← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 54

Sashe 16

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wurin first aid box ya nufa ya d'auko shi tare da duba abin da yake ciki, allura xai mishi kuma dole ya d'an sa wani abin a cikin shi kafin yayi mishi, don hka da sauri ya bud'e frige din musaddiq na bedroom ya tarar da fresh milk mara sanyi ya d'auko tukunna ya dawo wajen musaddiq jingina bayan shi yayi da pillow sannan ya fara bashi a baki a hankali bayan ya d'an sha ne tukunna yayi mishi allura tare da bashi magani, cikin en mintuna bacci ya d'auke shi ya fara gumi alamun xaxxa6in ya fara sauka, sai lokacin Dr muh'd ya saki ajiyar xuciya ta kwanciyar hankali.

K'arfe 9:30 mufida ta bud'e idanun ta da suka yi mata nauyi saboda sun kumbura sakamakon kukan da tasha kallon d'akin tayi taga sadeeq baya nan d'an ta6e baki tayi tare da tashi ta lalla6a ta shiga toilet wanka tayi ta fito kai tsaye wajen dressing mirror ta nufa ta shafa wani cream mai k'amshin apple tare da yin light make up a fuskar ta, wardrobe ta bud'e tare da d'auko wata swiss atampha d'inkin riga da siket ne under wear's ta d'auko bak'ak'e ta sanya tukunna ta sa atamphar tayi mata kyau sosai kalar ta amshe ta, tana cikin fesa perfumes ne sadeeq ya shigo yayi wankan shi yasha gayun shi cikin wata tsadaddiyar shadda light ash yayi kyau sosai don gaskia kusan kamar su d'aya da musaddiq bambamci su kad'an ne kamar wasu twins ko wasu twins d'in basa kama da junan su kamar hka.

Ajiye perfume d'in hannun ta tayi tare da tsugunna wa k'asan carpet cikin sanyin murya tace
"Ina k'wana sadeeq?"

D'ago ta yayi tare da rungume ta a kunnen ta ya rad'a mata "my wife lafia qlau, ya k'wanan bak'un ta da gajiya kuma".

Hannun ta tasa tare da rufe fuskar ta tana murmishi kafin kuma ta fara xare jikin ta cikin ta cikin nashi, sake rik'o ta yayi tare da cewa

"Ina xuwa my wife?"
"Wurin mumy xan je mu gaisa kaga yanxu 11 ta kusa"

"Okay muje mayi breakfast ma a can koh?"

D'aga kanta tayi alamun eh mayafin ta ya d'auko ya sanya mata da flate shoe ya sanya mata tukunna ya kano hannun ta ya rik'e suka fita daga part d'in su xuwa part d'in mumy, kallo d'aya xaka yi musu ka tabbatar amarya da ango ne kuma sun yi matuk'ar dace wa da junan su sosai, fuskar sadeeq fara'a ce kwance a fuskar yayin da mufidah ba yabo ba fallasa.

Da sallama suka shiga palon mumy da dinning wad'anda suke 6angaren dining table suna breakfast suka amsa fuskar su d'auke da fara'a, k'arasa wa wajen suka yi sai lokacin mufidah ta kwace hannun daga hannun sadeeq, tsugunna wa har k'asa suka yi suna gaida su cikin fara'a suka amsa musu tukunna mumy tace
"Da yanxu xa'a kai muku naku tun da kuma kun shigo sai muci tare bismillan ku"

Tashi suka yi duk suka xauna, daddy ne ya kalli mumy yace"kirawo musaddiq da muh'd sai mu yi breakfast d'in tare"

Dummm gaban mumy ya fad'i baxa taso musaddiq yaxo wurin nan ba don komai xai iya faruwa shiru tayi bata ce komai ba sai da daddy ya sake maimaita mata tukunna ta tashi cikin sanyin jiki xata tafi kenan ta hango musaddiq da Dr muh'd sun taho inda suke kan shi a sunkuye yake, tuni Dr muh'd ya hango mufidah tuni gaban shi ya hau fad'uwa hka ma mumy sun rasa ta yanda xasu janye hankalin shi daga wajen, muh'd ya jiyo da niyyar yi mishi amman ina har daddy da sadeeq sun gansu Dr muh'd mutuwar tsaye yayi hka mumy ma ta rasa abin yi................

_kuyi hak'uri da wannan fan's wlh mura, ciwon kai ne suke damuna dak'yar na iya wannan ma, dafatan xaku yi min addu'ar fatan samun sauk'i na d'ora daga inda muka tsaya, fatan alkhairi a gare ku masoyan yayi sake!_

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

_shafin naku ne abokan kirki, Queen bee marafa, real khady, jameesha, amal,nabilancy luv, ummu khady, mum useey, 'yar gatan hudah, ruksad and oll member's na exclusive writer's, ina matuk'ar alfahari da ku, Allah ya k'ara mana basirah tare da sauran marubuta en uwan mu, ina muku fatan alkhairi gaba d'ayan mu_🤝❤

*PAGE 22*

Bayan sun k'arasa airport ne a suka firfito daga cikin motocin da suke ciki,lokacin sauran mintuna 10 jirgin da musaddiq xai yi amfani dashi ya tashi, a lokacin ne Dr muh'd ya k'araso wajen hararar shi musaddiq yayi da sauri ya had'e hannayen shi alamar yayi hak'uri.

A gurguje musaddiq yayi sallama da iyayen shi bayan daman tun acikin mota daddy da mumy suka yi mishi nasiha sosai mai ratsa jiki kuma ya kula ya daina sa damuwa da tunani, sosai ya nuna musu xai bar tunanin komai yayi abin da ya kai shi su cigaba da taya shi addu'a, sun ji dad'in abin da ya fad'a musu nan suka sa mishi albarka tare da yi mishi fatan alkhairi.

