← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 54

Sashe 44

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gashi bata san musaddiq yana parlourn ba yana aiki kallon ta sai lashe lip's yake yana Kallon cute lip's d'in ta yana motsi yayin shan ice cream d'in da take, yana ayyana wasu abubuwa cikin xuciyar shi.

Ta d'ebo ice cream d'in xata sanya a baki idon ta akan tv unexpected ta ga an nuno wasu horror bakyan gani bakin su kaca kaca da blood, wani tashi mufidah tayi wanda sai da komai na jikin ta yayi motsi tare da sakin k'ara tana runtse idon ta don sam jinin ta bai had'u da kallon irin moves d'in nan ba.

Jikin ta sai 6ari yake tsabar tsoro da raxana tana cikin lalu6en hanyar guduwa bedroom ta rufe kofa sai taji tayi tuntu6e tare da hantsila wa kan kujerar da musaddiq yake kai ta fad'a kanshi.

Nan ta sake rud'e wa da gigice wa don bata gane ko waye ba jin da tayi an rik'e ta k'am yasa ta dad'a kwalla k'ara a karo na uku ta bud'e baki sosai da k'arfi tana cewa

"wayyo Allah na musaddiq kaxo ka taimaka min wani horror ya rik'e ni xai shanye min Jini"
Iyakar k'arfin ta take kwad'a mishi Kira da neman taimakon shi, sai kokawar kwatar kanta take amman ta kasa tuni ta fara jan wani irin numfashi alamun daf take da sume...........

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive writers forum*

Likes nd comment's fb page 👇🏻

#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

_ina kuke kawayen arxiki da karamci wannan shafin na ku ne kyauta ina alfahari da ku, zeee yabour marubuciyar (itace kaddara ta), sajida niger marubuciyar (duk karyar kada ta ruwa ce), khadija neenah tawa marubuciyar (Deejah) salma Ali wada marubuciyar (namijin gaske), my biebie dear marubuciyar (d'an hakin da ka raina), and Queen Ayush marubuciyar (ya sayyadi), ni Aishat A Muh'd ina muku fatan alkhairi Allah ya bar xumunci ina yin ku guy's_ 👄

*PAGE 51*

Ganin tana neman sume mishi a wurin ya sanya shi gimtse dariyar muguntar da yake yi mata tare da sanya hannun shi yayi hugging d'in ta very tight kafin kuma yayi amfani da d'ayan hannun shi yana bubbuga mata bayanta cikin kunnen ta yake furta
"shhhhhhh mufidah calm down kina tare da ni babu abin da xai same ki relax "
Jin muryar musaddiq ne yasa shi saukar mata da wata nutsuwa ta daban sai ta fara sauke ajiyar xuciya har yanxu dai jikin ta 6ari yake na tsoro gashi kirjin ta sai bugawa yake da k'arfi ta bi ta wani k'ank'ame shi sosai idon ta a runtse suke don tana tunanin idan ta bud'e su xata iya ganin horror d'in da ta gani.

A hankali yake bubbuga bayanta tare da hura mata iskar bakin shi cikin kunnen ta hkan ba k'aramin saukar mata da kasala yayi ba, babu dad'e wa bacci yayi awon gaba da ita a hkan gashi kuma duk tabi ta k'ank'ame shi sosai da dubara ya tashi tare da kashe tv d'in ya dauke cak bedroom d'in ta ya kaita ya kwantar da ita kan bed.

Tashi yayi niyyar yi amman yaji ta dad'a k'ank'ame shi kamar wadda idon ta biyu sai ya koma ya xauna tare da kafe da ido yana wani murmishi shi kad'ai yasan ma'anar murmishin nashi, ya dad'e xaune a hkan yana tunani na daban a karo na biyu ya sake kok'arin tashi but har yanxu tak'i sakin shi dakyar da dabara ya kwace jikin shi yayi mata addu'a tare da lullu6e ta da blanket sannan ya tafi bedroom d'in shi .

Yana tsaka da yin wanka yaji kamar ihun mufidah cikin sauri ya d'aura towel ko damuwa da wanke kumfar jikin shi bai yi ba ya fito da gudu yana kok'arin bud'e kofa ne ita kuma ta turo kofar sai k'um suka yi gware but mufidah bata damu da jin xafin da taji ba na bugewar ta fad'a jikin shi cikin shashshak'ar kuka tace
"ni gaskia ka mayar da ni wurin mumy tsoro na ke ji "
Musaddiq wanda yake dafe da goshin shi cikin damuwa yace
"me yafaru kuma yanxu?"
"ni ji nake kamar suna bina Allah tsoro nake ji "
Raba ta da jikin shi yake kok'arin yi saboda ya fara shiga wani hali amman ina mufidah sai dad'a rik'e shi take tana kuka
"okay okay ya isa hkan "

Shiru tayi tana faman sauke ajiyar xuciya suna tsaye a hka wajen 5 minutes kafin ya fara kok'arin raba ta da jikin shi nan tak'i yarda, ya rasa yanda xai yi da ita gaba d'aya ta d'aga mishi hankali wata muguwar kasala ce ta baibaye shi har takai da ya fara jin nauyin jikin shi yana kok'arin xubar dasu a k'asa.

Namijin kok'ari yayi wajen daurewa xuwa jan su saman bed ya kwanta yayin da mufidah ma ya kwantar da ita gefe amman sai da ta dad'a rik'e shi sosai, girgixa kai musaddiq yayi lokaci d'aya tunanin shi ya fara sauya salo xuwa wani abin daban.

