← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 52

Sashe 9

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin ma yayi magana sai ita ta ɗago kai a fusace kasancewar ganin wata kyakkyawar yarinya da yake kallo a jikin wayan, wanda hakan ne ya ɗauke mishi hankali har bai san da zuwanta wajen ba. Hakan yasa zuciyarta tayi baƙi nan da nan fushi da kishi suka bayyana a kan fuskarta, inda ta kalle shi cikin wani irin yanayi tace, "What is this Malik? Who is this girl? What is your connection with her?"

Ɗan waro idanusa yayi yana mata kallon mamaki, ba tare da ya amsa mata tambayoyin nata ba kuma sai ya ɗauke kanshi yana sake haɗe rai sosai

Hakan ya sake fusata ta cikin tsawa da ɗaga murya ta sake cewa, "Malik, are you talking to you and keeping me quiet? I said who is this girl? Ka bani amsa idan ba haka ba wlh zan yi abin da zaka yi dana-sanin sani na."

"Kiyi abun da za ki iya kinji ko? And bazan faɗa ko wace ce ba, dalla bani wayana."

"Bazan bayar ba." Tayi maganar cikin tsiwa still a fusace wadda har ƙwalla sun cika mata idanu

Shima a fusacen a yanzu yace, "Ke Nawwara ba na wasa da ke, i said give me the phone or..."

Ta katse shi da sauri cikin muryan kuka da cewa, "wato amanata kake ci ko? Wlh tallahi ba ka isa ba Malik, baka isa ka wulaƙanta Ni ba, kayi kaɗan." Ta ƙare maganar cikin buɗe mishi idanu wadda a lokaci ɗaya ta fashe da kuka cikin ƙunan rai da ke nuni da tsantsan kishinta

A dai-dai lokacin ne wani saurayi Black beauty ya iso wajen, tare da faɗin, "wai me ke faruwa ne a nan?"

Dalilin da yasa Malik ya kasa yin magana kenan ya bi saurayin da kallo suna haɗa idanu

Yayinda shi kuma saurayin ya mayar da idanunsa a kan Nawwara da ke faman kuka kamar wacce ranta zai fita, nan da nan har ta ɓata fuskarta da kwalliyan da ta caɓa. Kafin yayi mata magana har ta wurga wayan a jikin Malik ta ruga da gudu tana kuka sosai

Da kallo suka bi ta har ta ƙulewa ganinsu. Inda Malik ya ja tsaki yana ɗauke kanshi ya mayar a kan wayan da ke jikinsa ya ɗauka

While shi kuma saurayin sai ya taho ya zauna a saman carpet da ke shimfiɗe a wurin an jera drinks a sama. Zaman shi ya bi Malik da kallo yana cewa, "me kayi mata ka taɓo ta haka?"

"Me kuwa nayi mata? Shirmen kishin ta take so ta nuna min haukansa a nan."

Murmushi yayi yace, "Allah ko? Ni dai na san da abun da kayi mata shiyasa ka motsa mata, please tall me what did you do to her?"

Ɗago kai Malik yayi ya kalle shi, sai ya ɗauke kanshi yana mayarwa a saman wayansa tare da duban hoton budurwan da ke jiki, bai san sanda murmushi ya suɓuce mishi ba yana faman shafa kan wayan a hankali

Ganin haka ne yasa Abokin nashi ya amshi wayan yana dubawa shima. Arba da yayi da kyakykyawar halittar da ke gaban wayan, sai ya ɗago kai da sauri yana duban sa tare da faɗin, "wace ce wannan kuma?" Ya ƙare maganar yana sake duban wayan

Shi kuma Malik yalwataccen murmushin ne ya sake suɓuce mishi, sai da ya kai hannu ya shafa ƙasumban shi kafin yace, "I don't know her."

"Kamar ya?" Ya furta yana kallon sa

Numfashi ya sauke yana ɗan cije leɓen ƙasan bakinsa. Sai da ya fuskance shi before yace, "Sinior ita ce yarinyar da ta hana Ni sukuni a tsakankanin wannan lokacin."

"You mean. Ita ce wacce ta sanya ka a cikin wannan halin da kake ciki?"

Gyaɗa mishi kai yayi

Sai shi kuma Sinior yayi murmushi tare da cewa, "cab ɗijam! Kace ka taro match ne ba ka da ƴan wasa, ai dole Nawwara ta tashi hankalin ta ashe ta kama ka kana kallon wata ce, amma ya aka yi ban sanka da ita ba? Duk a cikin ƴan matan ka ban taɓa ganin kyakkyawa irin wannan ba, Guy aina ka samo ta domin ta haɗu wlh babu ƙarya?"

"Ban santa ba nace maka, yanda ka ga hoton ta haka nima nake gani kullum, kuma a haka ne ta sanya ni a cikin wannan halin."

"Wai ban gane ba fa, me kake nufi?"

"Sinior I don't know her, nima tsintan hotonta nayi a facebook, wani ne yayi post a page na Arewa show. Tunda naga hoton wlh na susuce hankali na ya tashi, bani da buri sama da in Yi tozali da ita, amma abun ya faskara, yau tsawon sati biyu kenan na rasa sukunina na kasa cire ta a raina bare in manta ta, hasali ma ko sunanta ban sani ba, na bibiyi wanda yayi post ɗin but shima yace min bai santa ba, ya tsinci hoton ta ne shima yayi post a page ɗin." Sai ya ja wani dogon numfashi mai fita da huci, a hankali kuma ya ci gaba da cewa, "Sinior na kusa na rasa hankali na gaba ɗaya idan ban samu yarinyar nan ba, zan mutu wlh, bani da buri face in ganta in bayyana mata irin tarin ƙaunar da nake mata ba, wlh ban taɓa son ɗiya mace makamanciyar yanda nake mata ba, kai ko kwatan-kwata ban taɓa yiwa wata halitta ba kamar yanda nake jin nata soyayyar a zuciyata ba."

