yasa hannun shi ya tashe ta xaune tukunna ta tashi xuwa wajen wasu kujeru guda biyu a gefen bed d'in akwai center table a tsakiyar su nan ta xauna shima sadeeq tashi yayi ya koma inda take tukunna ya bud'e plate d'in wasu gasassun kaji ne sun sha kayan vegetables sai tashin k'amshi suke ko ni dana ke gefe ina daukan muku rahoto sai da yawu na ya tsinke lol.

Gefe kuma drinks ne da fresh milk gasu nan kala kala masu sanyi, nan ya fara ciyar da mufidah da hannun shi don yak'i yarda taci da kanta, bayan sun gama ci ne mufidah ta tashi ta shiga toilet brush tayi ta wanke bakin ta da mouth freshener mai k'amshin mint leave's tukunna ta fito bata ga sadeeq anan ba don hka ta koma ta kwanta abin ta lokacin har an fara yayyafi.

Sadeeq ne ya shigo bedroom d'in tare da rufe kofar tukunna ya nufi kan bed ya kwanta kusa da mufidah, lokaci d'aya gaban mufidah yayi wani irin fad'uwa nan jikin ta ya fara rawa na tsoro, bugun xuciyar mufidah ne ya k'aru ganin sadeeq ya yi switch off d'in hasken d'akin nan duhu ya bayyana a d'akin sai dai hasken walk'iya da yake hasko ta tsakanin labulen window.

Ji tayi sadeeq ya sanya hannun shi ya jiyo da ita suna fuskantar junan su har suna jin d'umin numfashin junan shi cikin wata irin murya sadeeq yace

"Haba my wife ba dai bacci ba, ki bari abincin da kika ci yayi k'asa sai kin fi jin dad'in baccin"

Cikin marairaice wa mufidah tace"ni bacci nake ji gashi na gaji sosai"
"Okay bari nayi miki tausa"
Sadeeq ya fad'i hkan cikin murmishi yana sa hannun shi cikin jikin ta yana mata tausa a hankali, ita dai mufidah shiru tayi tana wani lumshe idanun ta don tana jin dad'in tausar.

Cikin mintuna biyar da fara yi mata tausar kid'a ya fara sauya salon shi, wanda adai dai time d'in ruwa mai k'arfi ya sakko tare da wata iriyar iska mai sanyi irin wadda take ratsa jiki har cikin k'ashi, nan fah jikin mufidah ya d'auki rawa don gaba d'aya sadeeq ya canja daga tausar da yake mata xuwa wani salo na daban wanda daga sadeeq d'in har mufidah sabon shiga ne a 6angaren.

Cikin nutsuwa yake sarrafa mufidah cikin wani irin salo mai wuyar fassara, gaba d'aya sadeeq ya rikici ya fara fita a hayyacin shi cikin rawar jiki yake juya mufidah yanda yake so, tuni mufidah ta fara kuka da had'a gumi har xuwa lokacin da mayar da ita cikakkiyar mace.

Adai dai wannan lokacin musaddiq da yake xaune saman sofa ya farka firgigit a matuk'ar firgice, ya mayar da kallon shi kan muh'd wanda yake kwance a kan bed ya tuk'unk'une jikin shi waje d'aya, tashi musaddiq yayi tare da d'auko blanket ya lullu6e muh'd, hka kawai yaji hankalin shi yayi matuk'ar tashi har wani gumi ne yake tsatstsafo mishi na tashin hankali.

Ya rasa abin da yake mishi dad'i kawai ya bud'e kofar da xata sada shi da corridor d'in waje yana bud'e kofar wani sanyi had'e da feshin ruwa ya bugi fuskar shi da gangar jikin shi amman bai damu ba sai kawai ya fitar da kanshi daga wajen rumfar corridor d'in nan take ruwan sama ya fara dukan shi kafin kace me tuni ruwan ya jik'a shi jagab.

Bai damu da jik'ewar da yayi ba ko dukan da ruwan saman yake mishi ya tsaya kawai waje d'aya ruwan na dukan shi xuciyar shi na wani irin xugi.

