← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 54

Sashe 31

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai farka ba sai yammaci sosai bathroom ya shiga yayi wanka tare da daura alawala ya fito jallabiya white ya xura tare da gabatar da sallahr da ake binshi bayan ya gama ya kwanta kan abin sallahn yana tunanin ta yanda xai fitar da mufidah daga cikin xuciyar shi gaba d'aya ya huta ma yana tunanin hawaye suna xuba daga idanun shi.

Wayar shi ce ta dauki k'ara akaro na ba adadi sunan mumy ne akan screen d'in picking d'in wayar yayi tare da sawa a hands free cikin sanyin murya mai tattare da damuwa ya gaida mumyn, jin muryar shi da tayi a hka sai taji hankalin ta ya tashi don hka tace

"My son what happened to u naji voice d'in ka very cool ?"

"Mumy ba wani abu just ina fama da ciwon kai ne throughout ko fita ban yi ba"

"No son da akwai damuwa a tattare da muryar ka, fad'a min matsalar ka baka da wadda ta fini don hka tell me "

Shiru yayi ya kasa sanar da ita abin da yake damun shi ,to mai xaice mata shi? Yana son matar Yah sadeeq nooo baxan iya fad'a miki ba mumy never! wannan abin kunya ne na bud'e baki na fad'a.

"Son ina sauraren ka fah"
"Mumy I don't know, just sometimes ina yawan tunanin ku ne kewar ku ce take damuna"

Shiru mumy tayi acikin xuciyar tana mai mamakin d'an nata da kafiya akan abin da yake so tasan dalilin shiga damuwar shi saboda muh'd xai auri mufidah, amman sai ta basar tace

"Okay son kadai na damuwa kaji bana son ganin ka cikin damuwa "

"Okay mumy ina daddy da afnan?"
D'an murmishi tayi kafin tace "daddy yana nan qlau hka ma afnan"
"Kusan 2 day's bamu yi waya fah ya daina damuwa da ni ko mumy?"

Er dariya tayi mumy kafin tace "daddy yana damuwa da rashin d'an sa mana yanxu hidima ce tayi mishi yawa "

Cikin mamaki yace "wacce hidima ?"
"Hmm ta aure mana xai aurar da 'ya'yan shi guda uku nan da two week's"

"Wanne 'ya'yan shi kuma mumy?"
Musaddiq ya tambaya cikin matukar mamakin abin da mumy tace

"Ohhh ya Allah daman bai fad'a mata ba mun xa6a maka matar da xaka aura sannan kuma muh'd da mufidah sun had'a kansu xasu yi aure"

Tun da mumy ta fara maganar musaddiq ya xama kamar mutum mutumi don ko kwakkwaran motsi ya kasa yi kafin kuma yace

"What! Mumy ni xaku yiwa aure da yarinyar da ban sani ba?"

"Yes! son kak'i mai da hankali wajen xa6ar macen da xaka aura don hka a matsayin mu na iyayen ka mun xa6a maka mace mai tarbiyya da ilimi wadda xata xauna da kai tsakani da Allah"

Jin shiru musaddiq bai yi magana ba yasa mumy tace
"Hello son are u on the line?"

Musaddiq wanda hawaye suke xarya akan fuskar shi yasa hannun shi ya gobe tare da saita muryar shi yace

"Mumy ngde da xa6in ku hak'ik'a ina alfahari da ku matsayin iyaye na nasan baxa ku xa6a min abin da xai cutar da ni ba Allah ya saka muku da mafificin alkhairi"

Gaba d'aya jikin mumy yayi matukar yin sanyi da abin da musaddiq yace mata idan ba hka suka yi mishi ba baxai yi aure yanxu ba ita kuma tana son ganin jikokin ta da yawa yanda Allah bai basu yawan haihuwa ba tana rokan Allah ya bawa musaddiq 'ya'ya da yawa, ajiyar xuciyar ta sauke a hankali cikin sanyin murya tace

"Ameeen son Allah yayi maka albarka ya baku xaman lafia da matar ka naji dad'in yi mana biyayya da kayi Allah ya baka yara masu yi maka biyayya ina alfahari da ke, insha Allah duk wani farincikin ka da walwalar ka suna daf da dawowa kamar da ka kwantar da hankalin ka son"

A hankali ya bud'e bakin shi yace "Ameeen mumy"
A cikin xuciyar kuwa cewa yayi mumy yanxu na fara shiga damuwa wane kwantar da hankali xan yi kuma bayan na rabu da farinciki na muradin raina.

Da hka suka yi sallama da mumy, yana ganin kiran muh'd but yak'i daga wayar daga karshe ganin yak'i dauka yasa muh'd rubuta mishi text message kamar hka," _My Friend ka dauki waya na please kasan kuwa halin da nake ciki da kin daga waya ta da baka yi ina cikin damuwa aboki?_

Wani tsaki yaja bayan ya gama karanta wa gaba d'aya wani irin haushin muh'd yake ji, shi yasan damuwar da ya jefa xuciyar shi yasan me yaji lokacin da yake fad'a mishi xai auri mufidah kuwa?, reply yayi mishi da cewa
" _kayi hak'uri aboki baxan iya daukan wayar ka ba sai xuwa wani d'an lokaci akawai dalilin hka kada ka damu, Allah ya tabbatar da alkhairi a auren ka"_.

Yana gama typing d'in message d'in yayi sending bayan ya tafi sai kawai yayi switch off d'in duka phone's nashi ,tukunna ya kwanta yana jin wani irin yanayi atattare dashi shi kenan na rabu da mufidah a karo na biyu na dad'a yin sake kuma nasan wannan saken da nayi na har abada ne, wasu sababbin hawayen ne masu xafi suke fita a idanun shi..........

