← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 54

Sashe 12

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana k'arasa wa gida Ko shiga da motar bai yi ba cikin gidan ya barta a nan waje ya shiga, saboda cikar da aka yi en biki yasa daddy kiran mumy a waya Allah ya taimaka wayar tana rik'e a hannun ta ba 6ata lokaci ta d'auki wayar ganin kiran maigidan ta ne "kixo yanxu ina wurin parking space ki taho da mayafin ki "
"toh shikenan "

Abin da mumy tace kenan sam bata yi tunanin wani abun ba ta d'auka ko abokanan shine yake so su gaisa, cikin en mintuna mumy ta fito tana yafa mayafi taci gayu sosai cikin wata arniyar shadda an sha adon gwal sai kyalli take yau ranar farinciki ne a gare ta sam baka ce ita ta haifi Yah sadeeq da musaddiq ba.

Turus taja ta tsaya ganin daddy shi d'aya a wurin gaba d'aya fuskar shi d'auke da damuwa cikin tashin hankali tace "Abban sadeeq lafia? "

D'ago kai yayi ya kalli mumy sai da gaban ta ya fad'i ganin tsantsar damuwa a cikin idanun na shi hannun shi ta rik'o tana cewa "Yah mijina me yake faruwa da kai? "

Runtse idanun shi yayi kafin yace "ina son ki kwantar da hankalin ki nutsu da abin da xan fad'a miki "
Cikin xakuwa mumy tace "ina sauraren ka? "

Sai da yayi dan shiru Sannan yace "musaddiq ne ba lafia yana hospital "

"me yake damun shi? "
Cewar mumy a rikice, girgixa kai daddy yayi tare da cewa "sai dai mun je xamu sani yanxu dai mu tafi "

Gaba d'aya mumy ta kasa tafia ta cak waje d'aya sai da daddy ya rik'e mata hannu har xuwa wajen mota shi ya taimaka mata ta xauna saboda gaba d'aya mumy ba'a hayyacin ta take ba, lokacin da suka K'arasa asibitin a reception din hospital suka had'u da Dr muh'd wanda ya fito kar6ar wata allura da xai yiwa musaddiq.

Gaba d'aya jikin su yayi sanyi ganin yanda muh'd idanun shi sunyi ja alamar yaci kuka sosai, shi yayi musu jagora xuwa cikin d'akin suna shiga ganin musaddiq da suka yi kamar gawa yasa su furta kalmar "inallilahi wa'inna ilaihir rajiun "
Su kayi kan musaddiq gaba d'ayan su a rikice............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ *EXCLUSIVE WRITER'S FORUM*

_Wannan shafin na ki ne *Asy khaleel* fatan alkhairi a gare ki Allah ya bar xumunci, ni Aishat ina k'aunar ki sosai kuma kirkin kine yaja miki dumbin masoya, ina miki fatan alkhairi a duk inda kike_

*PAGE 15*

Su kayi kan musaddiq gaba d'aya a rikice, tuni mumy ta fashe kuka tana cewa "wayyo Allah nah musaddiq me ya mayar min da kai Hka wannan wanne irin ciwo ne? "
Kuka sosai mumy take har da majina hankalin ta ba k'aramin tashi yayi ba na ganin d'annata a hka, shi kuwa daddy xama yayi tare da k'urawa musaddiq ido yana kallon shi ya ma kasa furta komai tsabar tashin hankalin da yake ciki.

"muh'd fad'a min abin da yake damun musaddiq? "

Dr muh'd xama yayi kusa da kafar daddy cikin rawar murya kamar xai fashe da kuka ya fara cewa "daddy kayi hak'uri akan rufe ma abin da yake damun musaddiq da muka yi da dad'e wa, saboda amana musaddiq ya bani akan kada na furta abin da yake damun shi, ina kok'ari na wajen kwantar mishi da hankali tare da bashi shawarwari amman yak'i dai na sa damuwa acikin xuciyar shi, so shine kuma d'axu wurin d'aurin auren Yah sadeeq ciwon nashi ya tashi "

Duk sun xuba wa muh'd ido suna sauraren shi mumy mai yin kuka ma shiru tayi don ta fahimci abin da ake cewa sai dai hawaye bai bar xuba daga idanun ta ba, cikin xakuwa a fad'i ciwon da yake damun musaddiq daddy yace
"toh wanne ciwo ne yake damun shi muh'd sanar da ni?"

Sai da muh'd ya d'auki tsawon mintuna kan shi a k'asa Kafin kuma cikin sanyin murya yace "daddy mumy Kuyi hak'uri musaddiq yana cikin wani mugun yanayi, ba wani abu ne yake damun shi sai ciwon xuciya "

Lokaci d'aya suka mik'e daddy da mumy suna furta "Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun "
Suka furta lokaci d'aya, mumy hannu ta d'ora a kanta tare da rushe wa da wani irin kuka mai ban tausayi, yayin da daddy ya maimaita cewa "ciwon xuciya ne yake damun d'ana, me musaddiq ya nema ya rasa da a rayuwar shi da har wannan mugun ciwon xai Kama shi? "

Hannun daddy Dr muh'd ya kamo tare da xaunar dashi kuka muh'd kawai yake ganin yanda wad'annan bayin Allahn yanda suka shiga wani hali mai ban tausayi.

"Ya fad'a maka abin da ya sa a ranshi har ya kamu da wannan ciwon? "
Cewar daddy yana kallon Dr muh'd, toh fa muh'd ya shiga tsaka mai wuya yanxu xai fad'a musu gaskiar abin da yake damun shi anya kuwa xai sanar dasu yarinyar da yake masifar so ita ce mufidah matar yayan shi sadeeq gaba d'aya ya rasa abin da xai ce gashi sun xuba mishi ido suna kallon shi kowanne yana son jin abin da xai fad'a.......

