← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 52

Sashe 23

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tare suka saki wani numfashi mai ƙarfi, kowannen su yana jin wani irin sha'awa tare da shauƙi yana taso musu

Ta kasa yin magana sabida irin salon da yake mata, sai ta lumshe idanu kawai tana sauraron shi

Hakan da ya gani ne da alamu saƙon shi yana ratsa ta, sai kawai ya dawo kusa da ita tare da ƙara tusa hannun nasa ɗaya a can tsakanin cinyanta yana shafa mata ko ina, inda ɗayan kuma ya zura a riganta cikin salo yake raɗa mata, "Baby mu koma ki kwana min."

Idanuwanta ta buɗe da suke ƙoƙarin sauya kala, sai ta ja numfashi tana cije leɓe a hankali, idanu suka ƙurawa junansu still yana mata yawo da hannayen sa a jikinta, ganin ya kawo baki zai haɗe bakunan su, sai bata hana shi ba ta buɗe bakinta suka soma tsotson juna, lokaci ɗaya suka rikice a cikin motan suna ta jiyar da junan su daɗi

Sun jima a wannan yanayin tamkar baza su rabu ba, kuma ita ta ƙi yarda su koma duk da kuwa tsananin sha'awar da ya sake tayar mata, gaskiya ta kula Tariq na musamman ne, yana da bambanci da sauran Mazan da take mu'amala da su, ya san kan yanda zai tafiyar da ita ta ji daɗi, bata taɓa jin makamancin daɗin da taji a hannun sa ba yau, shiyasa duk jikinta yayi sanyi yanzu ta kasa hana shi ta biye mishi

Tariq yana bin mata shima, sai dai ba kowa ba, ya jima yana wannan ɗabi'ar dalilin da yasa har yanzu bai yi aure ba, shekarun sa yanzu baza su gaza 33 ba, bare yanda yake da jini a jika saurayi mai tashe dole ne zai san kan harkan nan kuma ya san ta yanda zai tafiyar da ita, kuma ya ci nasara don bata yi zaton haka yake ba, ga shi duk da ya gamsar da ita sosai amma kuma sha'awar shi ya ƙi barin ta. Sai da tayi da gaske sannan ta sallame shi ta koma gida.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

       Fannin Malik kuwa tunda suka bar Zaria yake cikin baƙin cikin abun da Nawwara tayi mishi, shiyasa sam ya dena yin mata magana

Tun tana ganin abun da wasa ne a tunaninta zata rarrashe sa but abun ya faskara, har suka gama kwanakin su a Kano suka dawo ya ƙi sakar mata fuska, abu kaɗan faɗa yake mata, ga shi ita tana tsananin ƙaunar shi duk ta ba shi haƙuri amma ya ƙi kula ta, duk yanda tayi ta kasa shawo kansa har suka dawo gida, yawon shaƙatawan da yayi mata alƙawarin zasu wuce before su koma; sai da ta tuna masa but yayi banza da ita

Tunda suka dawo kuma sai duk hankalin sa ya koma tunanin zuwa Zaria, sabida ya san cewa dole a can zai samu yarinyar, duk yanda aka yi Zahra ƴar uwanta ce domin kaman nasu ya ɓaci, yana ji a jikinsa suna da alaƙa da juna, shiyasa yayi baƙin cikin rashin Numbanta, yanzu dole sai ya neme ta, koda ita ya samu ya tabbata dole zai samu yarinyar. A kwana biyun ya kasa samun natsuwa shiyasa ya sanar da Sinior halin da yake ciki, ya nemi shawaran shi saboda ba ya so Nawwara ta san inda zai je yana son komawa Zaria

Sinior yace, "yanzu kai kana nufin a can take kenan?"

"Haka nake tunani Sinior, na tabbata a can take, idan ma ba a can take ba in na gama bincike na in ban same ta ba fine."

"Ok to yanzu taya zamu fara? Ka san Zaria ba ƙaramin gari bane, yana da faɗi, ya zamu yi mu nemo ta?"

Shiru yayi, sai kuma ya ja numfashi before yace, "Ni dai zan riƙa kasancewa a can saboda ko Allah zai bani sa'ar ganin su dukka biyun, domin yanzu ba ita kaɗai nake nema ba, idan har zan samu wannan yarinyar da na gani zan ji daɗi gaskiya, in na bincika basu da alaƙa da juna dole zan ƙulla alaƙa da ita saboda kamannin ta da Babyna."

Dariya kawai Sinior yayi yana kallonsa

While shi kuma yace, "zaka raka Ni zuwa nan da two days sai mu je, ko hoton ta sai in nuna ma mutane wala'alla zamu samu wanda ya santa."

Kafaɗa ya ɗage yace, "Allah ya kaimu."

"Sai dai ba na son Nawwara ta san inda zamu je saboda na santa dole zata zargi wani abun, ka san halin ta."

"Baza ta sani ba, zamu san yanda zamu yi, kaima na kula fushi kake yi da ita, don haka kafin nan yakamata ku shirya ko don kar tayi tunanin wani abun, hakan zai fi."

"Shikenan." Malik ɗin ya furta yana kwanciya a saman gadon shi

Shi kuma Sinior ya tashi yace, "Let me go. We'll call later."

Ok."

