← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 54

Sashe 50

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun a cikin daren gaba d'ayan su, kowanne ya kamu da zazzafan zazza6i a jikin su, har zuwa wayewar gari, dakyar Musaddiq yayi k'arfin hali ya tashi, wanka yayi tare da alwala sannan ya fito a toilet.

Sallah yayi kafin ya taimaka wa Mufidah ita ma tayi wanka, sai da tayi sallah tana idar wa wani nauyayyen bacci yayi awon gaba da ita, ga jikin ta zafi har yanzu zazza6in bai sauka ba.

Shima Musaddiq d'in bacci ne ya d'auke shi mai nauyi sosai, don ba'a samu cikakken bacci ba, gashi kuma an tashi da zazza6i.

Knocking d'in kofar da ake yi ne ya tashi Musaddiq daga baccin da yake yi, dakyar ya iya lalla6a wa ya tashi tare da bud'e kofar, Afnan ya gani a tsaye tana kuka da alama ta dad'e tana yin knocking d'in, jikin shi ta fad'a cikin muryar kuka tace

"daddy ina kuka shiga kai da mami? "
Shafa kanta yayi tare da cewa "Afnan bacci muke yi, sannan mamin ki bata jin dad'i, kada ki tashe ta mu je na shirya ki, akwai skul "

Nan yaja hannun ta zuwa d'akin Mufidah ya shirya ta cikin uniform d'in skul, sannan suka fito ya had'a mata tea tare da soya mata eggs, tayi breakfast sannan ya wuce kai ta skul, bayan ya ajiye ta ne ya dawo gida yana addu'a cikin zuciyar shi Allah yasa Mufidah zazza6in jikin ta ya sauka.

Lokacin da ya shiga bedroom d'in shi bai tarar da Mufidah ba a ciki ba, sai ya wuce bathroom yayi wanka, sannan ya fito ya shirya cikin wani yellow 3quater and white T-shirt mara hannu, ya fesa different perfumes a jikin shi kafin ya fito zuwa d'akin Mufidah, jin shi yake yau wasai dashi kamar wanda aka sauke wa wani babban abu a kanshi da cikin zuciyar shi.

Yana tunanin halin da suka kasance shi da Mufidah a tsayin daren jiya,murmishi ne shimfid'e a saman fuskar shi na farinciki da nishad'i, yana k'arasa shiga cikin d'akin, ya hango ta kwance saman bed har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga har k'asa mai hannun vest, irin mai kwanciya a jikin nan ce, idanun ta a lumshe suke but ba bacci take ba, tunanin Musaddiq d'in ta take.

Daddad'an k'amshin perfumes d'in shi ne ya ziyarci cikin hancin ta, d'umin jikin shi taji a nata, a nutse ta bud'e idon ta ai kuwa suka had'a ido, yana wani haske ta da kyakkyawan murmishin shi, d'an hararar wasa tayi mishi tare kok'arin tashi zaune.

Cikin sauri ya janyo ta zuwa jikin shi yana cewa
"sweet baby nah ya zazza6in naki, dafatan ya sauka ?"
Ya k'arasa fad'i yana tatta6a jikin ta, jin babu d'umi yasa shi sakin ajiyar zuciya yace

"naji jikin naki babu d'umi alamun ya sauka, gashi ni kin shafa min har yanzu ban daina jin shi ba "

Kunyar shi take ji ta kasa yin magana, but fuskar ta d'auke da murmishi, ya gama karantar kunyar shi take ji,
"Baki tambayi ina Afnan ba ?"
Dakyar ta iya bud'e baki tace
"Hmm nasan ka kaita skul, tun da na tashi ban gan ku ba "

D'an murmishi yayi so yake ta d'ago kanta ya kalli face d'in ta, amman tak'i d'agowa, don haka ya sanya hannun shi ya dafe saitin zuciyar shi yace
"Wash! Allah nah zuciya ta"
A kid'ime Mufidah ta d'ago kanta tana kallon shi, ganin yanda ya kwanta sai juyi yake yana rik'e zuciyar shi, yasa Mufidah fara hawaye don duk a tunanin ciwon ne ya tashi, cikin rawar murya take cewa
"wayyo Allah, sannu Musaddiq don Allah ka tashi mu tafi hospital "

