Sashe 41
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"To na gode, na san dai ban kyauta miki ba ki sake haƙuri da Ni komai ya kusa wuce wa." Sai ya ja numfashi yana cewa, "mu je ki haɗa min ruwan wanka in na gama sai na ci abinci, na ga dare ma yayi." Ya ƙare maganar da duba agogon hannunsa
Tashi tayi suka wuce bedroom ɗinta, a nan yayi wankan sannan ya wuce nashi ɗakin da ke part ɗinta ya shirya
A time ɗin tuni Arab ta saka an shirya musu abincin a dainning. Yana fitowa suka wuce suka ci abincin, yana jan ta da hira har suka gama, nan da nan har ta saki jikinta ta ma manta me ya faru, sai da suka taɓa kallo before suka koma ɗaki suka kwanta
Abun da ya ba wa Arab mamaki ganin bai yi mata komai ba haka suka kwanta, shiyasa take tunanin to ko lafiya? But bata damu ba dai ta juya kai itama tayi barcinta tunda yau bata da matsalar komai already Tariq ya kawar mata da kwaɗayin ta
Zuwa washe gari sai kusan ƙarfe biyu sannan Senator ya bar gidan, lokacin ma Jameema ta dawo sannan ya tafi.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Yanzu haka su Inna suna ta shirye-shiryen wuce wa Saudiya ne tunda lokaci yayi, sai dai kuma jikin Baba ya ƙi daɗi a ɗan kwanakin nan, har sanadin hakan ne yasa aka kwantar da shi a asibiti
Inna dai babu ruwanta don tace, "wlh baza tayi jinyar sa ba, can ta matse mishi lokaci yana yi zata tafi Saudiyyan ta, yanzu ba tashi take yi ba."
Sai su Ummu ne suke zaune dashi, idan wannan ta kwana yau gobe sai wancan, sun sanar da Arab halin da yake ciki har ta turo musu kuɗi, kuma matsalar ga shi Senator ba ya zama a gida bare ta sanar mishi, idan ta kira wayansa ba ya ɗauka, shiyasa ta sanar da Jameema
Ita kuma tace mata, "ta shirya kawai ta je ta gaishe shi." Sannan ta bata kuɗi tace, "tayi hidiman asibitin dashi."
Arab ta amsa tayi mata godiya sosai don ba ƙaramin farin ciki tayi da kuɗin ba. Haka ta shirya suka wuce da Tariq don shima a lokacin ne zai koma sabida ayyukan sa.
Bayan sun sauka a Zaria ita ta wuce gida
Inna tayi farin cikin ganin ta ba kaɗan ba tamkar zata goya ta, haka ma Ummu tunda a time ɗin ita tana gida Zahra na Asibiti. Sai murna suke yi haka itama ɗin, farin ciki duk ya cika ta don ba kaɗan ba tayi kewar ƴan uwanta tamkar yau ta taɓa yin nesa da su, but wannan daban ne tunda aure ne
Haka Inna na rawan jiki tayi ta kula da ita, ta ɗauko mata wannan ta ɗauko mata wancan, duk a tunanin Inna ciki Arab take dashi saboda ganin yanda ta sake sauya wa a ɗan ƙanƙanin lokacin nan, tamkar ba ita ba, kowa ya ganta ya ga Matar manya sabida tsaban kyan da tayi, har wani ɗaukar idanu take yi, sosai ta sauya ba kaɗan ba komai nata ya sauya tayi dam da ita gunun sha'awa, ko maganar ta ma ta sauya salon ta tsaban yanda take yanga da kwarkwasa
Sai da ta huta sannan suka wuce asibitin tare da Ummu a motanta, motan da Senator ya bata ranan bikin ta tunda a shi suka zo ita da Tariq, dayake shi lokacin da ya je can motan haya ya hau, motocin ta na gida kuma guda biyun yanzu Zahra da Ummu kowa yana amfani da ɗaya ne. Koda suka je asibitin haka suka rungume juna da Zahra sai murna suke yi suna dariya, kowacce fuskarta cike da farin ciki
Jikin Baban da sauƙi don a lokacin ma ya samu barci ne har tashi yana iya yi ya zagaya. A lokacin da ya farka ya ji daɗin ganin Arab kuma ya nuna murnan sa sosai, haka yayi ta sanya musu albarka yana musu nasiha
Duk jikinsu yayi sanyi sosai a yau ɗin, sun zauna suna ta sauraron shi domin ji suke yi tamkar wasiyya yake musu sabida yanda nasihan nasa yake ratsa musu zuciya
Sai dare sannan suka wuce gida, aka bar Ummu ita zata kwana dashi
Bayan sun koma ne sai ga kiran Senator Ƙasim ya kira. Ta ɗauka suka gaisa yana tambayar ta, "ya mai jiki? Jameema ta sanar mishi but tayi haƙuri sai yanzu ya samu ya kira."
Murmushi kawai tayi tace, "babu komai Alhaji, ai jikin ma da sauƙi."
"To Masha Allah haka ake so." Sai kuma yayi ɗan shiru before ya ci gaba da cewa, "ki zauna zuwa lokacin da kike son dawowa sai ki dawo, zan tura miki saƙo ta account sai ayi hidimar asibitin dashi."
"To." Kaɗai tace mishi jikinta duk a sanyaye, har suka gama wayan bata yi wata magana sosai ba
Zahra da ke kusa da ita dariya tayi tace, "kina sha'anin ki ƙanwata, gaskiya kin more da yawa da samun wannan Mijin naki, kinga yanda kika sauya? Anya bazan bi ki mu tafi tare in Yi kwana biyu a can ba? Dama ina son zaman Kano wlh."
