← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 54

Sashe 23

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har xai bisu ciki Dr muh'd ya rik'o shi tare da cewa " kayi hak'uri babban yaya xata haihu lafia insha Allah"

Rik'o shi yayi suka fara tafia sai ga Doctor Aishat nan xata shiga labour room d'in hannun ta dauke da hand gloves.
" yawwa Dr Aishat don Allah ki kula da ita sosai"
Murmishi tayi wanda ya k'ara mata kyau tace " Doctor kada ka damu xata haihu lafia insha Allah"

"thanks Dr Aishat"
Fadin muh'd " ka wuce hkan Dr" ta fad'a tana shige wa room din da mufida take.

Suna nan tsaye a wurin muh'd yayi yayi da sadeeq yaje ya kwanta amman yak'i, suna cikin hka su mumy, daddy, Abba, umma, nabila da Yah Omar suka shigo asibitin a tare kamar had'in baki, mumy ce ta fara cewa
"Lafia muh'd na gan ku anan?"
"Uhm mumy mufidah ce xata haihu"
Nan fah kowa yaja ya tsaya suna faman yi mata addu'ar samun lafia, gaba d'ayan su hankalin su a matuk'ar tashe.

Sun d'auki tsawon mintuna hamsin a wurin sadeeq yana tsaye har lokacin jiri ya fara ji yana daukan shi wurin yana juya mishi kafin kuma a hankali ya fara yin baya xai fad'i, duk basu ankara dashi ba sai Yah Omar da sauri ya nufi wajen shi yana k'arasa wa kuwa ya fad'o jikin shi.

Sai lokacin hankalin su mumy ya dawo wajen a matuk'ar rud'e suka yo inda yake gaba d'ayan su, muh'd kuwa doctor's d'in nan da suke duba sadeeq ya kirawo aka d'auke shi suka shiga dashi cikin room.

Wayyo Allah abin tausayi wad'annan familyn idan ka gansu a lokacin xaka yi matuk'ar tausaya musu saboda halin dasu ke ciki babu mai nutsuwa a cikin su gaba d'ayan su babu mai kwanciyar hankali, Matan kuwa irin su mumy, umma da nabila kuka suke yi sosai maxan ma basu da kwanciyar hankalin rarrashin su.

********

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" ya fad'a bayan yayi xumbur ya tashi daga mummunan mafarkin da yayi, xama yayi akan gadon tare da kunna hasken d'akin duk da sanyin ac da fankar d'akin amman gumi yake had'a wa, kallo d'aya xaka yi mishi kasan hankalin shi a tashe yake.

Musaddiq kenan yau wajen kimanin wajen sati d'aya kenan yana wani irin mugun mafarki akan sadeeq da mufidah amman na yau yasha bambamci dana ko yaushe.

Idan yayi wannan mafarkin sai ya kirawo kowa ya ji muryar shi hankalin shi yake kwanciya amman ban da mufidah, duk da sadeeq yana gadon asibiti lokacin yana daurewa ya amsa mishi wayar kamar yanda yake amsa mishi da, but yanxu hankalin shi yayi gida kawai baxai iya jure wa ba yakai k'wana biyu bai ganshi a nigeria ba gaban d'an uwan shi da iyayen shi.

Wayar shi ya d'auko ya kira wata number tsayin mintuna goma ya d'auka yana waya da harshen turanci kafin kuma ya ajiye wayar, tashi yayi ya nufi wardrobe ya bud'e ya fara shirya kayan shi cikin trolley sai da ya had'a duk wani abin amfani tukunna ya rufe.

Toilet ya shiga yayi alwala ya fito ya fara nafila yana addu'ar Allah yasa mafarkan da yake kada su xama gaskia, sai da yayi sallahr asuba tukunna ya tashi yayi wanka ya shirya cikin wani black jeans da t-shirt black mai dogon hannu hatta belt da takalmi bak'ak'e ne, bayan ya fesa perfumes ne ya janyo trolley dinshi tare da jakar da take rataye a kafad'ar shi ta laptop da sauran muhimman abubuwan shi, fito wa yayi driver d'in shi ya kai shi airport.

