Sashe 3
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Shima ɗin kafe ta yayi da idanun yana cije leɓe cike da tsantsan sha'awar ta da ƙaunarta yace, "oh my Besty! Me kike ci na baka na zuba? Ai abun da yasa na kira ki kenan ki ƙariso don in shafa miki labarin abun da yake faruwa... Amma tukunna dai bari in soma hura miki wutan nan don naga time na gudu." Sai yayi saurin ɗaukar kafi-tankiyan ya ajiye sannan ya soma jera itacen a ciki, a haka ya gama ya hura wutan
Ita kuma har ta saka kujera ta zauna suna magana a tsakanin su. Wani almajiri ta kira ta kalli Ibrahim ɗin tare da cewa, "Besty ba shi kuɗi ya ƙaro min icce, don wannan bazai ishe Ni ba."
"Ok nawa kike buƙata?" Yayi maganar yana ɗago kai tare da kallon ta
"Two hundred is ok." Sai ta kalli Yaron tace, "ka siyo min iccen ne na ɗari, sai yajin hamsin."
"To." Yace yana amsar kuɗin a wajen shi
Komai Ibrahim yayi mata hatta da ɗaura mai a wuta, sai da yayi zafi sannan ita ta soma jefa waran tana cewa, "My Besty bani labarin in sha na ƙosa."
Dariya yayi yace, "Arab Sarauniyar son labari! Yanzu kuwa." Sai ya gyara zama a saman bencin da ya ɗauko
Har zai soma maganar kuma sai wani saurayi ya iso wajen yana kiran sunan shi, tare da ba shi hannu suka gaisa, sai ya zauna a kan bencin shima yana kallon Arab tare da cewa, "Ƙin fi ƙarfin Yaro ya ne?"
"Dai-dai Sa'id." Ta amsa shi batare da ta kalle shi ba tana ci gaba da saka awaran
Shi kuma yace, "but yau ba ki fara suya da wuri bane? I think zan zo inga wuri ya cika sai na iske babu kowa, yanzu ma kika fara ai."
Yatsina fuska tayi da cewa, "wlh kuwa. I did not start early."
"Ok. tunda na zo da wuri yau dai na taki Sa'a, za'a ajiye min na ɗari uku ina dawowa, don Allah yanzu ba jimawa zan yi ba kar in dawo inga an cika wurin sai na jira layi."
"Ba ka da matsala, kawo kuɗin sai in ajiye maka."
Sa'id ɗin da ya miƙe sai ya narke fuska yana kallon ta, tare da cewa, "haba Arab sai kace ba ki sanni ba? Zan ba ki mana kar ki damu ki zuba min."
Taɓe baki tayi sai a lokacin itama ta ɗago manyan idanuwanta tare da zuba mishi su tace, "ka san hali na, a kuɗi bani da mutunci ka san da sani, Allah bazan ajiye maka ba idan har ba ka bani kuɗi ba, Ni na dena wannan gangancin."
"Ibrahim ka sanya baki mana, wai kamar bata sanni ba? Yawa ne wannan wlh, kin san hali na nima na san naki, bazan miki wasa da kuɗi ba, don Allah ki ajiye min yanzu babu kuɗin ne a hannu na, kuma idan nace sai na dawo zan siya zan zo in tarar da layi, ƙarshe in rasa, kuma so nake yi in wuce da wuri saboda akwai inda zan je."
Tsaki ta ja da faɗin, "zancen kake so, bani da lokacin ka wlh." Ta mayar da hankalinta a kan abun da take yi bata sake bi ta kanshi ba
Yayinda shi kuma yana ta roƙon ta tare da ce ma Ibrahim, "ya saka baki ta ajiye mishi don Allah, wlh zai bata kuɗin."
"Kaima da tuni ka je duk inda zaka je ka dawo, ka san halin Besty tunda tace baza ta ajiye ba, to; baza ta ajiye bane, ka je ka dawo Ni zan ajiye maka."
"Ok. Shikenan sai na dawo." Yayi maganar yana juyawa zai tafi tare da sanya hannu a aljihu yana zaro wayansa
Sai da ya tafi Arab ɗin tace, "bar ɗan iska, wlh bazan ajiye ba sai ya bani kuɗi, da ma ace ban san halin sa bane."
Dariya Ibrahim yayi yace, "ke ma ba ki da dama Besty a kan kuɗi."
Tura baki tayi tana tsikaro ɗankwalin ta a gaba tace, "Ah to, wa ke wasa da kuɗi? Ai Ni duk inda aka ce kuɗi, to; ba na wasa dashi, a kan kuɗi zan iya yin komai."
"Gaskiya ne Besty." Yafaɗa yana ƙyalƙyale wa da dariya, sai kuma ya sauko ƙasa ya duƙa setting kunnen ta yana raɗa mata, "kamu nayi miki fa, wlh wani babban Alhaji na samo miki me shegen maiƙo."
Waro fararen idanunta tayi da cewa, "kai don Allah? Ba na son wasa fa me sunan Baba?"
"Ah to, wanne wasa zan yi miki? Kin san bamu saba haka ba, wlh da gaske nake miki, irin waɗanda kike so, bari ki ga." Sai ya ciro wayansa ya danna kana ya nuna mata hoton wani ƙaton Mutum tulele wanda da ganin sa ka san ba ƙaramin Mutum bane, kuɗi ya zauna masa sosai, don ma a inda ya ɗauki hoton kana gani ka san waje ne na alfarma
Amsar wayan tayi da sauri tana dubawa
Sai shi kuma ya ci gaba da cewa, "a Abuja yake zaune, amma shi mutumin Bauchi ne, a can iyalan sa suke, ɗan hannu ne wlh sosai, nima ɗan small ne ya haɗa Ni da shi sabida ya san Mutumin, yace wlh ba ƙaramin kuɗi zamu samu a hannun sa ba idan har na tura ki wajen sa, shiyasa da gaggawa na amsa tayin nasa saboda Ni kaina sai da nayi bincike before in zo wajen ki."