Gaba d'aya hankalin shi da xuciyar shi suna wani waje daban, yafi tsawon mintuna 30 a tsaye a wajen kafin kuma ya koma cikin bedroom dak'yar ya iya cire jik'akk'akun kayan jikin shi ya sanya wani wando dogo Mara nauyi da wata jibgegiyar rigan sanyi ya k'udundune da bargo wani sanyi ne yake ratsa shi tuni wani xaxxafan xaxxa6i ya lullu6e shi jikin shi sai rawa yake wasu hawaye masu xafin gaske suna xubo mishi.....................

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*

*PAGE 20*

Kiran sallahr asuba ne ya farkar da sadeeq daga bacci mai dad'in da ya d'auke shi kallon mufidah yayi wadda take kwance a jikin shi ta tuk'unk'une jikin ta waje d'aya sai faman sauke ajiyar xuciya take alamun taci kuka ta koshi, hannun shi yasa ya shafa mata fuska tare da gyara gashin da ya barbaxu akan kyakkyawar fuskar ta murmishi ne kawai yake fita daga idanun shi na nishad'i.

Anutse ya gyara mata kwanciyar tukunna ya tashi ya shiga toilet yayi wanka tare da d'aura alwala kafin ya fito sai da ya had'a wa mufidah ruwan d'umi a cikin kwamin wanka tukunna ya fito daga toilet d'in.

Cikin bedroom d'in ya dawo tukunna yasa hannu ya cire blanket d'in da mufidah take lullu6e a ciki ya d'auke ta cak xuwa cikin toilet cikin ruwan da ya had'a mata ya sanya ta ciki, haba wani xabura mufidah tayi xata tashi da sauri sadeeq ya rik'e ta tare da cewa

"Sorry my wife ki daure ki xauna hkan xai taimaka miki sosai kiji dad'in jikin ki"

Cikin xubar hawaye mufidah tace" ni ka fitar da ni daga nan sadeeq please akwai xafi"
Cikin marairaice wa da muryar rarrashi yace"haba my wife ke fah jaruma ce kiyi hak'uri d'an lokaci komai xai dawo normal, Allah yayi miki albarka matata"

A cikin xuciyar ta ta amsa da ameeen d'in, hka ya cigaba da lalla6a ta har ta gasa jikin ta tukunna ta fito ya tafi masjid xuciyar shi wasai farinciki ne fal a tattare dashi don mutum kallo d'aya xai mishi ya karanci hkan a tare dashi.

Bayan tayi wanka had'e da d'aura alwala tana fitowa ta shirya cikin wata gown mara nauyi tukunna ta shimfid'a abin sallah ta fara, bayan ta idar da sallahr tana cikin addu'a ne wani bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita.

A hka sadeeq ya dawo daga masallaci ya ganta kwance kan abin sallahr, daukan ta yayi tare da d'ora ta kan bed tukunna shima ya kwanta tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta kafin bacci kuma yayi awon gaba dashi.

Addu'ar tashi daga bacci muh'd ya furta bayan ya bud'e idanun shi tare da yin mik'a, agogo ya kalla yaga har 6:40 na safe yayi lallai yau ya makara sosai bai yi sallahr asuba akan lokaci ba, mik'e wa yayi tare da shiga toilet ya d'aura alwala sannan ya fito, bayan ya idar da sallah ne yayi addu'o'in shi tukunna ya tashi ya nufi bed da niyyar tashin musaddiq yaye blanket d'in yayi tare da cewa

"Musaddiq tashi kayi sallah yau mun makara sosai"
Shiru yaji musaddiq bai amsa ba kallon shi yayi sosai sai lokacin ya kula da yanda jikin shi yake rawa hawaye na fita a idanun shi, fuskar shi da idon shi sun yi ja sosai cikin tashin hankali muh'd yace

"Subhanallah musaddiq me yake damun ka?"
Ya k'arasa fad'i yana tashin shi xaune cikin rawar murya yace
"Muh'd mutuwa xan yi xuciya ta kamar xata fashe nake jin ta kuma sanyi nake ji sosai"

Ya k'arasa fad'i hawaye masu xafi suna xubo mishi, shima muh'd d'in hawayen yake yi ganin yanda musaddiq ya koma cikin sanyin murya yace
"Baxa ka mutu ba musaddiq xamu rayu tare insha Allah cuta ba mutuwa bace Allah ne ya d'ora maka kuma insha Allah xai yaye maka, bari na duba ka"
Chapter 15 · 0% Book details