Sashe 43
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Jameema ta hana sa da cewa, "kar ka ce komai ka dena hararan ta, gaskiya dai ta faɗa min kuma na gama yanke hukunci, a nan zaku zauna har ku tafi, yanzu bari in sa a kawo muku drinks ku fara sha before mu je mu ci abinci, nan jiran ku muke yi bamu ci komai ba sai kun zo; don nace tare zamu yi lunch ɗin." Sai ta koma kiran ƴar aikin nasu
Babu jimawa sai ga ta ta fito da gudun ta tana cewa, "Aunty gani."
"Kinga baƙi kuma sun zo ba ki kawo musu drinks ba? Bayan nace kar kiyi nisa da nan, maza haɗo musu snacks ki kawo musu, sannan ki kira min A'isha a ɗakinta."
Cikin girmamawa ta amsa mata before ta tashi ta tafi da saurin ta
Su kuma suka ci gaba da hiran su cikin raha da dariya; har sanda mai aikin ta kawo musu abun taɓa wa, suka ɗauka suna ci still suna hiran su
Malik yace, "Uncle ba ya nan ne wai?"
"Ba ya nan, amma na san nan da kwana biyu zai dawo sabida hidindimu sun yi mishi yawa ne ma."
"Maybe zamu tafi ma bai dawo ba kenan?"
"Ku yaushe zaku tafi?" Ta tambaye shi tana kallon sa
"Nan da two days din mu ma insha Allah."
Tace, "ok zaku haɗu ma kafin ku tafi tunda kuna tare da Ni." Ta ƙare maganar tana murmusawa
Su kuma sai suka yi dariya kawai
While Malik yana cewa, "wai Aunty ina Amaryan naki da aka yi miki?"
Nawwara da ke shan juice tayi saurin ajiyewa tana cewa, "Ni fa wlh Aunty da biyu na zo gidan nan fa, don wlh tunda aka ce an yi miki kishiya abun ya baƙanta min rai, gaskiya Uncle bai kyauta miki ba, yanzu mene ne abun ƙara aure kuna a wannan shekarun? Su fa Maza na lura basu da tabbas wlh."
Baki Malik ya saki yana kallonta
While Jameema sai dariya take yi sabida ta san halin Nawwara akwai ɗan banzan kishi, duk wanda yake tare da ita dole ne ya san halinta. Bata kai ga yin magana ba sai ga Arab ɗin ta fito, takunta suka ji shiyasa duk suka waiga ga turaren ta da ya bugi hancin su lokaci guda
Saukowa take yi daga matattaƙalan benen cikin taku irin na isa da tsantsan wayewa irin nata, tana sanye da bak'ar riga mai santsi har iya gwiwan ta, sai jan leggings tare da hill shoes red color, gashin kanta tayi parking ɗin shi sannan ta ɗaura hula mai tuntu wanda rabin gashin nata ta gaba a buɗe yake sabida style ɗin da tayi, tayi kyau matuƙa saboda yanda kayan suka halittu a jikinta suka bayyana kyakkyawar surar jikinta, duk da fuskarta babu makeup amma ta shafa lipstick mai maiƙo sai glowing yake yi bakin nata; daga nesa ma ana iya hango shaining ɗin sa
Wani irin shock Malik ya shiga da ganin fuskar Arab a wanann lokacin, bai yarda cewa ita bane shiyasa ya kasa motsi tunanin sa ya tsaya cak illa idanunsa da suke yawo a kanta
While Nawwara kuwa ita kanta kyawun Arab ɗin ya ruɗe ta har ta kasa ɗauke ido a kanta tsaban yanda tayi mata mugun kyau, tamkar hawainiya saboda yanda take sarrafa jikinta
Ita kuwa Arab ko kaɗan bata damu da irin kallon da suke mata ba, don itama ɗin idanun ta zuba musu musamman Malik, amma cikin jan aji sai ta ɗauke idanunta sabida ganin ta iso wajen, ta ƙariso da murmushi a fuskarta tace, "sannun ku da zuwa." Tana zama a kujeran da ke kallon wanda suka zauna, tunda duk suna kan three sitter ne sun sanya Jameema a tsakiya
Jameema tace, "wannan ita ce A'isha Matar Uncle ɗinku, ita ce Abokiyar zama na."
"Me?" Cewar Nawwara da ta kasa riƙe mamakin ta
Malik kuwa har miƙe wa yayi tsaban yanda maganar ta buge sa, tabbas Arab yake gani a gabansa wacce yake fatan ace yau Allah ya haɗa su, amma kuma mummunar maganar da ya ji Jameema ta furta sai da yasa lokaci ɗaya ya firgice ya shiga wani hali zufa na keto mishi
Da sauri Nawwara ta kalle shi tace, "mene ne haka Dear? Lafiya?"
Itama Jameeman tambayar da tayi masa kenan
While Arab na kallonsa ba tare da ta furta uffan ba, sai dai mamakinta yanda yake mata wannan kallon ƙurillan kamar maye
Shi kuma zama yayi yana kama kanshi ya kasa furta komai duk ya rikice har jikinsa rawa yake yi
Shiyasa hankalin su ya tashi don a tunanin su wani abun ne ya same shi, ga shi ya ƙi musu magana bare su san me ke faruwa
Nawwara miƙewa tayi ta dawo wurinsa duk ta gama ruɗewa itama, dafa shi tayi tana kiran sunan shi kamar zata yi kuka, "wai lafiya Dear me ke faruwa da kai ne?"
