Sashe 21
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Baba koda ya dawo ya tarar da mota a waje bai ce musu komai ba, harkan gaban sa kawai yake yi domin tunda ya ga yanda suke duba kaya cike a tsakar gida ya san cewa Arab ne ta taho dashi, kuma motan ma ya san cewa nata ne tunda yana jin Inna tana magana. Shiru kawai yayi ya zubawa sarautar Allah ido; tunda ya ga abun yayi gaba sai dai idan Allah ya so ya shirye su, kuma zai ci gaba da musu addu'a tunda shi kaɗai ne abun da zai iya, Allah yasa su gane gaskiya idan masu shiryuwa ne fatan sa kenan a koda yaushe.
Arab kiran Ibrahim tayi tace, "ya zo ya ga mota."
Ai kuwa babu jimawa sai ga shi, tare suka fita a motan yana tuƙa su, sosai ya taya ta murna sai koɗa ta yake yi yana cewa, "yanzu ne ta faso gari ta zama babbar yarinya, duk inda suka je yanzu ne za'a kalle ta da ƙima da mutunci."
Dariya tayi tace, "shiyasa nake sonka Bestyna sabida yanda kake sanya Ni farin ciki, kaima kason ka na nan zan tura maka ta account; sabida ba don kai ba bazan samu wannan kuɗin ba, Ni kaina na san Yanzu ne nake ji nakai na cika Mace babbar yarinya." Ta ƙare maganar tana buɗe hannayen ta cikin farin ciki
Dariya kawai yake mata ganin yanda ta koma tana rawa a zaunen. Sai ya soma rera mata waƙa suna dariya dukkan su
Cikin farin ciki haka suka kasance a wannan lokacin, duk da dare yayi but sun ƙi komawa gida, ƙarshe wani restaurant suka je suka ci abinci suka siya ice cream da shawarma. Bayan sun gama ci sannan suka nufo gida
A hanya ne Arab take ce mishi, "zai soma koya mata motan zuwa gobe."
Yace, "bata da matsala ai, yana da time duk sanda take so zai koya mata."
"Da yamma zai fi tunda Ni yanzu na dena tuyan awara, na zama big girl daga yau, zan sanar da Inna ma."
Ihu yayi yana buga sitiyarin motan da cewa, "hihu! Babban yarinya Matar manya, kin fi ƙarfin Yaro sai dai baban Yaro! Gaskiya dama lokaci yayi da Yakamata ace kin dena fita talla, yanzu kina da sana'ar da ya fi wannan Babe, don haka ki share batun talla kawai, kwanan nan zamu riƙa out garuruwa za ki ga irin manyan mutanen da za ki samo wlh."
Waro manyan idanuwanta tayi fuskarta da murmushi tace, "da gaske kake yi Besty?"
"Wlh kuwa. Ai zaman ki a waje ɗaya ne shiyasa har yanzu ba ki san matsayin ki ba Baby, irinku ba sa zama a waje ɗaya, don wlh kwanan nan burin ki zai cika, kin san irin Alhazawan nan da kike buƙata celebraties irin su za ki samu, Ni na san irin wuraren da ake iya ganin su; don haka idan muka samu time zamu riƙa fita muna zuwa buɗe ido kawai, a can za ki yi kamu wanda suka fi Alhaji Bashir, zaki ce na faɗa miki, bare ke kyakykyawa babu namijin da zai ganki bai susuce a kanki ba, ke ta musamman ce Arab a kullum ina faɗa miki, kuma na san ba Ni kaɗai nake sanar miki da hakan ba, kin bambanta da sauran Mata, kina da bambanci da su sosai, abun da nake so kawai in sanar miki ki sake dagewa, ki gyara kanki da duk inda kike so ki shiga za ki shiga, wlh a lokaci ɗaya ke kanki sai kin zama celebraty ba wai ki zauna sai kin yi hurɗa da celebraties ba, za ki zama mai kuɗi the Yong lady. Babbar mai kuɗi."
Bakinta ta washe zuciyarta cike da farin cikin jin zancen shi, tace, "Wow! Baka ji yanda nake ji a raina bane da ka furta wadannan kalaman, Allah ya tabbatar da zancen ka Besty, Ni na san kai me so na ne kuma bani da tamkar ka, ka taka rawa a rayuwata domin haɗuwa ta da kai alkhairi ne, shiyasa nake matuƙar ƙaunarka, kai nawa ne nima taka ce, ko aure nayi muna tare bazan rabu da kai ba."
"Na fi kowa sanin haka Besty, na san kina ƙaunata haka nima nake ƙaunar ki, Allah ya barmu tare."
Dariya suka yi har suna kashewa
"Ka san wani abu, Mutumin nan fa ya dame Ni, ban taɓa ganin me naci irin shi ba, ya takura min wlh." Ta ƙare maganar tana yatsina fuska
"Wanne Mutumi kenan?" Ya tambaye ta don bai fahimci wane ne ba
"Tariq. Ka san ya takura min matuƙa, sabida shi na kashe wayana ina Abuja wlh ya takura min, yanzu kuma kaga shi yake kira, da ya san na dawo garin maybe da tuni ka ganshi, but zan ɗauki mummunan mataki a kanshi tunda na nuna mishi ba na so but bazai ƙyale Ni ba."
Dariya yayi Ibrahim yace, "but a kan me za ki ɗauki mataki bayan na san hakan kika fi so? Kar ki manta fa shima daga ganin shi akwai maiƙo a wajen shi, kawai ki ajiye ajin nan naki ki ba da kai bori ya hau don na san kawai wahalar dashi kike yi har yanzu."
