Sashe 25
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da gudu ta riƙe Arab ɗin tana cewa, "Ah ah ya haka DPO? Ya za'a yi ka jefa min ƴata cell a kan wanne dalili? Su sauran shafaffu da mai ne da baza a saka su ba sai ita?"
"Ke! Ki kama kanki nan fa ba wajen wasan ku ba ne, ya za'a yi ku zo ku mayar mana da station filin dambe? Muna da maganin ku wlh don kun ishe mu, case ɗin ku yayi yawa a wajen mu zan ɗauki mummunan mataki a kanku."
"To ai naga dai ba wani abun muka yi ba, a kan haƙƙin ƴaƴana nake magana, wlh bazan bari a saka ta a cell ba sai an faɗa min abun da tayi, bazai taɓa yiwuwa ba."
Kallon yanda take kumfar baki kawai yake yi tsaban tsiya ya ci ranta, ya san matar nan bata da mutunci tunda ba yanzu suka saba sa'insa da ita ba idan aka kawo su nan, don haka yace, "yanzu za ki tsaya ayi sulhu ne ko kuma so kike yi mu nuna miki ƙarfin mu? Duk wani tsiya naki ba shi ne zai ƙwace ku a nan ba, don haka ki kama kanki tun kafin raina ya ɓaci."
Hakan ne yasa Inna ta sassauta ganin yanda taga fuskarsa babu alamun wasa, don ta san tsab zai iya kulle mata yara tunda shima ba kirki ne da shi ba
Kiran wani Corporal yayi yace, "ya je ya taho da sauran duk wanda zancen ya shafa."
Haka suka shigo mishi Office gaba ɗayan su har Shu'aibu mai shago, don yace, "wlh bazai yarda ba shima sai an biya shi kayan shagon shi." kuma ya san nan ne kaɗai zai iya samu a ƙwatan mishi haƙƙin shi
Nan DPO ɗin yace, "a sake mayar da maganar, kuma ayi masa daki-daki yanda zai fahimta."
Shu'aibu ya soma bayar da labarin abun da ya faru tunda shi aka ce yayi maganar since a gaban shi aka yi komai tun farko. Ai kuwa ya soma rattafa zancen komai yanda aka yi
Bayan an gama ne sai DPO yace, "to kin gani, ai har da laifin ƴarki tunda ga abun da aka faɗa a gabanta ta musa idan ƙarya ne."
"Eh babu zancen ƙarya a ciki, amma babu yanda za'a yi wata ta zo har inda nake ta taka Ni, meye laifi na don na ɗauki mataki? Idan don gaskiya za'a yi ai su ne da laifi tunda su suka zo suka taƙale Ni."
"Dalla rufe min baki mara kunya, ke dama ai ba a ka dake a zance, kina wannan halin ma baza kiyi shiru ba, to wlh idan na sake jin bakin ki za ki ganki a cell."
Tura baki gaba Arab tayi tana ƙunƙunai
Sarai yana jin ta shiyasa yayi ƙwafa ya mayar da hankalin sa a kan sauran
Inna tace, "to Ni ban ga aibun abun da Arab tayi ba tunda su suka soma taƙalan ta, don haka tun a nan wlh sai an yi musu tsakani kafin mu bar nan wurin, kuma dole ne a hukunta ta a kan kira min yara da tayi da karuwai, na rantse da Allah sai an ɗauki mataki don nima bazan yarda ba..."
"Ya isa haka Hajiya." DPO ya katse ta yana ɗaga mata hannu, "ki bari mu yanke hukunci ba ke za ki yanke mana ba."
"Ai naga nima maganar haƙƙina ake yi, wlh tallahi bazan yarda ba sai an hukunta ta tunda ta kira Ni da karuwa, zan ga idan ubanta ne ya taɓa ci na da take kira na da kalman." Arab tayi maganar tana kaɗa jiki don har ta manta da riƙe wurin da aka yaga mata gaban rigan, ta sake shi ana ganin breasts ɗinta
Da sauri DPO ya kawar da kanshi yana cewa, "ke shashashan yarinya ce ko? Ban hana ki magana ba? Zan ɗauki mataki a kanki kuwa yau. Kai kama ta ka saka min ita a cell." Ya ƙare maganar yana kallon inda Corporal din nan yake, duk suna tsaye da su Shu'aibu idanunsu yana kan Arab suna kallon t.v suna haɗiye yawu
Ita kuwa ko a jikinta. Sai ma jin da tayi za'a kama ta a saka ta a cell take faɗin, "ita wlh ba'a isa a saka ta a cell ba." Nan fa ta ɗaga musu hankalin wurin da hayagagan ta
Itama Inna ta riƙe ta gam tace, "baza a shiga da ita ba."
Ga shi shi DPO ba ya son kallonta sabida ganin albarkatun ƙirjin ta a buɗe, amma ganin suna son raina musu hankali sai ya cire kunya yayi musu jan ido yace, "a saka ta a cell."
Haka kuwa suka tura ta har ƴan sanda biyu suka saka ta kamar yanda DPO ya basu umarni, babu ɗankwali bare takalmi, har gyalen ma duk an watsar da su tun a can wurin dambe; ga riga a ɓarke
Wurin fa ya karaɗe da faɗan Inna, tace, "Sam sai an sako mata ɗiya baza ta taɓa yarda ba." Bala'i dai kala-kala da tijara haka take sauke musu, tana yi su Ummu suna taya ta
Sai da DPO ya sake yin musu jan ido ransa a mugun ɓace yace, "ya rantse sai ya haɗa su duka ya kulle idan basu bar mishi wurin nan ba."
