← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 52

Sashe 38

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk a cikinsu babu wanda yayi tunanin ya je ya duba ta, don hidimar biki ya sha musu kai, tunda aka sanar musu babu wanda ya sake bi ta kanta, su Zahra sun dai yi mata waya har suka nemi ta tura musu hoton Baby

Ita kanta bata so haihuwar nan yanzu ba don ta so zuwa gidansu, tunda tayi aure bata taɓa zuwa ba, kullum Nafi'u sai dai ya bata haƙuri yace, "ta bari zuwa wani lokaci, shi wulaƙancin da za'a yi musu ne ba ya so, kar ya zo su je Inna tayi musu koran kare, kuma bazai jure ganin ƙunci a tattare da ita ba, gwara ta bari duk sanda suka tashi zuwa ya zamana Inna tana buƙatar su kuma tayi kewar su a sannan ɗin." Da wannan daɗin bakin ta amince ta haƙura ta zauna, musamman idan ta tuna da Baba shima ya kan ce mata, "tayi zamanta kawai." Amma ganin ta haihu har ana saura kwana uku suna babu wanda ya leƙo mata sai kuka take yi, duk ta tashi hankalin ta, nan ta kira Baba tana sanar mishi, "babu wanda zai zo mata ne?"

Shi ne dalilin da yasa ya roƙi Inna a kan, "a tura wata ta je wajenta don Allah."

Amma furr Inna ta ƙi, tace, "babu wanda zai je, ai su ma sha'anin biki suke yi, ta ƙarata can tunda ita ta zaɓi haka."

Su kansu ba sa son zuwa tunda ana biki, amma ganin har da hawaye Baba yayi shiyasa Ummu tace, "zata je, amma ranan sunan zata dawo don bata yi alkawarin wuce wa ba."

Inna bata ce komai ba tunda ita da kanta ta so zuwa ba wani yayi mata tilas ba

Haka Ummu ta wuce Kaduna. To sai a lokacin ne Firdausi ta ɗan ji dama-dama, ko banza ta samu ƴar uwanta ta zo

A washe gari kuma sai ga ƙanwar Baba itama ta je, dayake yayi mata waya ya faɗa mata halin da ake ciki, duk da ita sam ta fita harkan gidan Yayan nata, musamman a kan ƴaƴan Inna Harira sam babu ruwanta, amma yanda ya kira ta ya nuna mata damuwarsa shiyasa ta shirya suka wuce ita da ƴarta wacce ta aurar, sai kuma budurwan yarinyar ta wacce take gabanta, sa'ar Arab CE, ita kuma wacce ta aurar sa'ar Zahra ce amma ta girme ta da watanni, Ƙannin Malam Iro su biyu ne, daga Nana Firdausi sai Samira. Nana Firdausi ita ce wacce Firdausi ta ci sunanta, kuma ta rasu tun haihuwar fari da tayi, yarinyar ce take wurin Samira, kuma ita ta raine ta har tayi mata aure, sai dai ita yarinyar sa'ar Ummu ce, tayi aure a can wani ƙauye gaba da inda Gwaggo Samira take aure tunda itama a ƙauyen take da zama. Tsiya da fitinan Inna ne yasa kaf ɗinsu ba sa ƙaunar zuwa wurin Baba, sabida sun san halinta bata da kirki bare mutunci ko ƙalilan

Har ƴan uwanta sun fita harkanta sabida tana da ƴan uba tunda ita kaɗai aka haifa a ɗakinsu. Sun fita harkanta tunda sun ce, "ba wani abun kirki take basu ba illa jaraba da zasu kwasa." Bare sun fita samu sun fita hutu da jin dadi, amma tunda suka ga yanda Allah ya mayar da ita a wannan gaɓar shiyasa duk suka sako jiki suka zo wannan bikin na Arab

Ai kuwa sun ga wulaƙanci da gori, sai dai dama matsiyaci wanda ba shi da zuciya; in dai a kan kuɗi ne sun rigada sun yar da zuciyarsu kare ya ɗauka, sam sun ƙi tafiya duk da gorin da tayi musu, a haka akai ta biki da su suna nane

Duk wani events da aka yi babu wanda SN. Ƙasim ya halarta, tunda ba shi da lokaci a cewar sa, gidan Amarya kawai suke kiɗan su suke rawan su, ai kuwa Arab tayi ƙarya a bikin nan ba kaɗan ba, an kashe kuɗi sanunu domin ƙawata bikin nan, ko ina ka je sai zancen bikin ake yi sabida yanda yayi matuƙar haɗuwa

A ranan da aka ɗaura auren kar ku so kuga jama'ar da suka halarta, manyan mutane ne masu hannu da shuni har da gidan sarauta, kama daga na Kanon har na nan Zarian, sannan ga ƴan siyasa waɗanda suka yi fice sosai. Bikin nan an nuna ƙarya gaskiya, musamman yanda sadakin Arab ya kasance Naira miliyan biyu da mota Mercedes Benz sabuwa fil tana walwali, motan a ƙiyasin ta zata kai 13million

Hmm babu bakin magana sabida farin cikin wannan ranan, sun sake tsinkewa da lamarin Senator Ƙasim, kuma lamarin nashi ya soma basu tsoro, amma dayake abun da suke so kenan babu wanda ya damu bare yayi tunanin wanne irin kuɗi ne haka dashi da zai riƙa musu ɓarin shi? Sun san dai Mutum ne ɗan siyasa dole a samu kuɗi a wurin shi

Mutane an samu bakin gulma, sai dai babu damar yi a gaban Inna, domin dai-dai take da ƙugun kowacce shegiya, yanzu sai ta raba halin ta ba damuwar ta bane

