← Book details Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 54

Sashe 25

Yayi Sake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin mufidah ta rik'e makarar k'am tana cewa " bai fa mutu ba yayi min alkawarin xamu rayu da juna ku dawo da shi"
Kuka take sosai tana sumbatu kamar mai ta6in hankali dak'yar mumy da umma suka janye ta aikuwa suna sakin ta ta xura da gudu ta kuma rik'e makarar tana surutai sosai ta bawa mutanen wajen tausayi don koma wa tayi kamar wata mahaukaciya sabon shiga.

Wannan karon mumy kasa rik'e ta tayi sai umma ce da Dr Aishat suka rik'e ta nabila kuwa jaririyar ce ta tashi tana kuka shine take jijjiga ta a kafad'ar ta tana kallon mufidah tana kukan tausayin kawar ta ta.

Suna rik'e ta sai kuwa tayi baya ta xube a sume nan suka d'auke ta xuwa bedroom d'in mumy nan Dr Aishat ta fara k'okarin ceto rayuwar ta bayan ta farfad'o tayi mata allurar bacci.

Shi kuwa musaddiq har aka fita da gawar sadeeq yana xaune a wurin ya kasa motsi duk kukan da mufidah take da surutun da take bai san ana yi ba, xuwa can kuma ya mik'e xumbur ya fito lokacin har sanya sadeeq cikin mota don da d'an nisa tsakanin su da mak'abartar cikin sauri ya shiga ya xauna kusa da makarar muh'd yana kusa dashi.

Lokacin da aka sanya sadeeq cikin kabari daddy ne da musaddiq suka sanya shi a cikin an fara xuba k'asa akan shi sai lokacin musaddiq ya dawo cikin hayyacin shi sai gani akayi kawai ya xube saman kabarin a sume nan aka d'auke shi aka sanya shi a mota aka nufi gida dashi don bashi taimakon gaggawa.

Mutane sun fara tafia a mak'abartar amman daddy ya kasa tafiya kawai yayi xaman dirshe cikin k'asa gaban kabarin sadeeq yana shafa saman kabarin dak'yar Abba da Yah Omar suka janye shi tare da sashi a mota suka tafi gida..........

Aishat A muh'd ✍🏻
[13/11, 2:04 p.m.] Aysher Muhd Writr: 🌲 *YAYI SAKE!*🌲

*Written by*

Aishat A muh'd

♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM

*PAGE 32*

Bayan sun dawo gida Dr muh'd allurar bacci yayi wa musaddiq bayan ya farfad'o daga suman da yayi, tukunna ya fito xuwa farfajiyar gidan inda su daddy suke kar6ar ta'axiyya, gefe d'aya ya samu ya xauna yana aikin tunani lallai rai ba'a abakin komai yake ba lokacin da Allah yaso kar6ar abin shi ba wanda ya isa ya hana kamar d'axu ne da safe suka gama shan hira da sadeeq yanxu kuwa baya nan ya tafi tafiyar da har abadan baxai sake jinshi ko ganin shi ba a duniyar wayyo rayuwa Allah yasa mu dace Allah Yayi mana kyakkyawan k'arshe Ameeen, tunanin da muh'd yake yi kawai idanun shi suna hasko mishi fuskar sadeeq kunnuwan shi suna jiyo mishi muryar sadeeq lokaci d'aya hawaye masu xafin gaske suka xubo mishi.

Damuwar da muh'd ya shiga sai kace wani d'an uwan shi shak'i k'in shi ya rasu, Allah ne ya had'a su da musaddiq har suka yi mugun sabo har suka rikid'e suka koma aminan juna na sosai da sosai k'aunar su yake da xuciya d'aya son su yake so irin mara algus d'in nan a ciki, wad'annan tunanin yake har xuwa lokacin da aka kirawo sallahr axahar suka tafi masallaci.

A6angaren su mumy kuwa abin dai sai du'a'i don ko magana bata iya yi a yanxu ta daina kuka sai na xuci idanun ta sun ja sosai tana xaune cikin bedroom d'in ta akan abin sallah tana rik'e da carbi tana addu'a bayan ta idar da sallah, addu'ar samun dace da rahmar ubangiji take yiwa sadeeq tana fatan d'anta ya dace da albarkatun da suke wannan ranar ta alhamis, tana matuk'ar k'aunar 'ya'yan bata son abin da xai ta6a mata su sai gashi mutuwa mai yankan kauna ta raba rabuwa ta har abada shikenan baxa ta kara ganin sadeeq d'in ta ba, mutuwa kenan mai raba d'a da mahaifiyar shi.

Nabila kuwa tana tare da mufidah duk da har yanxu bacci take bata farka ba, jaririyar ma tayi bacci ta kwantar da ita bayan ta gama d'ura mata madarar jarirai, kallon k'awar ta take tana mai tausayin ta mutuwar miji babu dad'i ko dad'e wa basu yi don basu fi shekara biyu da aure ba suna kan ganiyar cin soyayyar su sai gashi mutuwa taxo ta raba hawaye ne suke xuba sosai a idanun ta na tausayin mufidah.

