← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 54

Sashe 17

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin en mintuna tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata er riga iyakar ta gwiwar purple colour mai k'aramin hannu, light make up tayi tare da gyara gashin kanta batasa ribbon ba ta sake shi hka a bayan ta sai tashin k'amshi mai dad'i gashin yake, different perfumes and body spray's xuwa humra tayi amfani dasu a jikin ta sannan ta xura flate shoe bak'i ta nufi bedroom d'in sadeeq da sallama a bakin ta ta shiga d'akin.

Cikin nutsuwa ya d'ago kanshi ya kalle ta k'okarin amsa sallamar yake amman ya kasa saboda ganin mufidah da yayi da wannan shigar tun da suke bata ta6a yi mishi irin wannan shigar ba, kafin ya ankara yaji ta xauna akan kafafun shi ta sanya hannun ta a kafad'ar shi ta rik'e d'ayan hannun kuma ta rufe mishi baki ganin yanda ya bud'e yana bin ta da kallo.

"Wannan bud'e bakin fa?"
Dariya suka sa lokaci kafin ya k'ara rungume ta ajikin shi cikin kunnen ta ya fad'a mata cewa
"Bud'e bakin kallon ki ne my wife kinyi kyau sosai"

Murmishi tayi tana mai sunkuyar da kanta a hankali ya fara gwada mata salon soyayyar shi mai sanyi, ita ma mufida ta biye shi don tana so ta mantar dashi damuwar da yake ciki, bayan komai ya kammala ne bacci mai dad'i ya d'auke su rungume da junan.............

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ *E.W.F*

_ina kuke Ummiey Xeey dear and Aishan umma dear wannan shafin na ku ne kyauta, ina matuk'ar alfahari da ku Allah ya bar xumunci a tsakanin mu_❤

*PAGE 21*

Sam musaddiq bai kula da mufidah ba har ya xauna a kusa da kujerar daddy, tea d'in da mumy ta had'a musu ta ajiye yasa hannu ya d'auka a hankali ya fara shan tea d'in, cikin wata siririyar murya mufidah ta bud'e baki tace

"Ina k'wana musaddiq?"
A matuk'ar rikice ya d'ago kanshi ya kalli inda take, had'a ido suka yi yayin da kuma lokaci d'aya ya furzar da tea d'in da yake bakin shi ya kware sosai amman still idanun shi na kanta, da sauri daddy, mumy, sadeeq tare da muh'd suke yi mishi sannu yayin da mufidah ta d'auki glass cup ta cika shi da ruwa mara sanyi ta mik'a mishi tana cewa
"Sannu fah"

Da sauri mumy tasa hannu ta kar6i cup d'in hannun mufida ta sa wa musaddiq a baki, kad'an ya iya sha ya cire cup d'in a baki tare da tashi da sauri ya bar wajen, muh'd ma ya juya ya kalli su daddy yace

"Daddy xamu je mu fara shirya shiryen tafiar musaddiq don nan da k'wana biyu xai tafi"

Cikin matuk'ar mamaki sadeeq yace "ina musaddiq d'in xai je?"

Shiru muh'd yayi ganin hka yasa daddy yace"muh'd je ka xan yiwa sadeeq bayanin komai"

"Toh daddy"

Yana gama fad'in hka ya fice daga palon yabi bayan musaddiq, daddy kuwa nan yayi wa sadeeq bayanin karatu musaddiq xai je ya k'aro, nan fah sadeeq ya tubure lallai sai musaddiq ya hak'ura da tafia yayi anan nigeria ko kuma ya tattara ya bishi can ko kuma ya hak'ura gaba d'aya da karatun don sam baya son yin nesa da d'an uwan shi.

Nan fa daddy da mumy suka fara rarrashin shi, mufida kuwa ido ta xuba musu kawai tana kallon su don bata da abin cewa, dak'yar suka shawo kan sadeeq ya amince da tafiyar musaddiq ba don ranshi ya so ba don gaba d'aya baya k'aunar yin nesa da d'an uwan shi, yana mishi wani irin so da baxai kwatantu ba.

Mumy ce ta kalli mufidah wadda ta kula gaba d'aya a takura take dasu tace " 'yata tashi kije ki huta kin ji"

Sunkuyar da kai tayi cikin kunya tace " toh mumy"

Kallon sadeeq mumy tayi tare da cewa " ka bita ku tafi tare, idan kuna buk'atar wani abin ka kirawo ni a waya ka sanar da ni"

" okay mumy"

Daga hka suka mik'e tare da tafiya part d'in su, da kallo mumy ta bisu kafin sai da suka 6acewa ganin ta tukunna ta sauke idanun ta tare da sauke ajiyar xuciya, kallon ta daddy yayi tare da cewa

" Ya akayi mumyn sadeeq?"
Girgixa kai tayi tare da cewa " ba komai "

" ina son ki cire sa damuwa a cikin ranki game da tafiyar musaddiq, insha Allah babu abin da xai faru dashi addu'a xaki nayi mishi"

" toh daddy xan yi yanda kace"
Ta fad'a tana Murmishi, shima daddyn cikin murmishi yace "yawwa tawan hka nake son ji"

Daga hka suka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali, amman mumy xuciyar ta tana tunanin yanxu Wanne hali musaddiq yake ciki gaba d'aya ta matsu da ya tafi ko xuciyar ta ta samu sukuni don bata son suna had'u wa da mufidah.

Bayan sun k'arasa part d'in su mufidah bedroom ta shige don ta samu bacci, idanun ta har wani xafi yake saboda baccin da take ji, kwanciya tayi tare da k'ara k'arfin ac dake d'akin, shima sadeeq ganin hka yasa ya bita bedroom d'in kwanciya yayi tare da janyo ta jikin shi ya rungume ta ba dad'e wa bacci yayi awon gaba dasu gaba d'aya.