Da haka ya fice ya bar shi a ɗakin

Shi kuma ya ci gaba da tunanin sa kamar yanda ya saba, gaba ɗaya tunanin Arab ne a ranshi zuciyar shi har tsinkewa take yi, soyayyarta tayi mishi kamun da bazai iya haƙura da ita ba, take ya fito da wayansa ya lalubo hoton ta ya ci gaba da kallo, sai kuma ya miƙe ya je ya kulle ƙofan sa don ya san zai iya ganin Nawwara at any time ta shigo cikin ɗakin. Nan ya kwanta ya ci gaba da sana'ar kallon hoton Arab wacce tana sanye cikin ƙananan kaya riga da wando, sun yi mata kyau matuƙa kuma sun fito mata da ainihin surar jikinta mai jan hankalin duk wanda ya gani, fuskarta babu kwalliya tana murmushi a hoton, ta sanya facing cap a kanta sai dogayen takalma masu igiya a ƙafafuwanta, tana riƙe da ƙugunta da hannu ɗaya, yanda tayi style ɗin tsayuwarta kanshi abun kallo ne, dole duk wani namiji mai lafiya sai ya susuce a kanta, haka shima Malik ɗin sai da sha'awar sa ya tashi tsaban yanda yake mata kallon ƙurilla, kuma ya kasa denawa sai da ya ga yana shirin fita hayyacin sa duk ya gama susucewa ya rasa yanda zai yi, ƙarshe kiran Nawwara yayi sabida ya samu ya kwantar da sha'awar tasa, idan ba haka ba da matsala, Allah yayi shi mai tsananin sha'awa ne, shiyasa ko ya ya ne idan Mace ta raɓe shi sai ta rikita shi, dalilin da yasa ba ya haƙura da mata kenan, kullum ranan duniya sai ya je club ya samu wacce zai huta, shiyasa idan ya samu Macen da zai huta da ita sai su wuce gidan Sinior, a can yake holewar sa wani lokacin har mata biyu yake ɗauka. Nawwara ce kaɗai yake cin ta a gida tunda ya san ita yar gida ce kuma babu mai saka musu idanu

Mummyn shi ta san irin rayuwar da suke yi but bata taɓa damuwa ba, a ganin ta lokacin su ne sannan kuma da amincewar ita Nawwaran, don haka baza ta shiga tsakanin su ba tunda ta san ita zai aura, su kansu basu san cewa ta gane me suke yi ba idan suka shige ɗaki suka kulle

Ga shi yanzu har Nawwaran ta koyawa Zainab bin Maza, don ta kwaɗaita mata daɗin abun shiyasa itama ta soma, tace mata, "idan ba tayi har yanzu bata waye ba, kallonta zaa riƙa yi tamkar bagidajiya, rayuwar yanzu sai da irin haka sai ana yi ana morewa, idan tace sai ta jira tayi aure ƙarshe baƙin ciki da damuwa zai kashe ta."

Zainab kuma sai ta ɗauki huɗuban ta tayi amfani dashi tana ba wa samarin ta kanta, shiyasa yanzu ko karatun da take yi ba ta zuwa, sai dai ta fita da zummar zuwa makaranta but sai ta ɓuge a ɗakin saurayin ta, tana can suna holewar su, shiyasa ba ta gane komai yanzu don tuni ta jima da dena zuwa makaranta, sai dai idan tana son results mai kyau ta bi Malamai; sai ta ba su kanta sannan su bata result mai kyau, shiyasa sam ba a gane halin da take ciki

Nawwara kaɗai ta sani don ita ce ƙawarta, ita kuma ba ta bin kowanne namiji idan ba Malik ba, shi kaɗai take iya ba shi kanta don shi kaɗai take so, baza ta iya tarayya da kowa ba sai shi, shima dalilin da yake matuƙar sonta kenan.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

       Zahra da Arab ne tafe suna dariya a kan hanya, sun dawo daga wurin Baban su da Inna ta aike su su je su amso mata kifi.
Zahra ke riƙe da kifin don ita aka aika, sai suka haɗu da Arab wacce suke tare da Ibrahim a ƙofar gida, ita kuma tace, "zata raka ta." Shiyasa suka tafi a tare. Bayan sun je sun dawo ne Zahra take bata labarin Nawwara abin da tayi mata; tunda bata san komai ba basu sanar mata ba, kuma after ta dawo time ɗin an cire ma Zahra bandage ɗin da ke kanta har wurin ya warke

Abun dariya ya ba wa Arab ma sabida jin wai har marin ta tayi, sai ta sake tuntsirewa da dariya tana cewa, "wlh kin bani mugun dariya, abun ne kamar almara, wai kina mene ne har ta zauna ta mare ki?"

"Uhm baza ki gane bane Arab, Ni kaina nayi mamakin kaina saboda yanda na kasa ramawa, amma ta shammace Ni ne sannan ga mutumin da nake ba ki labari suna tare; yana ta bani haƙuri, Ni abin ma ya ɗaure mini kai yanda take nuna tsagwaron kishin ta."

Arab tace, "kashh! Ban ji daɗi da ba na wajen ba, na rantse da Allah da ace Ni ta yiwa marin nan sai na sumar da ita, ban ga abun da zai hana Ni tayar da ƙura a wajen nan ba koda jinina zai ƙare ne."

Zahra na dariya tace, "ke dai ayi sha'ani kawai, amma ai akwai alwashi a raina, sai dai kuma idan Allah bai haɗa mu ba."
Chapter 23 · 0% Book details