Komai na bikin a hotel aka yi odan shi, kama daga abun sha da ci har inda aka sauke baƙin a can hotel aka yi musu masauki, sai da zasu zo ɗaurin auren ƙofar gidan su Arab ne sannan suka fito

An ci an sha an ƙoshi kuma an watse lafiya. Sai Allah ya kaimu gobe za'a ɗauki Amarya. Kar ku so kuga yanda ta koma, babu wanda idan ya san Arab zai iya gane ta a wannan lokacin sabida haɗuwar da tayi, ta sha gyaran Amarya ciki da waje, har wani ɗaukar ido take yi idan ta zo wurin jama'a, tana fita daban ne kawai kowa ya ganta ya san amarya ce, ga ƙyalli da tsantsi da fatarta ke yi duk wanda ya kalle ta sai ya so ya dauwama yana kallon kyawu da tsarin halittar ta, bazai so ace ko da wasa ya ƙyafta ido a kanta ba. Da yawa ta tafi da imanin jama'a a bikin nan

Su kansu Abokan Ango abun ya ɗaure musu kai; ya aka yi Senator ya samo wannan yarinya ƙarama haka mai zubin larabawa sabida tsantsan kyau da Allah yayi mata?

Sai dai yayi dariya yace, "rabon sa ne kawai."

Sun taya sa murna sosai. Don su ma su Ummu babu wanda bata samu Saurayi a cikin su ba, domin tuni sun shige musu

Zuwa washe gari suka wuce Kano da su Zahra kaɗai. An sauke su a babban katafaren gidan Senator Ƙasim. Gida ne mai hawa uku tsaban girman sa tamkar baza a mutu ba, side ɗin Arab daban na uwar gida Jameema daban. Sun sake susuce wa da suka gansu a wannan gidan

Arab bakinta ya ƙi rufuwa tsaban daɗi, mafarkin da take yi a kullum kenan ga shi Allah ya cika mata burin ta, ko zama bata yi ba ta hau zagaye ilahirin part ɗinta

Haka su ma su Ummu suna biye da ita suna taya ta, sai ɗaukar hoton gidan suke yi suna yin video a tiktok. Sun yi santin gidan tamkar kar su taho su bar ta, bare yanda komai yin musu ake yi wanka ne kaɗai ba a yin musu, hatta kayan da zasu saka kawo musu ake yi, abinci kuwa sai sun ture sabida yawan shi

Kwanan su biyu aka zo da mota aka ɗauke su, tare da kyautar dubu ɗari biyar biyar da Jameema ta kawo musu a matsayin nata tsaraban, suka yi mata godiya sosai don ba ƙaramin burge su tayi ba sabida yanda ta kula dasu a zuwan nasu, kullum tana part ɗin tana tambayar matsalolin su, ko sun ce ba sa son abu sai ta kawo musu

Ita kanta Arab ta yaba da hankalin Matar kuma ta shiga ranta, har Aunty take kiranta dashi a lokaci guda, sabida Matar babba ce zata iya kai wa arba'in a shekaru, ga kuma yanda take kula dasu tamkar ƙannin ta shiyasa nan take ta bata girmanta

Bayan an kai su Zahra gida ne a nan me motan ya basu kyautar da Senator Ƙasim yace, "a basu." Motan cike fam da kaya sai murna suke yi

Tun tafiyar su Jameema take kula da Arab, don wani lokacin ma a part ɗinta take wuni, dayake ba sa aikin komai an wadata su da masu aiki ko ta ina, sai dai su zauna suna hira suna sake sanin juna, ko kuma suyi kallo sai dare sannan Jameema zata tafi. Har kuma wannan lokacin Arab bata sake ganin Senator ba, ita sam bai dame ta ba tunda ga ta a cikin daula, tana cin abun da take so ta bar abun da bata so, lokaci ɗaya ta sake kilewa kamar ba ita ba, tamkar ka taɓa ta jini ya tsillo

Jameema bata taɓa mata maganar Mijin nasu ba sai sau ɗaya da tace mata, "aiki ne yayi mishi yawa ba ya kwana a gida, kin san zaɓe ya kusa bare shi da yake neman babban kujera."

Murmushi kawai Arab tayi tunda bata damu ba, amma kuma yau da gobe tunda ta saba a koda yaushe ana cinta bata taɓa kwanaki babu namaji ba; sai abun ya soma damun ta, dalilin da yasa ta nemi abokan harƙallan ta a chart take samu har ta biya wa kanta buƙata, shiyasa ta ɗan rage zama da Jameema wuni tana ɗaki tana charting da ba ya ƙare wa, sai da taga tamkar zata mutu abun yayi mata yawa don har ta kai ba ta jin daɗin biyan buƙatarta da kanta, namiji kawai take buƙata, ga shi tsawon sati biyu ana shiga na uku babu Miji babu alamar sa, shiyasa tace ma Tariq, "ya zo kawai ya same ta." Ita ta tsara mishi komai yanda Plan ɗin su zai kasance. Har kuma ta sanar da Jameema a kan, "ɗan uwanta ne zai zo gidan sabida akwai kasuwancin da zai yi a nan Kano; shi ne zai zo su gaisa."

"Jameema tace, "ai babu komai ya zo nan ma ya zauna, suna da ɗakuna birjik sai inda ya so ya zauna."

Farin ciki ne ya cika Arab sabida dama hasashen ta kenan, kuma ga shi ya tabbata, har tsallen murna tayi a wurin

Yayinda Jameema take ta faman kallonta kamar wata mayya tana mata murmushi
Chapter 38 · 0% Book details