Hankalin fa Inna ya tashi sabida ganin an ƙi ba ta Arab, bare yanda taga duk an farfasa mata fuska a damben da suka yi; shiyasa take ta musu haukan, "idan ɗiyar ta ta mutu ba'a bata sun tafi asibiti ba kaf ɗinsu sai tayi ƙaran su." Haka suka bar wurin suna tijaran nan sai kallon su ake yi
Domin su kansu ƴan sandan abun ya zame musu t.v ne tunda sun saba ganin hakan a wurin su, abun ma ya wuce a kansu har da ogan su ake yi yau. Duk da dama wani lokacin suna zuwa station ɗin ake sakin su tunda sun samu dai-dai dasu ƴan iska, shiyasa suke sakin su tunda zasu kewayo su ɗibi rabon su a wajen su
Amma yau DPO ne da kansa kuma shi ba irin halin shi bane shiyasa suka samu matsala yau, ransa ya ɓaci dalilin da yasa ya hana belin Arab kenan, kuma yace, "sai yayi maganin su." Haka ya sallami sauran bayan ya kashe Case ɗin, yace ma Shu'aibu, "ya je ya ƙirga duk asarar da aka yi masa masu damben zasu biya shi, daga su Zaliha har su Arab ɗin".
*******
Duk yanda su Inna suka so a saki Arab abun ya faskara, don DPO ya hana belin ta. Daƙyar da suɗin goshi aka samu ta fito a daren ranan domin a cikin Samarin Ummu ne wani ya fito da ita, tunda yana da hanyar manyan ƴan siyasa sai ya je ya roƙe ɗaya; shi ya saka baki aka sake ta
Daga can station ɗin ne ma aka wuce da ita asibiti tunda Inna tace, "sai an je an duba lafiyarta."
Suka je aka yi treating ɗinta sannan suka koma gida
Baba sai faɗa yake yi amma nan da nan ta hau kansa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, a kansa ta ƙare haushin ta, don ma dare yayi ne shiyasa ta bar zancen a iya gidanta, amma ta sha alwashin goben nan a gidan su Zaliha zata dira kaf sai ta ci uban su, sai tayi musu iyaka da gidanta. Ai kuwa duk abun da ya faru a station bata hankalta ba; gari na wayewa ta yiwa gidan su Zaliha mikiya wai ta zo wa uwarta jan kunne, "ta ja ma ƴarta kunne ta fita harkan ƴaƴan ta, duk sanda aka ce ta sake zagin su ta rantse da Allah kotu ne zai raba su domin tsiya daga nan har Mahadi ya bayyana."
Tana yi su Ummu suna yi don tare suka zo gaba ɗaya sukai ta tijara
Ga shi Maman Zalihan irin matan nan ne masu haƙuri, ta kasa tanka su don hankalin ta a tashe yake, musamman abun da ya faru jiya, sai da ta saka Yayan Zalihan yayi mata dukan tsiya, tace, "idan ta sake taƙalo mata faɗa da gidan to sai dai ya ƙare mata can ita kaɗai." Ta san za'a rina don ba mutunci ne da su ba baza su bar maganar ya tafi iya nan ba, ilai kuwa ga shi nan sun biyo ta gida suna mata ɗiban albarka, babu kowa a gidan sai ita, Allah-Allah take yi su tafi ba tare da ɗaya daga cikin ƴaƴan ta sun shigo ba, don ta san su ma baza su bar su haka nan ba sai sun tanka su, ƙarshe kuma abu ya ƙara rincaɓewa tunda su tsiya gaba suka bata ba baya ba, kowa ya san jaraban gidan su
Ana haka sai ga Zaliha ta faɗo gidan, tsautsayi ya dawo da ita tunda makarantar hadda ta tafi, kuma sai aka yi rashin Sa'a an kore su kuɗin makaranta tun a Gate. Haka ta shigo gidan ta tarar da abun da ke faruwa, ai kuwa nan ta saka baki ganin yanda suke yiwa uwarta ɗiban albarka
Nan da nan sai suka rufe ta da duka daga ƴaƴan har Innar. Suka yi mata lilis duk da haƙuri da shiga tsakanin da Maman Zalihan tayi basu barta ba
Arab sai da ta huce kaf haushin ta suka yi mata jina-jina
Maganar ma ta so komawa police station don rigima aka yi raga-raga, yayyin Zaliha suka ce, "baza su yarda ba sai sun ɗauki mataki."
Mamansu ta hana su tunda ta san faɗa da su Inna da jaraban su bazai taɓa ƙarewa ba, ƙarshe idan aka je wurin ƴan sanda a kasa amsar musu haƙƙin su, tace, "idan dai ta isa da su to su bar zancen, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka, ita Zalihan da ta taƙale su faɗa gobe sai ta ƙara."
Sun ji haushi yayyin da ta hana su ɗaukar mataki, haka dai suka bar zancen ba a son ransu ba, amma kowanne yana ƙullace da su da burin ɗaukar fansa wata rana, sa'an su ɗaya akwai Mahaifiyar su a tsakani da su ma sai sun ga ƙarshen jaraban su, don wlh baza su haƙura ba dole ayi ta ta ƙare