Sashe 51
Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bayan sun k'arasa gida ne mamaki ya kama Mufidah da Musaddiq ganin yanda gaba d'aya aka canja fasalin gidan, side d'in da Sadeeq da Mufidah suka fara zama tuni an rushe shi, an sake wani sabon fasalin mai kyau da tsaruwa, komai an canja na gidan tamkar bashi ba.
A part d'in su Mumy aka zauna bayan anyi sallahr mangarib da ishsha ne, aka zauna yin kwarya kwaryar walima ta farincikin dawowar su Musaddiq gida lafia, anci ansha anyi musu addu'ar fatan alkhairi, kafin kuma kowa ya kama gaban shi cikin tsantsar farinciki.
Bayan watanni biyu da dawowar su Mufidah Nigeria Nabilah matar Yah Omar ta haihu an samu baby girl, ai kuwa sun sha suna yarinya taci sunan Mufidah ba k'aramin jin dad'i Mufidah da Musaddiq suka yi ba, ai kuwa babyn tasha kaya sosai a wajen su.
Bayan suna da kwana biyu ne Mufidah ta fara zazza6i sosai mai zafi nan Musaddiq ya rud'e sosai babu 6ata lokaci ya duba ta abin ka da matar likita nan ya hango babyn shi d'an wata biyu da sati uku a tare da ita, ai kuwa ya d'aga ta yana juyi da ita a cikin bedroom d'in cikin mamaki take kallon shi kafin ta bud'e baki tace
"lafia dear? "
Sakko da ita yayi tare da zaunar da ita kan sofa ya dire gwiwowin shi a k'asa tare da rik'o hannun ta cikin nashi yace
"my sweet baby ina matuk'ar farinciki yau saboda na kusan xama uba shine baki fad'a min ba sai da na gano da kaina koh? "
Wani murmishin jin kunya ta saki tana kare fuskar da hannun ta tace
"ni....ni fah bansani ba da gaske "
Tashi yayi ya xauna kusa da ita idanun shi cikin nata yace
"ina son ki Mufidah bazan iya rayuwa babu ke ba kiyi min alkawari na kasance wa dani har abadan ba xaki guje ni ba"
Bakin ta takai saman le6en shi ta sumbata kafin ta d'ora hannun d'aya cikin nashi tace
"nayi alk'awarin kasance wa da kai my man har k'arshen rayuwa ta i luv u musaddiq "
"i luv u too habibty "
Ya k'arasa fad'i yana shigar da bakin shi cikin nata soyayya sosai suka gwada wa junan su a wannan lokacin don Mufidah ma ta mance da wani ciwo sai da ta dawo dai dai tukunna ta sanya mishi kukan shagwa6a ai kuwa ya dunga yi mata dariya kafin daga bisa ni ya 6ige da rarrashin ta.
Su Mumy sunyi matuk'ar farin ciki da wannan albishir d'in da Musaddiq yayi musu na samun jika, daman tuni ta dauke Afnan daga wurin su tana hannun ta duk da kuwa gida d'aya suke zaune, su umma ma sunyi farinciki sosai, amman babu wanda ya kai Muh'd farinciki abokin shi ya samu matar da yake so gashi har zuri'a zata fara shiga tsakanin su, lokacin da Musaddiq yake sanar da Muh'd d'in bayan ya gama taya shi murna ne yace
"aboki wai ina ciwon xuciyar taka ne? "
"yaro tun da zuciya ta samu abin da take so, ai kuma shikenan "
Dariya Muh'd yayi kafin yace
"Toh Allah ya k'ara lafia "
"Amin, don wani time d'in fah sai a hankali tana yi min ciwo, sai dai ina kok'ari wajen kiyaye abin da zai taso min da ciwo, kaddara tawa kenan Muh'd "
Wani mugun tausayin shi ne ya kama Muh'd, nan ya yi mishi addu'ar Allah ya bashi lafia, kafin su yi sallama da junan su............
Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲
*Written by*
Aishat A Muh'd
♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:[email protected]
*PAGE 59*
Cikin kwanciyar hankali suka cigaba da rainon cikin Mufidah, su Musaddiq sai rawar kai ake za'a samu baby, kula da soyayyar Mufidah kullum k'ara k'aruwa take cikin zuciyar shi.
Ta 6angaren Mufidah duk wani kyautata wa tana yi mishi sosai, bata yi duba da irin son da yake mata ta wahalar dashi ba, biyayya sosai take mishi duk wani abin da yake so take yi mishi, tana kok'arin kiyaye abin da zai d'aga mishi hankali har ciwon shi ya tashi.
Duk lokacin da ta tuna sanadiyyar son ta ne, ya kamu da ciwon zuciya har kuka take yi mishi na tausayin shi, a haka cikin ta yake ta girma sosai, gashi babu wani laulayi sosai, sai dai yana sanya ta kwad'ayi.
Ana cikin haka nafisat matar Muh'd ta haihu an samu baby boy, waiii murna wajen Musaddiq ba'a magana, kamar Mufidah ce ta haihu haka yake jin shi.
Ranar suna sun yi hidimar suna sosai inda jaririn yaci sunan Musaddiq, rasa inda Musaddiq zai sa kanshi yayi don farinciki hak'k'a Muh'd aboki ne na gari, ya d'auke shi tamkar Yah sadeeq d'in shi, ya kashe kud'i sosai Musaddiq a wannan sunan,komai yak'i yarda Muh'd yayi sai shi, Mumy, daddy da Mufidah ma sun yi hidima sosai,sai dai fatan Allah ya raya lil Musaddiq.