Rungume daddy ya sake yi a karo na biyu idanun shi sun yi ja alamar daf suke da fara xubar hawaye, tukunna ya cika daddy ya rungume mumy sun dad'e a hka ya kasa sakin ta don ji Yayi gaba d'aya tafiyar ma ta fara fita a kanshi baya son yin nesa da iyayen shi da d'an uwan shi amman yasan shi kanshi dole yayi nesa da gida don yafi samun nutsuwar xuciyar shi tare da k'okarin fitar da son mufidah daga cikin xuciyar shi.

Dafa mishi baya aka yi da sauri ya d'ago kanshi tare da juyo wa ya kalli Yah sadeeq murmishin yak'e ya saki sam ya kasa kallon shi idanun shi na kan hannun sadeeq da ya yake rik'e da hannun mufidah daurewa kawai yake amman ji yake kamar ya d'ora hannu amai yana xunduma ihu ko yaji sassaucin abin da yake cikin xuciyar shi.

A hankali sadeeq ya cika hannun mufidah tare da rungume d'an uwan shi a jikin cikin wata irin soyayyar en uwantaka ta jini, lokaci d'aya idanun su ya ciko da hawaye, amman musaddiq ya had'iye kukan nashi shi kuwa sadeeq sai da hawayen shi suka xubo sakin shi musaddiq yayi tare da rik'e kafad'un shi yana girgixa kai alamar kada Yayi kuka cikin rawar murya yace

" ka barni nayi musaddiq bana son rabu wa da kai ko na second ne balle tsawon kwanaki xamu d'auka batare da ganin juna ba sai dai jin murya a waya"

Hannun shi musaddiq yasa a fuskar sadeeq yana goge mishi hawayen da suke xuba da 'yantsun shi, cikin rawar murya musaddiq ya bud'e baki yace

"Calm down Yah sadeeq kukan ka yana k'ara karyar min da gwiwar tafia, idan kana son ganina xaka iya xuwa inda nake nima idan na samu hutu xan na xuwa insha Allah ka taya ni da addu'a"

K'ara rungume junan su suka yi gaba d'aya sun bawa daddy, mumy, Dr muh'd da mufidah tausayi sosai, har sai da mufidah ta yi hawayen tausayin su musaddiq yana kula da yanda take fitar da hawayen sam baya son ganin hawaye a fuskar ta hkan ba k'aramin rikita shi yake ba, bai san lokacin da ya sanya hannu a aljihun black jeans d'in shi ya d'auko wani kyakkyawan hankacif ya mik'a mata ba tare da ya kalle ta ba ko yayi mata magana.

Babu wanda ya kula da hkan sai Dr muh'd, ita ma mufidah bata san lokacin da ta mik'a hannu ta kar6a ba don hankacif d'in ya birge ta pink colour ne da adon white flower's a jiki sai tashin k'amshin turaren shi yake mai matuk'ar dad'i.

A fuskar ta tasa tare da shak'ar k'amshin saboda dad'in shi sai da ta lumshe idanun ta kafin ta goge hawayen fuskar ta ta, wani tunani ta fara yi kafin kuma ta tuna ita matar aure ce a yanxu da gaggawa ta kauda tunanin tare da yin astagafrullah a cikin xuciyar ta.

Ganin mutane sun fara shiga jirgin ne yasa daddy yace " musaddiq lokaci fa yayi a hak'ura hka da sallamar"

Cikin sanyin jiki ya cika sadeeq tare da juyawa don su yi sallama da muh'd aikuwa sadeeq ya k'ara sa hannu ya rik'e shi gam, kallon shi daddy yayi tare da cewa

"Kae sadeeq cika shi mana kada ka 6ata mishi lokaci"
Dak'yar sadeeq ya cika musaddiq ya rungume muh'd sannan suka k'ara yin sallama da iyayen shi har yayi taku na biyu xai yi na uku yaji sanyayyiyar muryar mufidah tana cewa

"Allah ya kiyaye hanya malam"
Ko juyo wa bai yi ba yayi gaba don yanda yake xuciyar shi tayi rauni da yawa, suna kallon shi har ya fara tattaka matattakalar jirgin dai dai yaxo xai shige cikin jirgin ya jiyo ya kalli iyayen shi da d'an uwan shi tare da abokin shi aminin shi bai kalli wajen mufidah ba ya d'aga musu hannu tare da shige wa cikin jirgin da sauri kada xuciyar shi ta karaya Yayi kuka.

Dukannin su jiki a sanyaye har sai da jirgin tashi suka daina ganin shi sannan suka shiga mota sai gida, har suka k'arasa gida babu mai magana a cikin su saboda kewar musaddiq duk ta dame su.

Tun a hanya Dr muh'd ya wuce gida don baxai iya k'arasa wa ba tun da babu aminin shi, daddy da mumy ma part d'in su suka shige, hka mufidah ta kama hannun sadeeq suka wuce part d'in su don bata son su takura wa su mumy tun da weekend ne.

Suna shiga part d'in su sadeeq ya xame hannun shi daga na mufidah ya shige bedroom d'in shi da kallon mamaki mufidah ta bishi da kallo, ta6e bakin ta tayi tare da xama a kan kujera shiru tayi na en mintuna tana tunani kafin kuma ta tashi ta shige bedroom d'in ta mayafin da tayi rolling d'in kanta dashi ta cire ta ajiye tare da hankacif d'in da musaddiq ya bata, cire gown d'in jikin ta tayi tare da d'aura towel ta shige toilet.
Chapter 16 · 0% Book details