Sashe 8
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sauri da tashin hankali da ya nuna a kan muryansa yake magana, "don Allah kiyi haƙuri, ban san haka zai ɓata miki rai ba, but I will not do it again."
Yanda ta ji muryansa kamar zai yi kuka don har idanuwansa sun soma kaɗawa tare da ruwan hawaye, duk ya susuce yana ta roƙon ta, shiyasa tace, "is ok ya wuce."
Ajiyan zuciya ya sauke me ƙarfi tare da furta, "thanks Baby, kiyi haƙuri don Allah, Ina sonki."
"Ok. Ni zan kwanta, bye." Bata jira cewarsa ba ta katse kiran
Sai ya bi wayan da kallo zuciyarsa babu daɗi, haƙiƙa yana tsananin ƙaunar Arab a zuciyarsa, tsaban ƙaunar da yake mata ya rasa inda ke mishi daɗi a yanzu, bai san haka take ba sai a jiya da ya soma mu'amala da ita, yayinda tarin ƙaunar ta me tsanani ya ninku a zuciyarsa wanda yana jin bazai taɓa iya rayuwa ba tare da ita ba, dole ko ta halin ƙa-ƙa ne ya mallake ta ta zama tashi ta har abada. Numfashi ya sauke yana ajiye wayan a saman kujeran da yake zaune, a hankali ya furta, "na zama mahaukaci a kan ƙaunar ki A'isha, bazan taɓa samun sukuni ba har sai kin zama mallaki na, ina sonki da yawa!" Sai ya kama setting ƙirjin sa yana shafawa a hankali tare da lumshe idanuwansa.
Ita kuwa tana kwance bata tashi a wurin ba sai ga Firdausi ta shigo
Tace mata, "wai kina nan ba ki yi barci ba? I thought kin Yi barci tunda na ji ki shiru."
"No ina nan ban kwanta ba."
"Ok to ki kulle ƙofan, Ni zan wuce ɗakin Nafi'u sai in kwanta a can, sai da safe."
"To." Kaɗai ta furta tana miƙewa daga kan gadon. Sai ta bi bayan Firdausin bayan ta fita ta kulle ƙofan. Toilet ta shiga taYi wanka sannan ta ɗaura alwala ta fito, bayan ta gama shiryawa ta sanya kayan barcin ta riga da wando sannan ta rama sallan isha'i da bata yi ba. After she's finished sai ta kashe fitila ta kwanta, a nan ne ta ɗauki wayanta tana ta faman latse-latse. Bata yi barci ba har kusan ƙarfe ɗaya, tana kan WhatsApp tana hira da samarin ta, ciki kuwa har da Alh. Bashir da suke charting dashi, tamkar sun daɗe da sanin juna yanda ta saki jiki suna ta hira. A ranan basu kwanta ba sai da ta ci kuɗin shi, don account yace, "ta tura mishi." Tana yin mishi sending ya tura mata 50k a account ɗinta, farin ciki ne ya cika ta sai murna take yi
Yace mata, "yana buƙatar su haɗu, bazai iya jira har sai ya zo Zaria ba, amma ta biyo shi Abuja inda yake zaune."
Bata ja lokaci ba ta amince mishi zata zo, but sai dai tace mishi, "ya bari zuwa Sunday sabida yanzu tayi tafiya."
Yace, "ba komai."
Haka suka jima suna chart daga ƙarshe ta tura mishi hotunan ta sannan ta sauka ta kashe wayan, bata jira ma reply ɗinsa ba. A ranan a cikin farin ciki ta kwana, ta tabbata zata samu kuɗi a hannun mutumin nan, har ta lissafa irin fantamawan da zata yi, yanzu burin ta zai cika, dole ne ta wanke shi iya wanka har sai ta mallaki mota a hannun sa, burinta kenan. A haka barci ya sure ta cikin tunane-tunane da mafarkin kuɗin da zata samu.
[07/07, 11:30 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA BIYAR*
_______________ Washe gari Arab ita tayi musu Breakfast suka ci gaba ɗayan su
Ganin jikin Firdausi da sauƙi, sannan ga Arab a tare da ita shiyasa Nafi'u ya fita wajen aiki ya bar su
Bayan fitan shi ne Arab ta wuce ɗakin Firdausin tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigan atamfa fitet gwon. Sosai rigan ta zauna mata ɗas a jikinta ta fito mata da duk wata sura da Allah ya bata. Bata ɗaura ɗankwali ba sai ta zauna a bakin gado ta ɗauki wayanta ta kunna. Saƙonni ne suka soma shigo mata bayan ɗan wani lokaci da wayan ta gama daidaita, yawanci duk na samarinta ne sai na Ibrahim. Na shi ta soma buɗewa ta duba yana mata korafin, "meyasa ta kashe wayanta?" Bata yi mishi reply ba sai ta soma duba messages ɗin Alh. Bashir da taga ya turo mata. Murmushi ne ya bayyana a kan kyakkyawar fuskarta tana yi tana karantawa, ta san dama za'a rina dole zai susuce a kan hotunan da ta tura mishi, hakan take so dama. Wani irin shu'umin murmushi ta saki har da sautin shi, sai ta cije leɓen ƙasan bakinta tana wani turo baki, still akwai murmushin a kan fuskarta take ta faman karanta zafafan saƙonnin shi, har da korafinsa shima domin jin wayanta a rufe. Yana sanar mata ma, "bazai iya jurewa har tsawon wannan lokacin batare da ya kasance da kyakykyawa irinta ba, shi bai san ma haka take ba wlh." Kalamansa suna nuni da cewa ya gama susucewa da kyawun ta, hakan shi ne burin ta dama, yanzu ne wasan zai fara. Sai kawai ta danna airplane mode a wayan tare da ajiyewa, sai ta miƙe ta fice tana rera waƙar Isa Ayagi na "So ƙaddarar zuciya!" Har da murza jiki tsaban farin cikin ya kai mata
Firdausi da ke zaune a falo da Cup ɗin tea a hannunta, duk da yanzu suka gama karin safe amma har ta haɗa wani tea ɗin tana sha, sabida ba ta jure yunwa tunda ta samu cikin nan. Tun fitowarta ta ɗaga kai tana kallonta
Ita kuwa ko a jikinta tunda dama ba kunya ne a idanunta ba, rawan ta kawai take yi tana dariya sosai. A haka ta iso kujeran da Firdausi ke zaune ta zauna a kusa da ita cikin farin ciki da walwala wadda hakan ya nuna a kan fuskarta
Firdausi tace, "Auta wannan murna haka me ya faru?"
