Sashe 13
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Wlh kuwa, ban gama abun da nake yi bane Aunty."
"Ok yaushe zaka koma?"
Yace, "yau nake saka rai."
"Kana nufin baza ka koma gidana bane?" Tayi maganar cikin waro ido
Sai ya ɗan langaɓe kai da cewa, "to Aunty mai zan koma yi?"
Hararansa tayi da cewa, "mu yi sallama mana."
Sai yayi murmushi mai bayyana haƙora yana shafa suman kanshi yace, "to ai Aunty ga shi muna yin sallaman."
"A'a Ni ban yarda ba, wai kana saurin meye ne?"
"Aunty kin san na bar Dad, kuma kinga ban bar wa kowa drugs ɗinsa ba dole zan koma."
"Eh haka ne, but ya jikin nashi?"
"Da sauƙi sosai. Next week we'll be back in Germany to check it out."
Murmushi Auntyn tayi tace, "alhamdulillah Masha Allah, haka nake son ji, amma don Allah kar ka tafi ka bari in tashi mu je gida tare."
"Aunty akwai inda zan je yanzu, kuma ina son in ziyarci wani Aboki na da muka yi school tare, tunda na zo yakamata in je har gida mu gaisa before in koma, ban san ranan dawowana ba."
Aunty tace, "shikenan bazan matsa maka ba tunda kace hakan, sai muyi sallaman a nan."
"Or how long are you going to get up?" He speaks looking at her
Tace, "by six insha Allah."
"So I'll come and say goodbye when I finish what I'm doing, zamu haɗu a gidan."
Washe baki tayi tace, "yauwa ɗan lele na, haka nake son ji."
Murmushi sosai ya bayyana a kan fuskarsa sabida yana jin daɗin wannan sunan
Itama murmushin tayi tace, "yanzu ina son duba person suna jira na bari in je."
"Ok." Yace hakan yana miƙewa tare da sake faɗin, "bari in je nima aunty, sai na zo gidan."
"To Ƙanina, ka kula da kanka."
Murmushi yayi bai ce komai ba ya juya ya fice
Itama kuma ta rufe file ɗin gabanta sannan ta ɗauki wani ta tashi ta fita; zuwa room ɗin da zata duba mara su lafiyan ta.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
Su Arab da suka fita kai tsaye keke napep suka hau suka ce, "ya kaisu wani Asibitin." kamar yanda suka sanar da wancan
Sai dai har wannan lokacin babu wacce tayi magana a cikin su. Kowa yana jajanta abun da ya faru tare da tunanin wannan kyakykyawar saurayin da yayi musu haka
Musamman ma Arab wadda abun yayi matuƙar ƙona mata rai da bata mamaki, abun haushin yanda ta kasa buɗe baki ta mayar mishi da martani sabida tsananin shakkar sa da kwarjininsa da ya cika ta, tabbas ranta yayi matuƙar ɓaci saboda babu wanda ya taɓa gaya mata magana kamar wannan guy ɗin; bare har yayi mata tsawa a kai, sosai ranta ke ƙara ɓaci wanda ji take yi kamar ta koma tayi masa wulaƙanci, tabbas baza ta taɓa hucewa ba idan har bata mayar mishi da martani ba. Kanta ta kama ta riƙe sosai sabida ta rasa tunanin me zata yi don ta huce takaicin sa
Zahra kuwa itama tunanin ne a ranta, sai dai ita nata ya sha bamban dana Arab, ba ƙaramin burge ta yayi ba, yanayin sa kawai take tunanowa fuskarta ɗauke da murmushi, idan da ace zata same shi fa. Haƙiƙa ya haɗu ga baiwar kyawu, Allah yayi halitta a nan, ga babu alamar tsoro a tattare da shi wanda ko wacce Mace ta ga halayyarsa sai ta afka mishi a soyayya. "oh Allah! Dama akwai saurayi irin sa a wannan zamanin?" Ta furta a ranta tana sake murmusawa, sai kuma ta kalli Arab ganin yanda ta kama kanta, sai ta taɓo ta tana tambayarta, "lafiya Auta me ya same ki?"
Ɗago kanta tayi ta sauke mata manyan idanuwanta da suka soma sanja kala zuwa ja, sai dai bata ce komai ba ta mayar da kanta ƙasa ta duƙar
Itama Zahra bata sake magana ba don babu shakka abun da Aliyu yayi musu shi ne yake damun Arab, ta san halinta kuma tayi mamakin yanda ta kasa mayar mishi da martani, amma ta san ya cancanci hakan ne tunda ba wanda za'a yi mishi wargi bane, wannan ya wuce tunanin su domin ko da ganinsa ba shi da wasa.
Tsayar da napep ɗin da Drivern yayi ne shiyasa suka dawo cikin hayyacin su a lokaci ɗaya, ganin sun tsaya a wani gini a saman an rubuta Hospital center shiyasa suka tabbatar an kawo ne. Sai suka fito suka ba shi kuɗinsa da ya sanar musu suka shiga ciki
Wannan karon koda suka samu wata nurse basu tambaye ta kai tsaye Office ɗin Likita ba, sai suka bata kuɗi suka ce, "ta sanar musu idan ana zubar da ciki a nan? Nan suke nema."