Ganin yanda ta rud'e ne yasa shi tuntsire wa da dariya, sakin bakin ta tayi tana kallon shi, ga hawaye na zuba, kawai sai ta d'auko pillow ta fara dukan shi da shi, Musaddiq yana dariya tare da yi mata gwalo kuma yana kare dukan.

Gajiya tayi ta zube kan bed tana mayar da numfashi, janyo ta jikin shi yayi yana cewa
"nima na rama abin da kika yi min jiya a wurin beach "
Murmishi kawai take tana girgiza kanta, wato ashe ya gane karyar ciwo tayi.

"ina son ki Mufidah "
Ya furta hakan cikin kunnen ta, " nima ina son ka sosai "
Ta mayar mishi da amsa suna yiwa junan su murmishi.
A haka suka tashi zuwa parlour, kitchen suka shiga tare suka had'a breakfast bayan sun gama ne, suka sake koma bacci..........

Aishat A Muh'd ✍🏻
[13/11, 2:05 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*
Aishat A Muh'd

♻ *£xclusive Writers Forum*
*Likes nd comment's fb page*👇🏻
#https://www.facebook.com/Exclusive-Writers-Fans-E-W-F-1922297541423276/
Email:[email protected]

*PAGE 58*

Baccin su suka sha sosai, basu ankara da tafiyan lokaci ba sai da aka kirawo Musaddiq a waya daga skul d'in su Afnan kan yazo ya d'auke, don anjima da tashin su, cikin sauri suka shiga wanka tare suka yi, bayan sun fito ne suka shirya a gurguje don tafiya d'auko Afnan.

Bayan sun gama shirya wa ne, suka tafi school d'in d'auko Afnan, suna d'auko ta ya wuce dasu restaurant suka ci abinci,sannan suka wuce wayo cikin tsantsar farinciki suke a wannan ranar, sai da dare yayi suka dawo gida a gajiye.

Wanka Mufidah tayi wa Afnan ta kwantar da ita, sannan ta shiga nata wankan kafin ta fito har Afnan tayi baccin ta saboda gajiyar da tayi, tana cikin shirya wa Musaddiq ya shigo d'akin yana cewa

"My sweet baby laifi me nayi aka bar ni, ni da a parlour? "
Jiyo wa tayi tana murmishi tace
"ba laifin da kayi my man, wanka na tsaya yi ne "
Shima murmishin yayi tare da cewa
"Yayi kyau hakan habibty, mu tafi d'akin mu koh ya?"

Yayi maganar yana d'aga mata gira, sunkuyar da kanta tayi tana murmishi tace
"okay, yiwa Afnan addu'a kafin na k'arasa shirya wa "
"toh angama ranki ya dad'e"
Cikin sigar tsokana tace "Ohhh har na kai wannan matsayin? "

Yana jan hancin ta yace "kin ma wuce haka baby nah "

Yana gama fad'in haka ne yayi wa Afnan addu'a a jikin ta, sannan yaja ta suka bar d'akin zuwa nashi, hmmm wannan daren ma an bawa soyayya hakk'in ta sosai, don tsakanin Musaddiq da Mufidah kowanne yana nuna wa d'an uwan shi irin kalar son da yake mishi, kafin daga k'arshe bacci mai dad'i ya d'auke su, suna rungume da junan su, zuciyar kowa fal farinciki.

*_ASUBA TA GARI MUSFEEDAH_*

*AFTER 1 WEEK*
(Agurguje)

Cikin 'yan kwanakin nan tsakanin Mufidah da Musaddiq soyayya kawai ake xuba wa, suna bawa junan su kulawa sosai, hankalin su ya kwanta sun yi fresh abin su, suna waya sosai dasu Mumy, Daddy, Umma, Abba, Nabila, Yah Omar dasu Muh'd da matar shi Nafisat, ana jin lafiyar juna.