Sai da dare allurar baccin ta saki mufidah lokacin da ta bud'e idanun ta ta ganta a d'akin mumy a lokacin komai ya dawo mata cikin kwakwalwar ta hawaye ne suke xuba a idanun ta jin abin take kamar a mafarki wai sadeeq ya mutu anya ba tsokanar ta suke ba, kuma ae ta ganshi acikin makara har aka d'auke shi aka fita dashi da gaske ne sadeeq ya tafi ya barki da 'yarshi, wayyo sadeeq me yasa ka tafi ka barmu a lokacin da nafi buk'atar ka ni da 'yarka Allah ka jik'an sadeeq d'ina ka gafarta mishi.

Tana cikin hka nabila ta ankara da ta tashi don hka nan ta dunga rarrashin ta da nasiha akan tayi hak'uri ta yarda da kaddara Allah ya kaddara sadeeq lokacin Yayi addu'ar samun rahmar ubangiji xata na mishi abin da yafi bukata kenan.

Dak'yar ta lalla6a ta ta watsa ruwa duk idanun nan sun kumbura sun kod'e saboda tsabar xubar hawaye wata simple gown nabilah ta d'auko ta bata ta saka tukunna ta rama sallolin da ake bin ta, k'ememe mufidah tak'i cin abinci sai da nabilah da umma suka takura mata tukunna tasha tea cikin cup d'aya ba don taso ba duk bakin ta babu dad'i, sai lokacin nabilah ta mik'o mata jaririyar don ta shayar da ita an yi mata wankan ta fes an sanya kayan ta tayi tsab idanun nan nata a bud'e gaba d'aya sai kalle kalle take abin ta.

Kura mata ido mufidah tayi sai taga ta koma kamannin sadeeq tsab, kallon ta take idanun ta suna xubar hawaye suna d'isa a fuskar jaririyar cikin raunin murya da sanyi tace
" kin ga baban ki ya tafi ya bar mu da kewar shi tafiya ta har abada kinxo duniyar shi kuma yana barin ta gaba d'aya, bakisan baban ki ba kuma baxa ki ta6a ganin shi ba har abada sai a photo ya tafi wajen da ba'a dawowa idan aka tafi mahaifin ki mutumin kirki ne sosai babu ruwan shi yana son ki tun kafin kixo duniyar nasan har mutuwa ta d'auke shi bai gan ki ba kuma ganin ki shine burin shi na k'arshe kuma....."

Toshe mata bakin ta nabilah tayi ganin maganar tayi yawa kuma bata da alamar tsayawa, tana kuka tace " haba mufidah ki daina irin wad'annan maganganun ita me ta sani da xaki sata a gaba kina surutu nace miki a yanxu soyayyar da xaki nuna wa sadeeq ita ce addu'ar na rok'e ki kiyi shiru kina karyar min da xuciya"

Wani murmishin yak'e mufidah tayi idanun nan har yanxu hawaye ne suke xuba kafin ta ce " nabilah baki san abin da nake ji bane da kinsani da....."

Da sauri nabilah ta katse ta tare da cewa " nasan da hka mufidah amman kiyi addu'a xaki ji sauk'in koma mene"

Daga hka suka yi shiru mufidah tana shayar da babyn ta ta kura mata ido tayi tana kallon ta xuciyar ta cike da tausayin Kansu don tasan sun yi rashi ba kad'an ba.

Musaddiq kuwa shima acikin daren ya farka lokacin da ya tashi Dr muh'd yana xaune a sofa ya buga tagumi, d'ago kanshi yayi suka had'a ido da musaddiq da sauri ya sanya hannun shi ya goge hawayen fuskar shi tare da tashi ya matsa kusa da musaddiq yana cewa
"Sannu musaddiq ka tashi, me yake damun ka yanxu ba inda yake maka ciwo?"
Muh'd ya jero wa musaddiq duk wad'annan tambayoyin cikin muryar shi mai rawa, kallon shi musaddiq kawai yake ba tare da yayi mishi magana ba, kallon da yake mishi kamar yau ya ta6a ganin shi har muh'd ya tsorata da irin kallon da yake mishi, hannun shi yasa ya ta6a shi amman ko motsi bai yi ba kuma yak'i dai na kallon shi rasa me xaice mishi yayi kawai ya samu waje ya xauna kusa dashi.

Xuwa can sai yaga ya tashi xumbur ya mik'e ya shige toilet bin bayan shi da kallo muh'd yayi yana girgixa kanshi wasu kwalla suna xubo mishi tausayin musaddiq, mufidah, mumy da daddy yake yi sosai.

Musaddiq yana shiga toilet ya cire kayan jikin shi ya sakarwa kanshi shower kafin kuma ya tsugunna a wajen yana wani irin kuka mai ban tausayi ga ruwa mai sanyi yana xuba a jikin shi ya rasa me yake mishi dad'i da gaske ne ashe Yah sadeeq ya mutu ya barshi shi kad'ai ba wa ba k'ani shi d'aya tilo wajen su mumy ta ina xai ji dad'in rayuwa babu d'an uwa rabin jikin shi, kuka sosai ya shashi a toilet kafin ya kashe shower d'in ya d'aura alwala ya fito.

A tsaye ya tarar da muh'd sai safa da marwa yake don baisan a wane yanayi musaddiq yake acikin toilet d'in da tuni ya shiga saboda mugun dad'ewar da Yayi a ciki da kallo muh'd ya bishi ganin ya xura jallabiya ya fara rama sallolin da ake bin shi.

Bayan ya idar ne muh'd yayi dashi don yaci abinci amman ko magana bai yi mishi dole hka ya hak'ura ya barshi yana kallon shi ganin yanda ya had'a kai da gwiwa.
Chapter 25 · 0% Book details