Ko mintuna 30 bai yi da xuwa ba jirgin su ya tashi xuwa nigeria, gaba d'aya a matuk'ar kaguwa yake ya ganshi cikin iyayen shi da d'an uwan shi.

Lokacin da jirgin su yayi landing ya fito ya shak'i iskar k'asar sai yaji ya d'an samu nutsuwa don yana tunanin nan da en mintuna xai ganshi a gida, bai kirawo su ba a waya ya fad'a musu don surprise yake son yayi musu taxi ya d'auka har xuwa gida bayan ya sauka yana k'okarin biyan mai taxi d'in kud'in shi sai ga mai gadi nan ya fito cikin mamaki yake kallon musaddiq kafin kuma cikin girmama wa ya gaida shi, maigdin ne yace

"Yalla6ai as gaba d'aya en gidan basa nan suna asibiti"

A firgice musaddiq ya kalli maigadin yace " lafia, wane bashi da lafia?"
Sai lokacin maigadin yayi da nasanin fad'a wa musaddiq don daddy ya gargad'e su da hkan, cikin ina ina yace

"Bansan wanda bashi da lafiyar ba yalla6ai sai dai kaje suna can asibitin da alhj ya Gina maka"

Kafin ya k'arasa fad'i musaddiq yace "d'auki trolley d'in nan ka shigar min dashi gida"

Cikin rawar jiki maigadin ya d'auki trolley ya shige, shi kuma musaddiq ya shiga taxi d'in ya fad'a mishi inda xai kai shi............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: [9/19, 3:54 PM] Aishat A Muh'd ✍🏻: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ E.W.F

_lokacin da Allah ya sakkowa da bawan shi wata jarabta ya kasance cikin furta innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yayi ta maimaita har sai ya samu nutsuwa, ita rayuwa da muke ganin ta kowanne mutum da irin tashi kaddarar don hka mu kasance cikin takatsantsan da rayuwa da bautawa Allah tare da kiyaye dokokin shi don idan mutuwa ta tashi xuwa daukan mutum ba shawara ake dashi ba, don kowanne ita yake jira tun da Allah swt yana cewa cikin suratul imran (kullu nafsin xa'iqatul ma'ut) kowanne mai rai xai d'and'ani d'acin mutuwa, don hka ina kira a gare ku da mu kyautata mu'amalar da mutane domin ka samu shaida mai kyau a bakunan mutane, sannan mu dage da aikata alkhairi da karatun al'Qur'an, addu'o'i, nafilfilo, istigfari, salatin annabi da sauran su, a dunga kyautata iyaye ana musu biyayya, idan kina da aure ana yiwa miji biyayya, ana yawaita yin xumunci da axumin nafila da sadaka, Allah yasa mu dace duniya da lahira, Ameeen thumma Ameeen_.

*PAGE 30*

Ba k'aramin wahala mufidah tasha ba kafin Allah ya taimake ta ta haihu bayan sun gyara babyn Dr Aishat sai da tayi wa mufidah d'inki don ba k'aramin k'aruwa tayi ba don tubarkallah babyn k'atuwa da ita sai da ta duba ta ita da babyn ta tabbatar suna cikin koshin lafia tukunna suka fito a tare da sanar dasu mumy an sauka lafia an samu baby girl, sosai sun yi murna nan suka kar6i babyn har suka shiga room d'in mufidah da take kwance tana huta wa suna mata sannu, duk bata amsa ba sai ma bud'ar bakin ta tace
"Mumy ina sadeeq?"
Shiru mumy tayi ta kasa magana ganin hka yasa mufidah yunk'ura ta tashi xaune dak'yar saboda d'inkin da aka yi mata cikin tashin hankali ta kuma cewa

"Ina sadeeq ne ina tambayar ku kun yi shiru?"

