← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 54

Sashe 22

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaba d'aya ta rud'e tama rasa me xata ce mishi, shi kuwa kallon ta yake wasu hawayen tausayin mufidah ne yake xubo mishi, jikin ta na rawa ta d'auki waya har wayar tana sullu6e wa daga hannun ta saboda yanda jikin ta yake rawa.

Dr muh'd ta kirawo cikin rawar murya take maganar tana cewa " mu....muh'd ya.....ya farka sa....sadeeq yanxu"

Bai ce komai ba ya kashe wayar tare da fitowa daga office d'in da gudu ya nufi room d'in da yake yana cikin hospital d'in.

Da sauri ya tura kofar room d'in nan ya k'araso kusa da gadon da sadeeq yake kwance

" Alhmdullilah babban yaya sannu"
Cewar sadeeq kenan nan ya cire mishi drip da oxygen tube d'in tare da k'ara duba shi, tukunna ya jiyo ya kalli mufidah yace
" yanxu ki taimaka mishi yayi wanka ya d'an ci wani abin"
Gid'a kai mufidah tayi tare da taimaka wa sadeeq ya tashi xaune, shi kuwa muh'd fita yayi daga room d'in, sai da ta shiga toilet ta had'a mishi ruwa tukunna ta fito ta rik'e shi suka shiga toilet d'in, wanka yayi tare da yin brush da alwala suka fito daga toilet d'in.

Nan ta shirya shi cikin kaya marasa nauyi sannan a nutse ya tashi ya fara rama sallolin da ake bin shi, bayan ya idar ne ya xauna kan abin sallahr ya jingina bayan shi da gadon idanun shi a lumshe, tea mufidah ta had'a mishi cikin cup ta bashi dak'yar yasha rabin cup d'in yace mata ya K'oshi nan ta fara lalla6a shi da yasha amman k'arshe sai ya janyo ta jikin shi yana bata ragowar tea d'in yana cewa

" kema naga alama bakya son bawa baby na abinci xamu 6ata fah nayi miki hukunci da k'in yi miki magana na tsawon second 3"

Dariya ya bata saboda yanda yayi maganar amman sai ta murmursa kawai, shima murmishin yayi daman abin da yake son gani kenan akan fuskar ta.

" ayi min afuwa idan kayi min wannan hukuncin ae kuka xan tayi maka har sai ka hak'ura ka janye"
Hannun shi yasa yaja tsinin hancin ta tare da cewa " na fad'a ne kawai my wife baxan iya fushi dake ba ina son ki da yawa amman nasan xan tafi na barki"

Hannun ta ya kamo tare da cigaba da cewa " ki yafe min mufidah idan na 6ata miki rai a xaman mu kuma ga amanar baby na nan ki kula dashi ina son ki bashi irin tarbiyyar da su umma suka baki nasan baxan yi nadamar kasancewar shi a hannun ki ba, mace ko namiji duk wanda Allah ya bamu don ina godia ga Allah da ya bani ke matsayin mata ta, mufidah ina son kiyi min alkawari idan na mutu xaki au........"

Bai kai ga k'arasa fad'in abin da yake so ya fad'a ba mufidah tasa hannun ta ta toshe mishi bakin shi tana kuka sosai cikin muryar kuka tana cewa
"Bana son wad'annan maganganun sadeeq suna d'aga min hankali, ae cuta ba mutuwa bace ni nasan xaka samu sauk'i insha Allah mu rayu tare da ke"

Kukan da take yi ne ya tashin hankalin sadeeq sosai tuni ya fara rarrashin ta har ya samu tayi shiru dak'yar, hannun shi yasa saman cikin ta yana ta6awa yana mai addu'a Allah ya sa kafin ya mutu yaga babyn shi.

Xuba mishi ido mufidah tayi tana kallon shi ko kiftawa bata yi shima hka ya xuba mata nashi idanun suna kallon junan su sosai a cikin sanyin murya mufidah ta bud'e bakin ta tace

" I luv u sadeeq with all my heart hak'ik'a halayen ka suna birge ni Allah yasa d'an da xamu haifa ya debo halin ka"
Murmursa wa yayi tare da cewa " luv u too my wife, nasan ma insha Allah d'an da xamu haifa mai nutsuwa ne ina son ki mata ta"

Rungume junan su suka yi irin sosai d'in nan kamar wanda xa'a raba su da junan su, sadeeq yana son k'arasa mata maganar shi ta d'axu but yana jin tsoron kada tayi mishi kuka don sam baya k'aunar ganin kukan mufidah.........

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 12:28 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

_Naga comment's d'in ku fan's kowanne da irin ra'ayin shi da ya bayar kuma naji dad'in hkan sosai Allah ya bani ikon kammala muku shi lafia_ #ana tare❤

*PAGE 29*

Suna cikin hka har gari ya k'arasa waye wa, wajen 7 na safe mumy da daddy suka shigo hospital d'in nan dak'yar suka lalla6a shi ya sake cin wani abin, tukunna suka fito daga d'akin Dr muh'd da sauran doctor's biyu suna tare dashi suka shiga room d'in da sadeeq yake, bayan en mintuna kuma suka shige dashi wani room na daban, koma wa room d'in da aka kwantar da sadeeq suka yi dukkanin su xuciyoyin su d'auke da damuwa.