Da kallo kawai Sinior yake bin shi dashi ba tare da yayi yunƙurin katse shi daga zantukan shi ba, haƙiƙanin gaskiya yake gani tsagwaronta a cikin idanunsa, wanda ya san waye Malik ciki da bai kuma ya san tabbas da gaske yake yi, babu shakka ko shi da ya kalli hoton yarinyar ya ji matsananciyar soyayyarta domin ita ɗin abun burgewa ne ga kowa, sai dai me, babu halin ya bayyana nashi soyayyar sabida Abokinsa ya riga shi. Numfashi ya ja shima yana mayar mishi da wayan nashi tare da cewa, "yanzu kana nufin duk tarin ƙaunar da kake yiwa Nawwara bai kai na wannan yarinyar da ba ka san wace ce ita ba?"

"Bazan ɓoye maka ba ka san hali na Sinior, wlh da gaske nake maka ban taɓa jin irin soyayyar da nake mata a kan wata Mace ba, Ni kaina ina mamakin yanda zuciyata ta haukace da tunaninta, komai ba na iya yi yanzu sai da tunanin ta, wlh Sinior idan har zan samu yarinyar nan zan iya bada komai nawa domin in mallake ta, Ina sonta da gaskiya, kuma son da nake mata ba irin na sauran Mata da nake musu ba ne." Sai kuma ya fuskance shi sosai tare da ƙara faɗin, "wlh idan har zan samu yarinyar aurenta zan yi domin in killace ta a gidana, amma ban san ya zan yi ba, ban san ta inda zan fara ba."

Jinjina kanshi Sinior yayi tare da faɗin, "lallai kam Malik, kana da babban aiki a gaban ka, ba wai nemo yarinyar da ba ka san inda za ka neme ta ba, a'a; matsalar yana ga wurin Nawwara, yarinyar da ka koya mata soyayyarka tun bata san kanta ba, yarinyar da ta so ka a rayuwarta ba ta jin maganar kowa sai kai, yarinyar da ta mallaka maka komai nata, yarinyar da ta fitsare jikinta duk saboda kai ta koma yanda take a yanzu, to ya zaka yi da ita? Da wanne ido za ka kalle ta? Ka san halin Nawwara ba sai na ba ka labari ba, a kanka zata iya kashe ko waye ne sai dai itama a kashe ta, ta sha yin dambe duk a saboda kai, ta sha zuwa cell duk a sabida kai, ta koma tamkar Matarka duk don ta faranta maka rai, sannan kai ma kayi mata alƙawari ba sau ɗaya ba; ba sau biyu ba a rayuwa, to ya za ka yi da ita?"

Shiru kawai Malik yayi yana kallon Sinior yayinda ya kasa cewa uffan

Sai shi Siniorn ya sake cewa, "kaga Malik idan ma mafarki kake yi to ka farka daga wannan barcin, duk da naga hoton yarinyar nan na san cewa ta fi Nawwara komai, bama za'a haɗa su ba idan kyawu ne, amma ba ka san inda take ba, ba ka san ta ina za ka fara nemanta ba, ba ka san cewa tana raye ko ba ta raye ba, to; ta ya zaka soma sonta bayan ba ka da hanyar da zaka iya nemanta? ba ka da wani takamaiman hanya ɗaya mai sauƙi da zai kaika gare ta, Malik ka dawo hayyacinka tun kafin ta shiga tsakanin ka da Nawwara, kaima abun da bazai taɓa faruwa bane."

Malik yace, "na ji abun da kace, but ka sani wannan issues ne na rayuwata, soyayyata ne na gaskiya, bazai taɓa yiwuwa in cire abun da nake ji a game da yarinyar nan ba, ba Ni na sakawa kaina ba taya ya zan cire?"

"Akwai hanyoyi da dama da za ka iya bi ka cire ta."

"Which way is it?" Malik ya tambaye sa yana zura mishi idanu

Sai yayi murmushi shi kuma yana cewa, "na farko dai na tabbata soyayyar yarinyar nan abu ɗaya zuwa biyu yasa ka kamu da ita, na farko kyawunta, Ni na tabbata kyawunta da sha'awarta yake ruɗanka Malik, baya ga haka babu komai Malik, kuma idan kayi yaƙi da zuciyarka ka nuna mata wannan ba irin Matan da kake samu cikin sauƙi bane zata fahimta, wannan baka santa ba, ba ka da tabbaci ma Mutum ce ita ko aljana domin kyawun nata yayi yawa..."

Katse shi yayi da cewa, "yanzu kana nufin ba ka yarda cewa ina sonta har zuciyata bane? Taya kake ganin zan iya bayyana wannan magana alhalin akwai Nawwara a tare da Ni? Meyasa zan janyowa kaina fitina?"

"Shikenan na yarda kana sonta, amma zaka iya cire ta ai, kaga Malik don Allah ka dena wannan maganar ma domin abun da bazai taɓa yiwuwa bane, da ace ka san inda yarinyar nan take to Ni zan iya goya maka baya ka aure ta, sai dai da sharaɗin zaka haɗa su su biyu da Nawwara, amma babu batun ka kawo wata wai kana so alhalin kuna tare da ita."

"Ok." Ya furta yana miƙewa ba tare da ya sake cewa komai ba
Chapter 9 · 0% Book details