*AFTER 2 MONTH'S*
Mufidah zaune take a parlourn Mumy akan kujera, ta mik'e k'afafun ta saman centre table, tana cin wani gashashshen nama ya sha cabbage, tomatoes and onions akai ga yaji mai dad'i a gefe tana dangwala dashi, gefe d'aya kuma ga coconut drink wanda yasha milk gashi yayi sanyi, cin abinta take hankali kwance.
Duk wannan hidimar Mumy ce tayi mata, don ta hana ta yin wani aiki ko girki, kuma duk abin da tace tana so Mumy na kok'ari wajen sama mata shi, gaba d'aya ta duk'ufa wajen cin naman, batasan Musaddiq ya shigo parlourn yana tsaye sai kallon ta yake dawowar shi daga hospital kenan.
Ta d'auka naman a jikin fork tana kok'arin kai wa bakin ta, taji an rik'e hannun ta da ta da yake d'auke da fork d'in, da d'an sauri ta juya kanta baya suka had'a ido da Musaddiq, sakarwa junan su murmishi suka yi cikin so da kauna, kafin Musaddiq ya juya hannun ta zuwa wajen bakin shi ya sanya naman har da wani lumshe idanun shi saboda dad'in shi, kafin ya bud'e su ya watsa kan fuskar Mufidah.
Wadda ta ta6e fuska tana shirin yin kukan shagwa6ar da ta saba yi mishi, ya bud'e bakin shi yace
"Wow gaskiya Mumy tana ji da ke, irin wannan cin dad'i haka, sai an bari na tafi hospital take shirya miki abin dad'i don kada na ci koh, aikuwa wannan ya zama rabo na daman yunwa nake ji "
Ya k'arasa fad'i yana d'aga mata gira, turo bakin ta tayi gaba tare da cewa
"ni dai gaskiya a'a, ai ba laifi na ne ba, babyn kane yake son ci "
Mak'e kafad'a yayi tare da cewa
"uhm uhm ni ban yarda ba, kullum ai tace wa baby na yake son abu don dai bashi da bakin magana "
Yana gama fad'in haka ya kar6e plate d'in hannun ta, zama yayi kusa da ita sannan ya fara ci ,ganin haka yasa Mufidah fara tuttura k'afa zata fara kukan shagwa6a, dariya ya fara yi mata tare da sanya hannun shi ya d'an ja kumatun ta yace
"sweet baby rigima ko Afnan kin fita rigima, toh dai wannan duk kukan shagwa6ar ki sai na cinye "
Ya k'arasa fad'i yana mata gwalo, ai kuwa ta saki kukan shagwa6ar da babu hawaye sai goge idon da ake, shi kuwa Musaddiq sai tsokanar ta yake yi, gefe d'aya kuma yana cin naman tare da shan coconut drink d'in nan.
Ana cikin haka sai ga Mumy ta shigo parlourn, ta tarar da Musaddiq yana faman tsokanar ta, girgiza kanta tayi tana murmishi idan da sabo ta saba da rabon wannan rigimar kullum, k'arasa wa tayi cikin parlourn tare da kallon Musaddiq tace
"Ohhh ni, Musaddiq me yasa ka fiye tsokanar ta ne? "
Turo bakin shi yayi irin na shagwa6ar nan yace
"Mumy kullum sai kin nuna son kai, idan na tafi hospital sai ki ta bata abin dad'i tana ci ni ba'a ajiye min "
Murmishi Mumy tayi tare da cewa
"kai ai babba ne kuma kaga abin da take d'auke dashi, dole ana bata abin da take so, ina ce jiya wurin karfe 10 na dare ka fita samo mata shawarma da take son ci"
D'an sosa kai yayi yana kallon ta, don ya tuna rigimar da tayi mishi jiya da dare, sai da suka kwanta bacci ta tashe shi ita shawarma take son ci, jiki na rawa ya tafi siyo mata, ko da ya dawo rabin d'aya ta iya ci a duk yawan da ya siyo mata, kafin yace
"Ehemm na tuna Mumy, but ni ana ajiye min komai aka yi mata tun da ina taya ta rainon babyn "
Murmishi Mumy tayi tare da cewa "shikenan za'a ajiye maka, amman na yau a hak'ura a bar mata"
Mik'a wa Mufidah plate d'in yayi yana wani langa6e kai, kallon shi tayi sai taji ya bata tausayi, cikin murya k'asa k'asa don kada Mumy taji tace
"My M, na bar maka kaci, daman na k'oshi "
Ta k'arasa fad'i tana yatsina fuska, murmishi yayi tare da jan karan hancin ta yana cewa
"Hmm da gaske kike habibty? "
D'aga mishi gira tayi, nan ya d'an huro mata kiss da bakin shi, aikuwa ta lumshe idanun ta tare da bud'e su alamar ta kar6i sak'on nashi, lokaci d'aya suka sakarwa junan su murmishi.
Mumy ma murmishin ta saki, zuciyar ta fal farinciki da kwanciyar hankalin d'an nata, kuma tana jin dad'in yanda Mufidah take bashi kula wa sosai.
"Mumy ta bar min ba ashe ta k'oshi ma ta tsaya yi min rigima gashi har ya fara sanyi "
"Hmm ka dai dame ta shi yasa ta bar maka "
"Da gaske nake fah Mumy, koh Sweet baby? "
"naji shikenan "
Cewar Mumy, nan ya fara ci suna d'an ta6a hira har ya gama, ya sanya hannu zai janyo tissue ya goge bakin shi, da sauri Mufidah ta sanya hannu ta dauko mishi tissue paper d'in ta bashi, kar6a yayi tare da cewa
"thank u habibty, Allah yayi miki albarka yasa ki haihu lafiya "
Cikin jin dad'in addu'ar da yayi mata tace
"Amin sweetheart ".
Tashi yayi tare da cewa
"Mumy yau na gaji, zan d'an je na huta kafin lokacin mangarib yayi "