Daddy ne ya fara magana da cewa " bana son musaddiq yasan da labarin rashin lafiyar sadeeq shi yasa sam ban fad'a wa en uwana ba saboda bana son xancen yaji kunnen shi"

Cikin muryar kuka mumy tace " ya Allah na rok'e ka kasa ba wanda xai fad'a wa musaddiq halin da d'an uwan shi yake ciki ba don nasan idan yaji shikenan xan rasa su gaba d'aya, ya Allah na rok'e ka ka bawa yara na lafia kada ka d'auke min su gaba d'aya"

Da sauri daddy ya matso kusa da ita tare da rufe mata baki yana cewa " haba mumy kada kiyi sa6o mana ki kasance mai tawwakkali mana, Allahn da ya d'ora musu larurar yana sane dasu ya jarabce su da hkan don gwada imanin su da namu don hka ina son kiyi hak'uri, kuma insha Allah xan toshe duk wata hanya da xai sa musaddiq yaji labari, ki dunga hak'uri kina tausar mufidah kalli ki ga halin da take ciki yanxu ga tsohon ciki"

Sai lokacin ta tuna da mufidah a d'akin kallon inda take tayi, ganin ta tayi tana shar6ar kuka sosai tana dafe da cikin ta wani irin tsoro ya d'arsu a xuciyar mumy kada kuma ta janyo su yi asarar cikin da yake jikin ta da sauri ta tashi ta nufi inda take suka hau rarrashin ta ita da daddy har tayi shiru amman xuciyar ta fal tashin hankali.

Suna xaune a hka har aka shigo da sadeeq cikin room d'in aka kwantar dashi kafin sauran doctor's d'in su tafi muh'd kuma ya tsaya yana son yiwa su daddy bayanin abin da ake ciki amman yana fargabar halin da mufidah da mumy xasu shigo dole yaja hannun daddy suka fita daga room din xuwa office d'in shi.

Sun kai wajen mintuna talatin acikin office d'in kafin daddy ya fito kallo d'aya xaka yiwa daddy kasan ba k'aramin tashin hankali yake ciki ba idanun shi sun yi ja, hka Dr muh'd da yake bin shi a baya nashi idanun sun yi ja sosai lokaci xuwa lokaci yana goge hawayen fuskar shi, koda suka koma room d'in da aka kwantar da sadeeq basu cewa mumy komai ba.

*AFTER ONE WEEK*

A ciki wannan satin al'amara sun k'ara tsanani don sadeeq ba lafia sosai yau lafia gobe ko anjima ciwo ya tashi duk yabi yayi mugun rame wa, hka ma mufidah sai katon cikin da yake rinjayar don a yanxu ta shiga 9 month's kuma tak'i yarda ta bi su mumy gida daddy ya xauna da sadeeq kullum tana kusa dashi bata son tayi nisa dashi ko na second d'aya, idan ka kalli mufidah sai ka mugun tausaya mata.

Duk wata hanya da musaddiq xai samu labarin rashin lafiyar sadeeq daddy ya toshe a yanxu ma daddy shirye shiryen fitar da sadeeq India yake duk wasu shiri ya gama xuwa gobe da dare jirgin su xai tashi xuwa indian, koda kud'in shi xai k'are xai nema wa sadeeq lafia.

Mufidah ce a xaune kan kujera hannun ta d'auke da Qur'an tana karanta wa sadeeq suratul alrahman cikin muryar ta mai dad'in karatu duk kuwa da yanda muryar ta dashe, idan ta kai k'arshen surar sai yace ta dawo hannun ta d'aya yana rik'e da hannun shi.

Idanun shi a lumshe suke yana sauraren ta, kad'an kad'an take jin mararar ta tana murd'a wa sai ta d'aure bata kawo komai a ran ta ba don tun da cikin ta ya girma take fama da hkan.

Can kamar mintuna goma sai taji ciwon ya k'aru don bayan ta da marar ta suka rik'e lokaci d'aya suna yi mata wani axababben ciwo tuni ta fara had'a uban gumi duk da kuwa sanyin ac d'in da yake room d'in, duk dauriyar da take yi batasan lokacin da ta bar karatun ba ta furta "Wash Allah na"
Tana dafe da kugun ta wanda take jin shi kamar ya 6alle ya rabu da gangar jikin ta, da sauri sadeeq ya bud'e idanun shi ganin yanda mufida take had'a gumi fuskar nan ta ta tayi ja sosai tuni ya mik'e da sauri tare da rik'o ta yana cewa
"Mufidah lafia kuwa mene yake damun ki?"
Duk a rud'e ya tambaye ta hannun shu ta damk'a ta rik'e gam cikin axabar ciwo tace

"Sadeeq ka yafe min mutuwa xan yi ka fad'a wa su umma, Abba, daddy da mumy su yafe min don Allah"
Gaba d'aya ta kid'ima sadeeq sosai lokaci d'aya kan shi yayi wata irin sarawa amman duk da hka cikin dauriya yace

"No mufida bata ki mutu ba nine xan mutu ki tashi please, ina ne yake miki ciwo?"
Ina babu bakin magana shi kuwa ya kasa tafiya ya kirawo muh'd gashi ba kowa a wajen, suna cikin hka Dr muh'd ya shigo kallo d'aya yayi wa mufidah yasan labour take don hka yace
" babban yaya haihuwa xata yi ae"
Yana gama fad'in hka ya fita ya kirawo wasu nurses biyu suka taho akan gadon tura mara lafia suka d'ora ta sadeeq hannun shi yana rik'e da hannun mufidah yana xuba mata sannu duk yabi ya rud'e ya gigice sosai da hka har suka shiga da ita labour room.
Chapter 22 · 0% Book details