Ai kuwa ganin kuɗi har 5k. Farin ciki ya cikata tunda sun samu haɗamammiya dai-dai da wacce suke nema. Ta ko kai su wurin wani likita Christian
Babu ɓata lokaci ya amince da buƙatar su bayan ya sara musu kuɗi mai yawa, wanda suka ciro ma bai ishe shi ba sai da ya caje su wani kuɗin
But sai Arab ta ƙi ba shi don ita ta fi shi zalamar kuɗi, duk wani wayonka ba ka isa ka ci bati a wurinta ba duk da ba ita zata biya kuɗin ba. A nan tayi dabaru irin nata a matsayin ta na riƙaƙƙiya ƴar duniya wacce ta san yanda ake tafiyar da naMiji, ta kalallame shi da yaudaran ta a haka yayi musu sauƙi. Har da yin mishi alƙawarin, "zasu haɗu da shi a duk inda yake so." sannan ta amshi Numban shi
Shi kuwa gogan ya ga zuƙa-zuƙan ƴan mata kuma ya samu banza a ɓagas, ai kuwa ya yiwa Zahra abun da zai mata ya cire mata cikin, sannan yace, "dole sai ta zauna ya ƙara mata ruwa tunda jikinta babu daɗi."
Haka kuwa babu yanda suka iya sabida baza ta iya tashi ba, duk jikinta yayi weak sai jiri da take ji sakamakon yanda ta zubar da jini
Kasancewar suna sauri ba sa son su jima sosai sai Arab ta matsa mishi, "ya sallame su kawai." Tunda ta ga leda ɗaya ya ƙare. Tace, "idan suka koma gida za'a saka mata wani."
Yace, "kin tabbatar za'a saka mata?"
"Yes Doctor I'm sure, muna komawa gida zamu samu Doctor ya ƙara mata."
Baki a washe yace, "Me kyau ko za ki bani address ɗin gidan ku sai in zo in saka mata hakan zai fi ko?"
Murmushinta da ke shagaltar da duk wanda tayi masa ta saki, tana wani yatsina fuska cike da yanga tace, "don't worry doctor, ba sai ka zo ba muna da likitan da zai duba ta, babu damuwa."
"Yarinya mai kyau kin tabbatar?"
Kanta ta gyaɗa mishi still tana sakar mishi kyakkyawar murmushinta
"Ok. Let me give you the medicine she will take, her body will be much easier."
"Ok thanks."
Haka ya haɗa musu a kyauta kuma da kanshi ya amso musu. Ya basu ya raka su har haraban asibitin, tamkar kar ya rabu dasu yana ta ɗaga musu hannu yana washe baki cike da jin daɗi
Su kuwa ko bi ta kanshi basu yi ba suka wuce gida
Ai kuwa Firdausi da Ummu tuni sun soma tambayar su, "ina suka je suka daɗe haka?" Musamman yanda suka ga yanayin Zahra tamkar bata da lafiya tunda har a lokacin daƙyar take tafiya, fuskarta duk ta sauya
Arab tace, "zaga gari nace muku zamu yi, kuma Aunty Zahra zazzaɓi ne ya rufe ta shiyasa."
Nan fa suka ruɗe dukkan su. Firdausi har da cewa, "su je asibiti hankalin su zai fi kwanciya, gwara a duba abun da yake damunta."
But Arab tayi saurin cewa, "sai da muka je daga can ma muke, ga maganin ta a hannu na, sun ce babu damuwa fever ne kawai, very soon zai sauka."
Hakan yasa hankalin su ya ɗan kwanta
Sai Zahran ta je ta kwanta a ɗakin Firdausi
Nan Arab ta bi bayanta tana cewa, "ta bari idan sun koma gida sai a ƙara mata ruwan idan jikin bai yi daɗi ba." Sai ta juya ta barta ta koma Falo.
Kusan ƙarfe biyar da rabi suka gama shiryawa zasu tafi gida. Wanda har lokacin jikin Zahra bai yi sauƙi sosai ba tunda bata da wani ƙarfi, sai a hankali dai zata warware. Sun yi shigan su iri ɗaya riga da skirt na material les, kowacce da nata style ɗin, sun yi kyau matuƙa tunda sun saba shiga iri ɗaya, kowa ya gansu sai ya ji sha'awar su shiyasa duk inda suka je a tare sai an kalle su kuma sai sun burge don daga gani ƴan gida ɗaya ne
Firdausi kamar zata yi kuka ganin sun fito zasu tafi, sai tace, "don Allah kar su sake banzartar da ita, Please su dawo nan kusa kar su biyewa Inna su ƙi zuwa su duba ta, zata ji daɗi idan sun zo."
Duk dariya suke mata ganin yanda tayi da fuska kamar zata yi kuka
Arab tace, "to ke Aunty ke meyasa baza ki zo ba sai mu?"
"To Auta kin san halin Innarmu shiyasa ma Nafi'u ya hana Ni zuwa har yanzu; sabida bai san me Inna zata yi mana ba, amma kwanan nan zan zo in duba ku ko ba a so."
"To ai naga kina da Baba me ƙaunar ki meye na wannan maganar? Kawai idan za ki zo ki zo ba wai ki tsaya da hujjar Inna ba ta so ba." Arab ɗin ta sake faɗa tana taɓe baki
Murmushi kawai Firdausi tayi sai ta sauya maganar da cewa, "to Ni dai don Allah ku zo ba sai na haihu ba."
Ummu tace, "kar ki damu Aunty duk sanda muka samu hutun school me yawa zamu zo muyi miki kwana biyu, ki kwantar da hankalin ki kawai."
Murmushin farin ciki tayi cike da murna tace, "yauwa Nagode, don Allah idan kun je ku gaishe da su Innan da kyau, ga wannan ledan sai ki bata, da saƙon Baba a ciki shima ki gaishe shi da kyau, idan kun koma zamu yi waya." Ta miƙo ledan da ke hannunta; Zahra da ke kusa da ita ta amsa
Arab tace, "wai Aunty mu fa zamu tafi idan Mijin nan naki bai dawo ba, mun gaji da jira."