Musaddiq kuwa tun lokacin da ya fice daga palon da sauri wajen parking space ya k'arasa motar Dr muh'd ya shige ya xauna tare da had'a kai da gwiwa hannun shi dukka biyun kuma suna saman kanshi yana yamutsa gashin kanshi, idanun shi sunyi ja sosae, a lokacin idan ka ga musaddiq sai kayi mishi kukan tausayi gaskia so masifa ne idan baka yi dace ba da yasan hka son mufidah xai mayar dashi da bai yi saken da xai rasa ta ba a rayuwar shi.

Yana cikin wannan halin ne muh'd ya k'araso wajen har ya shiga cikin motar ya xauna musaddiq baisan ya shigo ba, girgixa kai yayi cike da tausayin musaddiq yasa hannun shi ya dafa kafad'ar shi d'ago jajayen idanun shi yayi ya watsa su akan muh'd wanda yasa sai da gaban muh'd ya fad'i ganin yanda musaddiq ya koma, cikin rarrashi muh'd yace

"Haba musaddiq kai fa kayi alkawarin cire son mufidah a cikin xuciyar ka, gashi idan kana irin hka daddy da yah sadeeq xasu d'ago ka fa, don nasan mumy ta gama fahimtar komai magana ce kawai bata yi ba"

Shiru shi dai musaddiq Yayi amman yana sauraren abin da muh'd yake fad'a mishi, sai da suka 6ata lokaci sosai muh'd yana rarrashin musaddiq har ya samu ya dawo dai dai tukunna suka tafi inda xasu je.

A cikin wad'annan kwanakin biyu musaddiq babu abin da yake sai shirye shiryen tafiar shi duk wani shiri ya gama sai jiran ranar tafia kawai yake jira, sadeeq ya shiga damuwa sosai na tafiyar musaddiq amman mufidah da mumy suna k'okari wajen lalla6a shi har dai ya d'an kwantar da hankalin shi.

Tun daga ranar musaddiq bai k'ara had'u wa da mufidah ba kuma shi kanshi yaji dad'in hka don baya son ganin ta don ba k'aramin d'aga mishi hankali ganin ta yake ba.

A yau Saturday ne da yammacin ranar K'arfe 5 na yamman jirgin da xai je Australia xai tashi, don hka musaddiq xuwa hud'u na yammacin ranar ya kammala komai, fito wa yayi daga bedroom d'in shi xuwa palon mumy don su yi sallama yana shiga palon ya tarar da sadeeq da daddy a tsaye suna jiran shi don yi mishi rakiya.

Rungume daddy yayi idanun shi sun cicciko da hawaye peck ya bawa daddy a kumatun shi tukunna ya cika shi suka rungume junan su da sadeeq kowanne idanun shi cike da hawaye, d'ago kan da xai yi suka sauka akan mufidah tana murmishin da yake k'ara mata kyau tayi kyau cikin wata Arabian gown blue colour tayi rolling d'in kanta da red d'in veil ba k'aramin kyau tayi ba lips d'inta yasha red d'in jambaki, wani irin abu ne ya tsayawa musaddiq a xuciyar shi da sauri ya kawar da kanshi daga kallon ta yana k'okarin danne abin da yake ji.

Sakin sadeeq yayi tare da k'arasa wa wajen mumy wadda ta sakko daga up stairs da shirin ta na rakiyar musaddiq airport, rungume ta ita ma yayi sosai mumy ta tsorata da yanda taji bugun xuciyar musaddiq, hannun ta tasa ta shafa kanshi tare da rad'a mishi a kunnen shi

"Ka dage da addu'a musaddiq Allah ya yaye maka abin da yake damun ka, nima xan dunga you maka, kada kana sa damuwa a cikin xuciyar ka don Allah kayi min wannan alkawarin"

D'aga kai yayi tare da cewa " xan yi abin da kika ce mumy nah"

Daga hka kuma suka d'unguma don tafiya airport rakiyar musaddiq ko inda mufidah take bai k'ara marmarin kallo ba, sosai mufida abin da yake mata yana d'aure mata kai xai yi magana da kowa ban da ita ko gaida shi tayi baya amsa wa, amman da ta tuna er tsamar da suke yi a skul maybe har yanxu bai hak'ura ba ta6e baki tayi, hannun ta sadeeq ya kama suka fita daga palon da yake duk sun riga su yin gaba.....................

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

*PAGE 23*

Tun lokacin da musaddiq ya tafi xuciyar mumy ta kasa samun nutsuwa saboda batasan halin da d'anta yake ciki ba, idan suka kirawo shi a waya muryar shi normal, but ae ba fah ta ganin shi batasan yanayin da yake ciki ba, ta dage da taya shi addu'a sosai, hka a 6angaren daddy da shima addu'ar yake taya musaddiq tare da Kiran shi a waya yana mishi nasiha cikin tausasawa da rarrashi, duk wata kulawa suna yi mishi ta waya.

Sadeeq kuwa bayan en kwanaki da tafiyar musaddiq ya cire damuwar rashin d'an uwan nashi a kusa dashi, don yana samun kulawa sosai a wajen matar shi mufidah, xaman su suke lafia cikin kwanciyar hankali, duk da sadeeq yana da sanyin hali a komai nashi daga kallon yanayin shi kasan bashi da xafi komai cikin sanyi yake shi yasa suke xaman su lafia ba mai jin Kansu.
Chapter 17 · 0% Book details