← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 52

Sashe 31

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tun yanzu Arab? Ki bari ku kai anjima ko Nafi'u zai dawo sai ku gaisa."

"A'a Aunty, yanzu zamu tafi tunda ba wani abin zai bamu ba, ki gaishe shi dai in ya dawo." Tayi maganar tana tashi tare da rataya gyalenta

Babu yanda ta iya tana ji tana gani suka yi mata sallama ta raka su har bakin ƙofa, sai da ta ga fitan su gidan before ta dawo ciki zuciyarta cike da fatan shiriya gare su.

             A ranan su Arab suka dawo Zaria, don tace, "baza ta kwana ba ta gaji, kewar ƴan uwanta take yi." Dole suka dawo gida cike da niƙi-niƙin kaya da ya kashe mata kuɗi.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           Su Malik duk yawon da suka yi don neman Arab but basu yi nasara ba, domin kuwa duk inda suka nausa sai sun nuna hoton ta ko zasu dace, duk da ita ba ɓoyayyiya bace don babu wanda bai san su ba a arean su, amma kasancewar ba wurin suka yi ba basu samu waɗanda suka santa ba, wasu kuma sun nuna sun santa sai dai basu san gidan su ba, sai dai a fuska sun santa har sukan ce, "suna yawan ganin su ta nan. Ko a waje kaza". Dole ba don sun so ba suka dawo gida tunda kwanan su biyu a Zaria, shiyasa suka koma Abuja da zummar bayan wani lokaci sai su sake komawa tunda gobe Monday ranan aiki ne

Sai dai kuma baƙin cikin sa tunda suka koma gida Abban su yace, "za'a tsayar da maganar auren sa da Nawwara, dama ya gaji da ganin su haka nan basu yi aure ba, don haka ya yanke shawaran dukka zai yi musu aure har Zainab itama ta fito da mijin."

Farin ciki wajen Nawwara ba a magana, kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha, duk wanda ke tare da ita ya san tana murna da wannan albishir ɗin da Abba yayi musu

Shi kuwa gogan ko kaɗan ba ya farin ciki, bai san dalili ba amma ko kusa ba ya son Auren yanzu, amma kuma babu yanda ya iya don ko a fuska bai nuna yanda za'a fahimta ba

Tunda aka tsayar da rana nan da wata ɗaya sai Nawwara ta matsa mishi, "sai sun yi party."

Babu yanda ya iya ya biye mata suka shirya gagarumin taro a gidan su Malik ɗin, kuma duk ƴan uwa sun zo komai an tafiyar dashi cikin girma da arziki

Zainab ma an tsayar da ranan auren nata duk tare za'a yi, wani Ustaz ta samu zata aura don dama ya jima yana neman ta, tunda ta yiwa sauran Samarin ta maganar auren suka gudu don babu wanda yake fatan ta zama matar shi, Macen da suka gama sani a waje ita ce zasu aura? Haka suka guje ta kuwa kowa ya ƙi auren ta, don haka ta dawo ta lallaɓa Ustazun da ya nuna yana ƙaunarta ba tun yanzu ba amma kullum wulaƙancin yau daban na gobe daban, tayi mishi cin kashin duniya but ya ƙi haƙura da ita ya nace mata

Shiyasa a sanda ta sanar mishi yayi farin ciki matuƙa, bai taɓa zaton zai iya samun ta ba don ya cire rai, sai dai zuciyarsa ne ta hana sa rabuwa da ita, sai ga shi Allah mai jin roƙon bawan sa ne ya tabbata addu'ar da yake yi ne Allah ya amsa mishi, cikin murna ya sanar da iyayen sa suka je nema masa auren ta, aka sanya rana wata ɗaya tare da na su Malik. To Allah yasa yana da abun yi don Malamin secondary ne kuma har da islamiyya yana dashi, yana samun kuɗi ta hanyoyi daban-daban a sana'ar sa don baza a ce mishi talaka ba, har gida yake ginawa

Amma dai Zainab tayi kuka sosai tunda har ga Allah ita ba ta ƙaunar Ya Sheikh; wanda ɗalibansa suke kiran sa da haka. Amma kuma haka nan ta ɗauki shawaran ƙanwarta Ikhlas wanda tace mata, "ta fito dashi kawai tunda ta rasa wanda zata nuna, idan ba haka ba Abba bazai bar maganar ba tunda har yace mata ta fito da Miji."

Shi matsalar sa ba ya magana biyu, idan zai yi abu yana yin shi ne a lokacin da ya yanke, kuma babu wanda ya isa ya sauya mishi zance, idan ma bata fito dashi ba zai iya zaɓo mata wani a ƴan uwa tunda ya sha yin zancen, "shi yana son auren zumunci." Shiyasa auren Malik da Nawwara ya fi komai faranta mishi. Ya so ace su ma su Zainab sun samu mai son su a cikin ƴan uwa, don wani lokacin har kwatance yake yi, "da ace wane zai nemi Zainab; ko wane da wane." Ire-iren maganar nan yana yawan yin shi