Kasa daure wa yayi ya lalu6o lips d'in mufidah ya fara kissing d'in su cikin wani yanayi na daban jikin shi har 6ari yake tsabar birkita mishi lissafi da mufidah tayi.

Tuni mufidah ta wartsake daga baccin da ta fara yi saboda abin da taji musaddiq yana yi mata kasa kwace kanta tayi saboda rik'on da yayi mata irin na sadaukan maxa ne.

Kukan da ta daina shi ya dawo mata ta fara kokawa saboda jin wannan bak'on al'amarin da yake kok'arin shiga tsakanin ta da musaddiq, sai da yayi romance da ita son ranshi, mufidah ido ya raina fata tun da duk kukan da take da kok'arin kwatar kanta da take ta kasa sai kawai tayi luf da ita ta mik'a wuya tun da duk ragowar k'arfin da yake jikin ta, ta rasa shi ganin hka da musaddiq yayi yasa shi cigaba da abin da yake yi.

Yana daf da cimma burin shi ne mufidah taji ya tsaya cak kafin taga kuma ya tashi tare da shigewa bathroom tana jin k'arar yanda ya saki shower ruwa yana xuba a kanshi, da sauri ta mik'e ta gudu bedroom d'in ta sai da ta sanya key a kofar tukunna hankalin ta ya kwanta duk tsoron da take ji ya kau abin da ya koro 6era daga rami ya fad'a wuta yafi wutar xafi, kafin ta kwanta ta lullu6a da blanket har xuwa yanxu gaban ta fad'uwa yake jikin ta ma rawa yake, tana tunanin yau mai juyar da hankalin musaddiq har yayi kok'arin yin wani abin da ita.

Tun da ta ta6a jin hirar shi a waya da muh'd har yake fad'a mishi shi ya rasa yanda xai yi da yanayin shi gashi baxai iya tunkarar mufidah da buk'atar shi ba ya bashi shawara yanda xai yi bata ji abin da muh'd ya ke fad'a mishi ba but taji musaddiq yana cewa wannan ba shawara bace baxan iya ba idan na gaji sai na sake aure amman dai so shi d'aya nake yiwa sweet baby nah, daga hka hirar tasu ta xo k'arshe sosai mufidah a lokacin ta fad'a duniyar tunanin wace ce sweet babyn musaddiq, tun kafin ta ganta ta fara kishi da ita.

Tun da ita tasan auren had'i aka yi musu da musaddiq ba ganin juna suka yi ba suna so, a yanxu bata da tabbacin ko yana sonta, ita dai tasan ta fara son musaddiq a tun kafin ta auri sadeeq.

Shigowar sadeeq cikin rayuwar ta shi ya hana son yin tasiri cikin xuciyar ta tun da ta riga da tasa a ranta sadeeq xata aura, amman xuwa yanxu ita kanta har tsoro take ji ganin yanda xuciyar ta take son musaddiq abin har mamaki ya ke bata, ita yanxu mene ne mafita.

Da wannan tunanin bacci mai k'arfi yayi awon gaba da ita bata kai da ta nemo mafitar ba.

Musaddiq kuwa tun da ya kunna wa kanshi shower ruwa yana xuba a jikin shi idanun shi a rufe suke ruf kan shi yayi xafi brain nashi tana tunano mishi da irin yanayin da shiga a en mintuna da suka wuce.

Tunanin mafita shima yake ya gaji da wannan abin yana son kawo k'arshen irin wannan xaman a tsakanin shi da mufidah, ya d'auki tsayin mintuna 20 a hkan kafin ya samu kwarin jikin shi ya kashe shower d'in tare da d'aura towel ya fito.

Ajiyar xuciya ya saki ganin mufidah bata d'akin kafin kuma ya saki wani murmishi yace
"ashe ma tsoron bai kai xuci ba sai da ta gama hargitsa min tunani ta gudu idan na kama ki sweet babynah xaki yaba wa aya xak'in ta "

Yana gama fad'in hka ya sake sakin murmishi yana tunanin yanda xai yi wajen fara janyo mufidah a jikin shi ta saba dashi yana son ta dawo bedroom nashi suna kwana tare ko da wani abin baxai had'a su ba shi dai yana ganin ta kusa dashi hankalin shi sai yafi kwanciya da hka shima bacci ya dauke shi mai dad'i cike da mafarkan mufidah...........

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive writers forum*

*Likes nd comment's fb page*👇🏻

#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/

_ina masoyan my sister *sumayya salees sadeeq*,ina masoyan karanta littattafan ta irin su *rayuwar ashwema,dangartakar xuci, yareema jawad*kun ji ta shiru na kwana biyu hutu ta tafi amman yanxu ta xo muku da sabon wani daddad'an labari mai suna *DARIYA BA SO BA*my sister sumy muna biye da ke har xuwa lokacin da xaki kammala shi, maxa ku garxaya ku nemi shi don kada a bar ku a baya, ni Aishat A Muh'd ina miki fatan alkhairi tare da addu'ar Allah ya k'ara basirah da xumunci a tsakanin mu_ #ana tare

*PAGE 52*

Washe gari da safe tun da mufidah ta shirya afnan xuwa skul ta had'a mata komai ta dawo bedroom ta kwanta duk jikin ta ba k'arfi tana nan kwance taji an turo kofar tare da jin muryar musaddiq yana tambayar afnan
"ina mameen ki afnan? "
"daddy tana bedroom a kwance "
Chapter 44 · 0% Book details