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

*PAGE 40*

A wani matuk'ar tashin hankali da firgici mufidah ta mik'e tsaye hawaye na fita a idanun ta tana mai girgixa kanta saboda tsabar shiga rud'u da tashin hankali ta kasa magana sai girgixa kai, mumy ce ta tashi tare da rik'o hannun ta xaunar da ita tayi tare da goge mata hawayen fuskar ta da suke xuba da tissue d'in da xaro amman kamar bata goge wa saboda hawayen basu tsaya ba.

Kunnen tane suke amsa kuwwar maganar da abban ta ya gama yi mata yanxu bayan sun gama gaisa ne dashi da umman ta ga mumy,daddy a xaune a palourn sai ita ya fara da cewa

"Mufidah na gaji da yi miki magana akan ki tsaida hankalin ki waje d'aya ki fitar da mijin aure, wajen shekara hud'u da mutuwar sadeeq baxa kiyi hak'uri ki kwantar da hankalin ba, kalli iyayen shi da suka haife shi sun rungumi kaddara sun hak'ura tsakanin su sai dai addu'a kuma nasan duk son da xaki nuna mishi bai kai iyayen shi ba"

Palourn yayi tsit baka jin motsin komai, mufidah tun lokacin da Abba ya fara magana hawaye suke tsere a fuskar ta gaba d'aya ta rasa tunanin yi taya xasu fahimce ta ne?, ita fah gaba d'aya auren ne bata so wa xata aura ita yanxu babu wanda ta ta6a tsaya wa dashi da sunan xance duk wadanda suke son ta bata sauraren su.

Cigaba da maganar shi Abba yayi bayan ya ajiye numfashi yace
"Ganin kin k'i tsayar da mijin aure ne yasa na yanke hukuncin neman wadanda suke xuwa neman auren ki, na sanar da Alhj Abubakar hkn da ya tara su mai auren ki da gaske ya turo manyan shi ayi magana, sai kuma kafin hka Dr muh'd yaxo mana da xancen yana son ki xai aure ki shine nan take muka aminta tun da munsan ko wane muh'd don hka ba wani 6ata lokaci muka tsayar da bikin nan da sati biyu"

A matuk'ar gigice ta d'ago kanta tare da kallon abban idanun ta na xubar da hawaye cikin rawar murya take cewa

"Ab......Abba ka....ka rufa min asiri don Allah kada ka aura min muh'd ni sam bana son yin aure, mumy, daddy ku bawa Abba na hak'uri"

"Inaaa mufidah lokaci kuma ya k'ure don baxan yi magana biyu ba kiyi hak'uri ki cigaba da addu'a kawai amman auren ki kamar anyi angama ne"

Shine fa ta mik'e tana girgixa kanta ta kasa maganar ma har mumy ta rik'o ta tare da xaunar da ita, cikin tsananin tausayin mufidah daddy yace
"Ya kamata aboki atausaya mata kabar ta a hankali ta xa6i wanda take so"

Girgixa kai Abba yayi tare da cewa "baxai yiwu ba Abubakar idan ba hka nayi mata ba baxa ta shiga taitayin ta ba "

"Kwarai kuwa wannan hukuncin shine dai dai "
Cewar umma yayin da mumy ta janyo mufidah suka fita xuwa d'akin ta nan ta rarrashe ta dakyar tayi shiru kukan ya koma na xuci sai ajiyar xuciya take idanun ta sun kumbura sunyi ja hka fuskar ma tayi jawur da ita saboda tsananin kuka, wani axababben ciwon kai tare da wani xaxxafan xaxxa6i ne ya rufe ta ruf lokaci d'aya.

Tun daga lokacin mufidah ta dai na walwala rai a junkushe ko dayaushe bata da wani abin sai dai ta kule cikin bedroom tana aikin tunani da kuka,sosai afnan ta shiga damuwa ganin yanda mameen ta ta canja gaba d'aya ko irin wasan nan da take mata yanxu ta daina, lokaci d'aya mufidah ta wani rame ta xabge ko cikakken abinci bata iya ci sosai, xuwa hospital ma Abba yace ta dakata da xuwa sai bayan anyi auren idan mijin ya yarda sai ta cigaba.

Shi yasa yanxu bata fita ko'ina daga d'aki sai d'aki mumy itama duk ta shiga damuwa saboda tana matuk'ar son mufidah batason tana ganin ta cikin damuwa,kullum cikin rarrashin ta take, gashi a wannan lokacin kusan kullum sai tayi mafarki da musaddiq fuskar shi dauke da tarin damuwa abin ya fara bata tsoro yanda ita ba wani sashi a ranta tayi ba mance wa take dashi sai ko mumy,afnan da muh'd sun ambaci sunan shi take tunawa dashi.

A wannan time d'in tsakanin musaddiq da mufidah baxan iya fad'a muku wanda yafi shiga damuwa ba, shi musaddiq tunanin rabuwa da mufidah yake wanda sonta har yanxu d'awainiya yake dashi ko raguwa bayayi ga kuma auren da su mumy suke shirin k'ak'aba shi tabbas duk yarinyar da tayi gigin auren shi har ya mutu baxa ta ta6a jin dad'in aure dashi ba, don xuciyar shi babu son wata d'iya mace sai mufidah xuciyar shi ta gama kar6ar so akan mufidah ta rufe wannan shafin, yasha rashin lafia sosai don sai da ya kwanta a hospital na tsayin wajen kwana ki uku saboda ciwon shi da ya tashi yasha wahala ba kadan ba duk ya rame abin tausayi.
Chapter 31 · 0% Book details