Ci je baki tayi tana ɗauke idanunta a kan hoton da ta kafa masa, ta mayar a kan Ibrahim tana cewa, "Ni ba wannan nake son ji ba. Ka tabbatar akwai samu a ciki sosai? Don ka san hali na ba na son harkan ƙaranta."
"Haba tawan, kin san na fi kowa sanin halin ki, akwai nace miki, but kinga mutane sun soma yowa nan, ki bari zamu ƙarisa zancen idan kin koma gida, ko kuma muyi waya kawai."
Baki ta washe cikin farin cikin da ya bayyana a kan kyakkyawar fuskarta tace, "ok. I would also prefer that."
"Yauwa Besty na."
Da haka suka ci gaba da magana suna dariya, yayinda wurin sai cika da jama'a yake yi, duk maza ne manyan samari da magidanta, har da masu kuɗi ƴan hannu zuwa siyan awaran nata suke yi don kawai suyi harƙalla da ita
Nan da nan sai awaran nata ya ƙare ko kiran sallan magriba ba'a kai ga yi ba, shiyasa ta tattara kayanta ta ba wa wani almajiri yayi mata gaba da su, sannan suka tako da Ibrahim zai raka ta gida
Wani saurayi ne a mota ya bi bayan su, ya tsayar da motan a kusa da su yana cewa, "ƴan mata ji mana."
Tsayawa suka yi yayinda suka zuba mishi idanu. Gaba ɗayan su kallon yanayin tsarin zubin motan nashi suke yi tare da hasashen yanayin sa; kuma ba tare da tayi yunƙurin amsa shi ba
Sai ya sakar musu murmushi tare da cewa, "Aboki na ɗan bamu wuri mana, zan yi magana da ƙanwar taka."
Shima murmushin Ibrahim yayi tare da shafa kansa yace, "ok ba damuwa Alhaji." Sai ya kalli Arab yace, "Besty Ni zan wuce gida, zamu yi waya kawai."
"Ok bye." Ta furta cikin yanga tana ɗaga masa yatsu
Bayan wucewan sa ne sai saurayin ya buɗe mata ƙofan mazaunin banza yace, "shigo mana Gimbiyya."
Sai da ta kalle sa ta tura baki cikin jan hankali kana tace, "a nawa?"
Murmushi yayi yace, "duk farashin da kika yanka min Ni na amince."
"But ban yi tunanin da sauƙi hakan ba." Tayi maganar tana kafe shi da kallon ta da ke rikita su
Still murmushin yayi yace, "ai ke ce kin fi ƙarfin hakan, ko dukiyata kika ce in ba ki domin mallakar ki; da gudu zan aikata hakan."
"Allah ko?" Tayi maganar tana zaro ido waje kaɗan mai nuni da mamakin maganar sa, yayinda fuskarta ke ɗauke da shu'umin murmushin ta da ba kowa yake iya gane ma'anar sa ba
"Da gaske, kin wuce haka a wuri na, but na san tsokanata kike yi ke ma kin san da haka, ba Ni ne farkon faɗa miki ba."
"No you were the first to tell me, in your mouth I began to hear, kuma kaga dole in yi shakkar amincewa da kai At the same time, bare yanzu da kidnappers suka yi yawa."
Dariya yayi saboda yanda tayi maganar, cike da burgewa yake kallon ta yace, "haba Princess ban zaci haka a gare ki ba, anyway idan ba ki sanni ba Ni na san ki, cuz na daɗe ina bibiyan ki, kuma ina zuwa wurin nan sosai, but sai dai ba ki taɓa kula dani bane, but idan ma Ni kidnappers ne ai ba laifi bane, a kanki zan iya sace ki idan har hakan zai saka zuciyata ta samu natsuwa."
"Ko?" Tayi maganar tana sake ware mishi kyawawan fararen idanuwanta a kanshi
"Yeah, please ki shigo ba don hali na ba, wlh na ƙosa in ji ki a cikin motata, idan ba haka ba zuciyata zata fashe." Sai ya ɗaura hannun sa a setting zuciyar nasa tare da ƙarisa zancen da cewa, "saboda ba ki ji yanda take bugawa bane, saura ƙiris..." Sai ya cije leɓe yana sake faɗin, "wash Allana!"
Dariya tayi kaɗan cike da jan aji, sai tayi wal da idanunta cike da yanga tace, "afwan kyakykyawar saurayi, bari in shigo."
"Yauwa ko ke fa." Yafaɗa yana washe baki, "wlh bazan iya jure jan ajin nan naki ba, gwara ki taimaka min."
Sai da ta shiga ta zauna before ta juya tana kallon sa da kyakkyawar murmushinta me shiga rai tace, "to kayi haƙuri na ce ai, gani na shigo."
"To amma zan nemi wata alfarma."
"Why not." Tace tana ɗage kafaɗa
"Zan ɗan gyara parking sabida naga kamar a hanya nake."
"Ok ba damuwa."
Sai ya yiwa motan key ya ja zuwa gefe sannan ya faka, tare da juyowa kacokan yana kallon ta cikin tsantsan sha'awa da nuna zalaman sa, inda kyakykyawar murmushin sa ke gudana a kan fuskarsa
While itama yanda yayi tayi, ta zuba mishi narkakkun idanuwanta masu shegen kaifi da ratsa ɓargon Mutum, wanda lokaci ɗaya suke sake zautar da ma'abocin kallon su