Duk wani shiri Musaddiq ya gama yi na koma nigeria, hospital d'in da yake aiki yayi musu sallama tare da ajiye musu aikin su, sam basu ji dad'in barin Musaddiq asibitin ba, don ba k'aramin taimaka musu yake ba babban likita ne da yasan me yake yi, da haka suka rabu cikin tsananin kewar shi.

Sai da Afnan ta samu hutu a school tukunna suka tattara inasu inasu suka bar Australian, suka tafi k'asar switzerland suka samu hutun tsayin sati uku acan.

Kafin su nufi k'asar Saudi Arabian su yi umarah, sai da suka yi wajen sati hud'u a Saudi Arabian saboda Musaddiq ya d'an yi fama da mura da zazza6i, kafin daga baya ya warware su fara shirye shiryen dawowa gida Nigeria, sun yi tsarabar su sosai wadda zasu raba wa 'yan uwa, duk k'asar da suka je sai da suka yi tsaraba.

Daman tuni an sanar da 'yan uwa dawowar su don haka aka fara shirin tar6ar su, ba irin Mumy da tafi kowa farinciki saboda Musaddiq da ya fad'a mata ya dawo gida kenan bazai koma Australian ba, ba k'aramin jin dad'i da farinciki tayi ba.

Jirgin da suka hau saukar yamma yayi sosai daf da mangarib, bayan jirgi yayi landing mutane suka fara fito wa 'yan uwa sai wara idanu suke su hango ta ina zasu gano su Mufidah.

Babu jima wa suka hango Musaddiq yana rik'e da hannun Mufidah, ga Afnan a kafad'ar shi tana bacci sun yi matuk'ar yin kyau sosai, fad'ar irin had'uwar da suka yi ma 6ata lokaci ne.

Duk sai aka zubo musu ido ana kallon su, ganin yanda suka yi matuk'ar dace wa da junan su, ga wani kyau da suka k'ara da ka gansu kaga fulanin asali.

Kunya ce ta rufe Mufidah ganin yanda ake kallon su, zame hannun ta tayi daga na Musaddiq kallon ta yayi kawai ya girgiza kai, tun kafin su k'arasa su Mumy ma suka taho aka had'u cikin farinciki, kowa bakin shi yak'i rufuwa saboda murna, nan aka gaggaisa da juna tukunna aka nufi motoci don tafiya gida.

Dr Muh'd wanda ya zuba wa Musaddiq ido ganin yanda yayi k'iba kamar ba shi ba gashi sai murmishi yake saki yana wani jifan Mufidah da wani irin kallon so, sai ya kasa daure wa yayi ya ta6o Musaddiq yana cewa
"lover boy adai kula ba mu kad'ai ba ne akwai surukan ka, kada ayi abin kunya a bari sai an ke6e "
Hararar shi Musaddiq yayi tare da cewa
"ke fah na fahimci d'an sa ido ne na k'arshe, ina ruwan ka da mu naga matata ce "

Dariya Muh'd yayi tare da cewa "d'an duniya, naga alama ma mun kusan samin baby da gani baka yi sassauci ba wajen uhm "
Bai k'arasa ba ya kwashe da dariya sai kawai Musaddiq ya biye mishi suka yi dariyar tare da tafawa, da haka suka k'arasa gida suna tsokanar junan su, uhm Aminan kwarai kenan, Musaddiq nd Muh'd kullum son junan su suke tamkar wasu 'yan uwa na jini, (ni kaina amintar su na birgine, don a yanzu kafin a samu irin aminan sai an tona, saboda son zuciya yayi mana yawa
yanzu, Allah kada ka bamu ikon cin amanar mutumin da ya d'auke ka matsayin aboki, amini kuma d'an uwa, Amin).
Chapter 50 · 0% Book details