Kafaɗa ta ɗage da faɗin, "nothing. It was just something I remembered."
"Ok."
Sai ta shafa kanta tana sake kallon Firdausin da cewa, "za ki yi min kitso Aunty, kaina duk ya kwance."
Ɗan waro ido Firdausin tayi da cewa, "haba Auta, Ni da ban da lafiya ai bazan iya ba, ko kin manta jinya kika zo?"
Dariya tayi, sai kuma tace, "na manta wlh. Shikenan idan na koma sai in Yi, or when Aunty Ummu arrives she offers it to me." Ta ƙare maganar tana tashi ta ɗauko remote control da ke gaban t.v, and she came back sat down and started changing channels. Da haka suke hira da Firdausi zuwa ɗan wani lokaci sannan ta tashi tace, "bari ta ɗaura musu girki." Tana sane ta kashe wayanta saboda Alh. Bashir, tana son ta sake kama zuciyarshi don sai ta gama jan mishi aji before ta sake kula shi, haka tsarin ta yake, ba kowa ke samun Arab cikin sauƙi ba, yarinya ce me shegen wayau da shiga rai, musamman yanda kyawunta ke fuskar mutane shiyasa take da sauƙin kama zuciyar ko waye. Sai dai komai nata tana yi ne cikin class, She is not easy to deal with in her people, abu ɗaya ne yake saurin kama zuciyarta shi ne kuɗi, idan kana da kuɗi zaka ga tarairaya da ƙauna a wurinta, sai dai tana yin komai ne duk saboda kuɗi, tana da taurin zuciya wanda ba kowa ne zai iya shigan ta ba, duk yanda zata nuna maka ƙauna na ɗan lokaci kaɗan ne zata watsar da kai, ko kaɗan soyayya ba ta burge ta, koda wasa bata taɓa yi ba, in fact ma har yanzu ita bata yarda akwai wani SO ba, already ta sa a ranta komai kuɗi yana yi, farin ciki ne a soyayya, to ta tabbata duk sanda ta samu hamshaqin me kuɗi wanda take mafarkin samu a koda yaushe zata aure shi, shi ne kawai zai kawo mata farin ciki da soyayya a ranta, kuma har yanzu idanunta basu nuna mata wannan zaɓin ran nata ba, domin duk samarinta da ta taɓa yi kala-kalan masu kuɗi; har yanzu bata samu me kuɗin da zai iya siye zuciyarta ba bare har tayi marmarin auren shi. Sannan ita a rayuwa ba ta ƙaunar aure yanzu sabida gani take yi yanzu ta soma ɗiban duniyarta da tsinke, baza ta iya kashe kanta tun da ƙuruciyarta ba ta tarawa kanta matsalolin aure ba, tana da burika da yawa sai ta cika su kafin zata zaɓo namijin da ya cancanta ya mallake ta, sannan baya ga kuɗi tana son namijin da yayi suna a duniya ko iya Nigeria, wanda dai ya zama shahararre ne shi, irin kalan Mazan da take buƙata kenan.
Sai ku bi Ni masoya mu gani burin Arab zai cika ko kuwa? Wanne irin ƙalubale zata fuskanta sakamakon duniya da ke ruɗanta? Uhmm bamu fara ba fa, ku gyara zama kawai FAN'S 😍.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*ABUJA STATE*
Kwance yake a bakin tafkin Swimming pool, a kan kujera mai kamar gado na katako, babban garden ne wajen wanda aka ƙawata ko'ina da green grass. Yana sanye da Singlet fari sol tare da gajeren wando kalan kore da ɗige-ɗigen ja. Yayinda ya ɗaura dantsen hannunsa ɗaya a saman goshinsa, ɗaya hannun kuma yana riƙe da wayansa yana kallo, inda kyakykyawar murmushi ya ƙawatu a saman beauty face ɗinsa, ga dukkan alamu ya shagalu da kallon fuskar wayan ba tare da ya ankare da zuwan wata budurwa ba
Ita kam tana sanye da riga da wando matsatstsu da suka fito mata da halittun jikinta, sai ta saka baƙin gyale ta ɗaura a saman gashin attachment ɗinta da aka yi mata kwalliya dashi. Zuwan ta wurin ba tare da ya san da ita ba sai ta sanya hannu ta zare wayan daga hannunsa
Yayinda shi kuma a lokacin sai yayi firgigit tamkar ya dawo a cikin hayyacin sa yana bin ta da kallo, kana kuma ya tashi zaune fuskarsa tana haɗewa lokaci ɗaya murmushin da ke kai ya ɓace ɓat