Murmushi Arab tayi tace, "zan ji daɗin hakan gaskiya tunda nima na gaji da zaman Ni kaɗai, kullum kana zaune kamar wani maye."
Zahra tace, "haba kina nufin kishiyar taki yanzu babu ruwanta da ke ne ko kuma Mijin ba ya zama ne?"
"Hmm baza ki gane ba." Arab ta furta tana ajiye wayanta a saman cinyanta tare da ɗaura hannunta ɗaya a saman fuskarta tana shafa wa
"Ki sanar da Ni zan gane, ko akwai wata matsala ne?"
Kallon fuskarta Arab tayi before tace, "babu wata matsala zan iya cewa; tunda ban rasa komai ba a gidan, sannan Aunty Jameema tana kula dani sosai yanda kika san ɗiyarta, matsalar har yanzu Mijin bai taɓa kwana dani ba, ke in faɗa miki ma tunda aka yi auren sau ɗaya na taɓa ganin shi ya dawo ya kwana a gidan, kullum ba ya gida, Ni kuma gaskiya bazan iya ba duk da dai zuwansa da rashin sa bai dame Ni ba, amma bazan iya zama a haka babu namiji kusa da Ni ba, shiyasa kawai na kira Tariq ya zauna dani a can."
"Me?" Zahra ta furta da sauri tana ware idanun ta
"Ƙwarai kuwa, kiran sa nayi kuma a gidan ya zauna a matsayin ɗan uwana, babu wanda ya zarge Ni ya maye min gurbin Mijina tunda shi ba ya tani."
"Tab ɗijam... Kin yi auren ma baza ki bar wannan rayuwar ba Arab? me kike nema ne da yanzu ba ki samu ba? Ina jiye miki abun da zai faru a gaba."
Taɓe bakin ta tayi ko a jikinta tace, "me zai faru? Babu abun da zai faru, ke bari ki ji Ni fa ba nayi auren nan don wani abu bane face kuɗi, kuma dama ban taɓa saka wa a raina zan dena rayuwar ƴanci na ba, sana'a ce a gare Ni idan har zan samu dama sai na dama wlh, bazan takura in hana kaina jin daɗin rayuwa ba, duk da kuɗi dai alhmadulillah sai dai na ba wani amma bazai yiwu na cuci kaina wajen hana zuciyata abun da take so ba, tsoho na aura fa, a haka zan ƙare rayuwata?"
Zahra tace, "lallai ina jiye miki lokacin da asirin ki zai tonu Allah kuwa, aure kuma ba abun wasa bane Arab, shiyasa nima nake son yin auren nan don na gaji da zama a haka ina cutuwa, Haidar ya dawo har mun yi magana zai turo, kin san fa tunda ya ji labarin Alhaji Abubakar yana nema na shi ne duk ya damu wai kar in ƙara kula sa, yanzu tunda ya dawo yace zai turo muyi auren."
Arab ta kalle ta tace, "amma ke wawiya ce wlh, kina nufin za ki bar Alhaji Abubakar ɗin; ki auri Haidar? Kin kuwa san waye Alhaji Abubakar? Wlh wlh ya fi Mijina kuɗi domin da kanshi Mijin nawa yake faɗa min yanda suke, kuma yace duk wasu kasuwancin su shi ya ɗaura sa a kansu."
"To ai hakan ba shi zai sa in aure shi ba don yana da kuɗi, Ni farin cikin zuciyata nake so, kuma da kike cewa yana da kuɗi ai shima Haidar ɗin ba matsiyaci bane kin sani, sannan jini ne na Sarauta, wlh ya fiye min shi a kan in auri tsohon nan, Allah ya kyauta sam bazan iya ba, yanzu ke ma kike faɗa da bakin ki baza ki iya rayuwa da tsoho ba babu jin daɗin rayuwa."
Tsaki Arab ta ja tace, "wani zubin ke doluwa ce Allah, ana nuna miki ga Annabi kina runtse ido."
Hannu Zahran ta sa ta taska mata duka a cinya tana cewa, "ya ishe ki fa wlh, uwar waye doluwar? Allah Arab kin raina Ni Ko kina manta Ni Yayar ki ce?"
"Ban manta ba, gani nayi sam ba ki da wayau." Tayi maganar a fusace saboda jin zafin dukan ya shige ta, kana ta ƙara da cewa, "Bari zan faɗa ma Inna sai ta nuna miki gaskiya tunda ke sam ba kya gane wa." Ta ja tsaki tana tashi zata fice
Zahra tace, "wannan kuma ke ta shafa, zan gani idan za'a yi min auren dole ne." Itama ta ja tsakin tana tashi ta bi bayanta
Arab kuwa na fita wajen Inna ta je ta faɗa mata
Itama Innan bata goyi bayan Zahran ba
Amma ita Zahra sam tace, "baza ta iya auren tsoho ba Haidar ne zaɓin ta, gwara ma su dena zancen."
Haka dai suka haƙura suka bar ta tunda ta ƙi gane abun da suke nufi.
**********
Arab tayi zaman ta a gidan su tunda ga abun da mijin yace, iyakan ta kira Jameema suyi waya, yawo kuwa babu inda ba ta zuwa don ba ta zama a gida, daga tana can da wannan namijin sai a ganta da wancan, tamkar bata yi aure ba don manta wa take yi da wani Aure a kanta tsula tsiyanta kawai take yi, ta ƙi komawa ne sai idan Inna ta tafi Saudiya tunda lokaci yayi ana ta kiran Alhazai