Daƙyar ya iya furta, "babu." Yana ɗago kansa tare da zuba wa Arab idanunsa da suka soma canza kala
"Wai me ke damun ka Abdul? Ya za'a yi kace babu komai bayan muna zaune lafiya yanzu?" Inji Jameema cike da damuwa a fuskarta itama
"Babu komai Aunty, kaina ne ya ɗan sara min." Ya furta a hankali yana runtse idanunsa
Jameema tace, "Ayya sorry, Allah ya baka lafiya, bari in samo maka magani ina zuwa." Sai ta miƙe da sauri ta wuce
While Nawwara sai sannu take mishi tana tattaɓa shi duk ta rikice
Arab kuwa taɓe baki kawai tayi don ita haushi ma yake bata ganin yanda yake ɗago kai yana kallonta a sace kamar wani tsohon maye, amma kuma wai ba shi da lafiya, alamu ya nuna mata akwai wani abu a ransa ne saboda kallon da yake mata, "ko dai ya sanni ne?" Wata zuciyar ta kawo mata wannan tunanin, sai kuma ta taɓe baki tana ɗage kafaɗa bata damu ba
Jameema na dawowa ta ba shi maganin ya sha sai sannu suke mishi
Ya so ya bar wurin amma bazai iya ba, domin ganin Arab ya fi mishi komai a yanzu, bazai taɓa iya jirgawa a wurin ba bayan ya ga yarinyar da yake burin gani a rayuwar sa, ga ta a gabansa tamkar mafarki, anya dai ba mafarkin yake yi ba har yanzu? Zuciyarsa ta hautsine gaba ɗaya don bai taɓa tunanin ganin ta ba, murna zai yi ko ihu? Ya rasa wanda yakamata yayi tsaban farin cikin da yake ji a cikin ransa, sai dai abun da ke ruguza mishi farin cikin a nan take idan ya tuna kalaman Jameema na cewa ita ce Matar Uncle ɗin su, wannan wacce irin mummunan ƙaddara ce? Yau ga ta ya ganta amma wai a matsayin Matar Uncle ɗin shi? Shikenan ya rasa ta kenan? No bazai taɓa yiwuwa ba domin yayi ma kansa alƙawari ko tana da aure sai ta zama tashi, ba ya da sukuni ko kaɗan a wannan lokacin, ya kasa ma furta komai hankalin sa kacokan yana kanta duk da ba ya fahimtar me ke faruwa a wurin
Ita kanta Arab ta gama tsarguwa da wannan shegen kallon da yake mata, bare itama tana jin kamar ta taɓa ganin mai kama da shi, maybe ya santa ne, shiyasa ta miƙe zata bar wurin
Amma sai Jameema tace, "ta tsaya tunda abinci zasu ci." Haka ta basu umarnin tashi su je su ci abincin
Babu musu suka miƙe su duka suka wuce wurin, Nawwara na manne a jikin Malik ɗin ta hana shi saƙat sai kula take yi dashi, ita tayi save ɗinshi ta tura mishi abincin a gabansa, sai kuma tace, "ko ta ba shi abincin da kanta tunda ta ga ya ƙi ci?"
Jameema tace, "oh wa ya ga masoya, a gabana ma sai kun nuna min kenan?"
Arab ta soma tashi tace, "ta ƙoshi." Sai ta koma Falo ta zauna
Shima sai Malik ɗin ya tashi tsalan yace, "ya ƙoshi."
Da mamaki Nawwara ta kalle shi tace, "Dear ba ka ci komai ba fa? Ka zauna ka ci ko kaɗan ne don Allah."
"Ba na ci, bazan iya cin komai ba yanzu baki na babu daɗi, zuwa anjima zan ci." Yayi maganar yana yin gaba zuwa Falon
Nawwara ganin ya zauna a Falon tare da Arab, sai kawai ta miƙe ta koma wurinsa ta manne mishi tana jan shi da hira don ɗauke mishi hankali
Amma sam bata san cewa ba ta ita yake yi ba, hankalinsa yana a kan Arab wacce ta duƙufa tana latsa wayanta tunda ta ga zuwan shi wurin
A sace yake kallonta ba ya son Nawwara ta gane, shiyasa yake ɗan biye mata don kar ta zargi wani abin tunda ya san halinta da shegen kishi yanzu sai ta iya gano wani abun
Ana haka Arab ta ɗago kanta saboda a jikinta tana jin irin kallon da ya tsare ta dashi, shiyasa ta ɗago itama ta zuba mishi idanu, suna haɗa ido ta sakar mishi harara tana yatsina fuska
While shi kuma sai ya sakar mata da singnal yana ɗan mata murmushi da wani irin narkakken kallo da ya jefa mata
Tuni Arab ta gane manufar sa; kasancewar ta ƴar hannu domin in dai akwai abu a ran Mutum zaka iya fahimta ko daga irin kallon da zai maka, itama ta fahimce shi shiyasa ta saki guntun murmushi kawai tana ɗauke kanta saboda zuwan Jameema wurin, sai ta miƙe tace, "Aunty bari in shiga ɗaki zan yi Call." Bayan ta amsa mata ne sai tayi gaba kamar zata tafi kuma sai ta sake haɗa ido da Malik ɗin suka sakar wa juna murmushi a tare; don ita burge ta yayi bare yanda ta ganshi mai kyau da alamu yana da tsananin tsafta koda kallon yanayin sa, komai nashi kamar ka sace musamman jikinsa na ƙirar ƙarfafa, shi ya fi ruɗanta, har kwaɗayin sa ta ji tana yi
Tunda ta tafi bata sake bari sun haɗu ba don ta ƙi fitowa bare su ga juna
Shi kuwa Malik duk ya zuba ido ya ga ta fito amma shiru, suna zaune sallah kaɗai yake tayar da su suna hira