Abba ne yayi k'arfin cewa "ki kwantar da hankalin ki mufidah ciwon shi ne ya tashi likitoci suna kan shi suna duba shi"

Hawaye ne masu xafin gaske suka xubo daga idanun ta komawa tayi ta xauna tana kuka k'asa k'asa acikin xuciyar ta kuma addu'ar samun sauk'i take yi wa sadeeq, duk d'akin anyi shiru kamar ba mutane babu wanda yayi iya yunkurin rarrashin mufidah sai nabila.

A can kuma room din da sadeeq yake likitoci sun dukufa akan shi wajen ceto rayuwar shi, ana cikin hka nau'orar da take nuna yanda numfashin mutum yake tafiya tare da bugawar xuciya ta fara yin k'asa, a firgice muh'd ya kalli yanayin numfashin shi ya ga yana sauka har xuwa 50 tuni muh'd ya rud'e cikin rawar murya yake cewa

"Babban yaya kalle ni kada ka mutu please gashi mufidah ta haifa maka baby girl"
Kallon shi sadeeq ya tsaya yi kafin kuma yana jan wani numfashi dak'yar yace
"Muh'd taimaka ka d'auko min babyn na gani don Allah"

Cikin rawar murya yake cewa "to...to ina xuwa kada ka tafi ka barmu" murmishi sadeeq yayi mishi na d'aga kanshi, da wani irin gudu Dr muh'd ya fice ya shiga room d'in da mufidah take ciki ya banka kofar da k'arfi ya shiga gaba d'aya su mumy sun firgita da ganin shigowar muh'd bai bi ta Kansu ba ya d'auki babyn ya fita da ita da sauri su ma suka bi bayan shi har da mufidah wadda dak'yar take tafia nabila na rik'e da ita.

Tuni muh'd ya shige room din kafin su mumy su k'araso an rufe kofar dole suka tsaya hankalin su a matuk'ar tashe.

Da sauri muh'd ya k'arasa wajen gadon yana nuna wa sadeeq babyn, bai da ikon daukan ta saboda drip d'in da yake hannun shi hannun shi yasa ya shafi fuskar ta xuwa kanta kafin dak'yar ya furta
"Allah ya raya min ke ya albarkaci rayuwar ki Nana khadijah"
Kallon muh'd yayi tare da yin wani irin murmishi da sake tsurar da muh'd ya bud'e bakin shi dak'yar yace
"Muh'd ina son ka kular min da musaddiq, mumy, daddy, mufidah da kuma 'yata don nasan ke mutum ne nagari, ka rokar min yafiya wajen iyaye na da d'an uwana da matata da duk wasu abokanan hurd'ata, kace su yafe min Alhmdullilah nasan ba me bina bashi yanxu tun kafin ciwon yaci k'arfina na biya kowanne ma'aikacin company na kud'in su, daga k'arshe muh'd ina son ka daukar min alkawari guda d'aya"

Tari ne ya sark'e shi yana yi sosai gaba d'aya doctor's d'in nan biyu hawaye ne yake xuba a idanun su na tausayi, muh'd kuwa kuka yake wiwi cikin rawar murya ya ce
"Fad'i alkawarin ka babban yaya insha Allah xan cika maka shi"
Sai da tarin ya lafa kafin yace "ina son kada ka bari kowanne namiji ya aure mufidah sai musaddiq d'ina don nasan xai kular min da ita da d'an da na haifa don Allah muh'd ka cika min wannan burin"

Cikin kuka ya rik'e hannun sadeeq yace "na d'auki alkawari babban yaya xan cika maka shi amman baxa ka mutu ba xamu rayu tare da kai ka tashi please"
Murmishi sadeeq yayi bai k'ara magana ba sai wasu hawaye da suke xuba a idanun shi yana kallon 'yarshi a hannun sadeeq tana bacci.
Chapter 23 · 0% Book details