A 6angaren amarya mufidah kuwa tun lokacin da taji an d'aura auren ta da Yah sadeeq sai gaba d'aya jikin ta yayi matuk'ar yin sanyi, sai tsokanar ta aike en uwa suke amman babu bakin magana sai dai tayi musu yak'e, don gaba d'aya baka ce ga yanayin da take ji ba farinciki ko akasin hka, tana kule cikin bedroom d'in umman ta, tun lokacin da aka sa lokacin auren bata iya cin abincin kirki ba sai tunani kuma ta rasa tunanin da take, ita dai tasan wani lokacin tana tunanin musaddiq musamman lokacin da ya kaita gidan shi ta wanke mishi kayan da ta 6ata mishi, da lokacin da take rungumar shi tana neman taimakon shi xuwa lokacin da taje gidan su da ya kusan fad'uwa har ta rik'o shi suka had'a jiki, sosai tana tunano lokacin har wani lokacin tana murmishi, ta rasa gane abin da yake damun ta shi yasa gaba d'aya ta rame saboda da tunani ga rashin son cin abinci.

Umma, nabila da Yah Omar sun yi nacin duniya da ta fad'a musu abin da yake damun ta amman sai tace ba komai, to me xata ce musu ita kanta wani lokacin sai ta rasa ma tunanin da take, abinci kuwa sai umma ta sa ta a gaba da fad'a take iya ci, sai dai Kyan da ta k'ara don tasha gyaran jiki ciki da waje don umma ba wasa a wannan 6angaren ta tsaya tsayin daka ta gyara d'iyar ta daman ita kad'ai Allah ya bata mace sai Yah Omar dole ta gyara ta.

Shigowar umma cikin d'akin yasa mufidah saurin d'aukar wayar ta tana danna wa don bata son umma ta gane tunani take, amman duk da hka sai da umman tace
"Hmmm ana nan ana sana'ar ko mufidah? "
Er dariya ta k'ak'alo tayi tare da cewa "Haba umma ba tunani nake ba, hutawa nake na gaji da hayaniya wlh"
"ae sai hak'uri taron kenan, gashi can ana d'aukan pictures da en uwa da kuma angwaye sai ki fito "
D'an 6ata fuska mufidah tayi tare da cewa "ni gaskia umma na gaji "
"Haba er umma d'aure ki tashi kin ga abin tarihi ne "
Kafin mufidah ta ce komai sai ga wasu emmata sun shigo sun ci uban kwalliya 'ya'yan k'anin baban su mufidah ne, hannun ta suka rik'o tare da fito wa xuwa main parlour inda ake d'aukan pictures, duk inda mufidah ta gifta idanun Yah sadeeq akanta har sai da Yah Omar ya fara tsokanar shi, shi dai sai murmishi yake don yau ranar farinciki ce a gare shi, ita kuwa mufidah duk ta gaji da kallon da Yah sadeeq yake mata K'arshe sai ta sulale ta gudu d'aki.

******

"kai muke saurare muh'd maxa fad'a min gaskia? "

"uhm daddy daman wata yarinya yake masifar so, sai kuma bai furta mata da wuri ba har wani ya riga shi iyaye suka shiga xancen shine abin ya kasa cire shi daga cikin xuciyar shi saboda yana masifar son ta "

"Wace yarinya ce muh'd? "
Mumy ta tambaye shi cikin mamaki sosai don ko da wasa musaddiq bai ta6a nuna musu yana son wata yarinya ba.
"Mumy sunan ta mufidah kuma yau ne d'aurin auren ta ma"
"Wacce mufidah kake nufi??? "
Lokaci d'aya Mumy da daddy suka furta gaban su na mugun fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia.................

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A Muh'd

♻ *E.W.F*

_Wannan shafin naku ne ma'abota kirki da karamci, Anty maijiddah ta cikin group d'in (novella's lodge) da fatyma (Mrs Omar), ina ji daku sosai gashi kuna k'aunar littafin nan sosai, Allah ya bar mu tare ina yin ku sosai, fatan alkhairi a duk inda kuke_🤝😍

*PAGE 16*

Lokaci d'aya suka furta gaban su na fad'uwa tsoron su kada ya kasance ace hasashen su ya xama gaskia, Cikin xak'uwa da son jin cigaban xancen mumy tace
"Muh'd fad'a mana wace mufidah?"

Sai lokacin Dr muh'd ya tuna kato6arar da yayi don baisan lokacin da bakin shi ya furta hkan ba, kallon mumy da daddy yayi wad'anda suka xuba mishi ido suna kallon shi kowannen su ya matsu yaji abin da muh'd xai fad'a, kauda kanshi yayi daga barin kallon su tukunna ya ce
"Am mumy, daddy yarinyar da musaddiq yake so wato mufidah tana xaune a garin katsina karatu ne ya kawo ta buk, so shine iyayen ta suka aurar da ita, gashi musaddiq yana son ta sosai, kasa cire ta yayi daga ranshi shine har ya haddasa mishi kamuwa da ciwon xuciya"

"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
Daddy ya fad'a tare da dafe kanshi, yayin da mumy sai taji sam bata yarda da abin da Dr muh'd ya fad'i ba, kuma ta dauki niyyar bincika wa don ta fahimci gaskiar xancen.
Chapter 12 · 0% Book details