"Baza ka gane bane Besty, na kula shi ba hakan yake so daga gare Ni ba, shi aure na yake so yayi." Sai kuma tayi dariya tare da cewa, "abun da bazai taɓa yiwuwa bane ai, Ni in Yi aure yanzu ai maganar ma bata taso ba, but duk bayanin da nayi mishi ya ƙi fahimta."
Ibrahim yace, "ba ki fahimtar dashi bane shiyasa bai gane ba, ki sake gwada wa but Ni dai kar ki bar shi sabida nayi miki bincike a kanshi yana da kuɗi gaskiya, za ki more."
Bakinta ta taɓe kawai tana mayar da hankalinta a kan wayanta ganin ana kira, sai dai bata ɗauka ba suka ci gaba da hiran su da Ibrahim har suka kai gida. Sai da suka yi sallama tukunna ta shiga gida da key ɗin motan ta, sai kuma tsaraban abubuwan da suka ci da ta kawo ma su Inna.
Washe gari sai ga Tariq a ƙofar gidan su
Tayi mamakin ganin sa tunda bata sanar mishi ta dawo ba, hasali ma bata ɗauki wayan sa ba tun jiya. Ta fito kenan Inna ta aike ta nan maƙota taga motan shi. Tana sanye da shuɗiyar atamfa da kalan fari da ja a jikinta, ɗinkin riga da skirt ne sai dai an ci ma kayan mutunci matuƙa, duk shatin halittar da Allah yayi mata ya bayyana, kanta babu ɗankwali sai farin gyale siriri da ta yafa a kai, ƙafanta kuma flat shoes ne baƙi mai siraran igiya, face ɗinta babu makeup but ta sha jan janbaki sai glowing yake Yi bakin nata, tana yi tana taunan chewing gum irin na gogaggun ƴan duniyar nan
Tunda ya hange ta ya fito daga motan ya nufo ta
Tana ganin shi ta ɓata fuska, sai dai ta tsaya bata tafi ba illa kallonsa da take yi
Haka shima kallonta yake yi har ya iso wajen, fuskarsa da yalwan murmushi yace, "ranki ya daɗe! Ashe kin dawo shine ba ki sanar min ba? Laifin me nayi miki da kika kasa ɗaukar wayana?"
Yatsina fuska tayi kamar yanda ya zame mata jiki, cike da yanga irin nata tace, "ina da uzuri ne, yanzu me ya kawo ka gidan mu bayan ban ce ka zo ba? Ka san irin hakan ne na tsana ban buƙaci mutum ba ya tako inda nake."
Idanu kawai ya zuba mata kamar zai cinye ta sabida yanda take sarrafa bakin nata yana tafiya da imanin shi, cikin rashin kuzari kamar zai yi kuka yace, "don Allah kiyi haƙuri tunda na san nayi laifi, but rashin ɗaukar wayana da ba ki yi bane, sannan kuma naji labarin kin dawo ba ki neme ni ba kamar yanda muka yi alƙawari, hankali na ya tashi a tunani na nayi miki laifi ne."
"Babu laifin da kayi min, but yanzu dai ina da abun yi zan tafi sabida sauri nake yi."
Da sauri ya sha gabanta ganin har ta wuce shi, "haba Princess haka za ki tafi ba ki ce min komai ba? Na san ke mai cika alƙawari ne kuma kin yi min alƙawari zamu yi magana idan kika dawo, but ga shi yanzu kin ƙi kula Ni."
Kallonsa tayi tace, "shikenan. Ka bani address ɗin inda zamu haɗu zan zo."
Washe baki yayi yace, "da gaske kike yi?"
Kanta ta jinjina mishi bata ce komai ba illa kallonsa da take yi
"Ok. Ina da guess house sai mu haɗu a can, hakan zai fi mana sirri ko?"
Murmushi tayi masa tace, "why not, idan yayi maka ai shikenan."
"Yayi min, a nan tudun Wada ne layin ƴan nono, but baza ki gane gidan ba zan zo sai in ɗauke ki mu tafi, yaushe ne?"
Shiru ta ɗan yi, sai kuma tayi fari da idanuwanta cikin salo irin nata tace, "ok. Zuwa ƙarfe biyu sai ka zo, Ni na tafi bye." Da haka ta wuce bata jira cewarsa ba
Shima yana mata ba-bye har ta ƙule masa, sannan ne ya shiga motansa ya ja ya tafi cikin farin ciki, ya san zai kasance da ita yau kenan, but da sannu zai mallake ta wata rana, amma ai yanzu aka soma zai ci gaba da bin duk hanyoyin da zai ja hankalinta ta ƙaunace shi har suyi aure, wannan shi ne burin shi don ya fi so gaba ɗayanta ya mallake ta ne sai yanda yayi da ita babu shamaki a taren su.
Zuwa ƙarfe biyu kuwa sai ga shi ya zo, yana yin parking ya kira ta a waya ya sanar mata
Kamar shuɗewar mintuna goma sha biyar sai ga ta ta fito, sanye da riga da wando ƙananu, kayan sun matse ta matuƙa ko ina na jikinta ya bayyana sai rawa yake yi, fuskar nan nata tasha makeup da yayi mata kyau ainun, ta yafa ƙaramin gyale iyakan wuyanta, sai tayi using da hill shoes, tana taunan chewing gum kamar yanda ya zame mata ɗabi'a. Kai tsaye wajen motan ta nufa ta shige ya ja suka tafi