To itama ta so hakan a yanzu, sai dai kuma ta san halin su duk a cikin wanda yake lissafowa babu wanda bai kama ta a club ba, duk sun san halin ta shiyasa suke yaɓa mata magana ba sa shiri da ita ko kaɗan, maganganun ɓatanci da musguna wa shi suke jifan ta dashi, ta san duk sanda ta sake ta faɗa gidan ɗaya daga ciki kashin ta ya bushe, gwara ta lallaɓa Ya Sheikh tunda ta san yana ƙaunarta, ga shi kyakykyawa ba shi da wani makusa, kawai dai Allah bai sa mata soyayyar shi a zuciyarta bane, amma gwara shi sau dubu a kan su tunda shi bai san tana da wannan halin ba

Shiyasa tunda aka sa ranan suka soma gyara ita da Nawwara. Ita Nawwara nata mai sauƙi ne tunda wanda zai aure ta ya san wace ce ita sannan kuma tare suke iskancin su. Amma ita Zainab ita ce a tsaka mai wuya, tunda zata shiga gidan da ba'a san tana aikata zina ba, ya Sheikh bai taɓa sanin wannan mummunan halin nata ba, Nawwara ta kaita ta baro ga shi ita damuwar abun da zai biyo baya ya cika ta, tun ba'a je ko ina ba samarin ta sun guje ta ina ga tayi auren? Da wanne idon zata kalli Ya Sheikh ta sanar mishi ba ta tare da budurcin ta?

Ganin ta damu sai Nawwara tayi ta kwantar mata da hankali tana nuna mata, "babu wani ganewar da zai yi, idan aka je aka ɗinke ta ta ci gaba da shan magungunan mata nan da nan zata haɗe, duk da lokaci ƙanƙani ne amma ya ishe su ta gyara kanta ciki da bai bazai taɓa ganewa ba, abu ɗaya kawai zata yi ta nisanci kowanne namiji daga yanzu, ita kanta itama baza ta tafi gidan Malik a haka ba sai ta matse ta koma budurwa, zai sha mamakin ta."

Shiyasa suka shirya suka tafi asibiti aka ɗinke su kuwa. Suka soma shan magunguna kala-kala duk don su matse

Wannan dalilin ne hankalin Zainab ya ɗan kwanta ta saki jikinta tunda tana ganin an sami solution ɗin matsalarta.

Please share and voted 🙏
28/July/ 2022.
[29/07, 8:33 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

   *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA GOMA SHA TAKWAS*
_______________Tun dawowar Arab Alh. Bashir ya matsa mata, "sai ta zo ta same shi." Har a cikin ranta ba ta son tafiya sabida yace mata, "yana Lagos ne yanzu haka." Amma kuma yanda yayi mata alƙawarin kuɗi har wasu ya tura mata ta account shiyasa duk ta ruɗe ta amince mishi

Already yanzu motanta dukkan su suke hawa, tare da su Zahra ake koya musu kuma duk Ibrahim yake koya musu, ko a sanda take Kaduna yana fita tare da su Zahran ya koya musu, da ta dawo kuma sai suke fita tare, yanzu ita hannunta ya faɗa duk da ba wai sosai ta iya ba, amma ta fi su Ummu since ita an daɗe da soma koya mata. Yanzu haka ta samu wurin ajiye motanta don ba ta ƙaunar ajiye ta a waje dama, yara suna taɓa mata duk da ba ta ganin su but idan ta zo ta duba sai taga alamun ana taɓa mata, shiyasa tayi tunanin kai ajiya gidan wata Amarya da aka yi a layin su, kasancewar duk layin babu wani gida mai Gate sai sabon gidan da aka yi, sun tare kusan sati ɗaya kenan, a gidan motan take kwana yanzu; tunda ta je ta tambayi Matar gidan, "zata riƙa kawo motan idan babu damuwa?"

Ai kuwa ta amince mata don yarinya ce itama Amaryan baza ta wuce sa'ar Zahra ba, amma kuma kasancewar Arab ta shiga ranta lokaci ɗaya suka yi sabo da juna, har da su Zahran ma suna zuwa gidan suna gaisawa

Kuma Mijin ba shi da matsala bai hana su ba tunda dai akwai filin ajiyewa, duk da yana jin raɗe-raɗin mutane da suke hana shi barin Matar shi tayi mu'amala da su Arab, ana yawan faɗa mishi, "karuwai ne kawai zasu ɓata mishi Mata ne, gwara ya raba su tun wuri." To shi dai bai hana su ba tunda suna gaisawar mutunci suna mishi kirki, ya dai ja kunnen Matarsa tayi hankali da su duk da yana ganin yanayin su da shigan da suke yi sam ba na masu tarbiyya bane, amma kuma wannan ba shi ne dalilin da zai hana taimaka musu ko ya hana matar shi mu'amala da su ba, idan za'a yi zaman lafiya shikenan, idan kuma abun zai juye a samu matsala sai ya ɗauki mataki

Ita dai Arab tunda ya amince ya bar su suna ajiye mota hakan ya fi mata komai daɗi, idan zasu hau suna zuwa su ɗauka, kuma baza su mayar da ita gidan ba sai dare. Koda ta tashi tafiya Legos ba da motan tayi ninyar tafiya ba, zata bi jirgi kamar yanda Alh. Bashir ya turo mata kuɗin da zata biya, ai wannan abun ba ƙaramin faranta ran Arab yayi ba, wannan ce rana ta farko da zata hau jirgi a rayuwarta, farin cikin ta ba ya misaltuwa, tana ganin girman ta da matsayin ta ya ƙara ƙaruwa
Chapter 31 · 0% Book details