← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 52

Sashe 37

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai abun da yayi gaba yanzu a wajen Arab, ta ƙaro wulaƙanci tunda komai tana dashi, babu abun da masu kuɗi zasu nuna musu wanda su basu dashi, su ma sun tashi a talaka sun koma masu kuɗin waɗanda sun fi ƙarfin raini, ga motocin ta duk a gidan, ɗaya take hawa ta bar wa su Zahra ɗayan. Yanzu ko school ta dena zuwa don yanzu bata da lokacin sa ma, ba don lokaci ya ƙure ba da tuni ta zana S.S.C.E ɗinta tunda yanzu abun da tayi tunani kenan, but ta bari zuwa next year ɗin sai ta zana, yanzu komai kuɗi nayi ko bata je ba zata samu kwalinta a hannu shaidar ta gama school, yanzu iskanci a wajen ta sai abun da yayi gaba, ba ta kula ƙananun yara sai manya, kuma idan har zaka ganta a wuri sai irin manya-manyan wurin nan inda sai masu hannu da shuni suke zuwa, shiyasa yanzu samarin ta duk irin manya-manyan Alhazawan nan ne; sai dai ta ci kuɗinsu son ranta

Har yanzu suna tare da Besty don tare suke tsula tsiyan su. Tare suke yawon ta-zubar ɗin su duk inda akwai casu da holewa can zaka gansu, yanzu ta kai har ba ta kwana a gida sai idan ta so, wata rana ma sai dai su bar garin gaba ɗaya sunan sun tafi biki ko wani party, babu mai hana ta tunda Inna tana goyon bayanta. Yanzu ba Alhaji Bashir kaɗai take bi duk inda ya so ba, kowanne Alhaji idan ya kira ta tana bin shi ya kwana da ita, zai ɗauke ta tsawon kwanakin da zai yi idan tafiya yayi, zata zama ita ce tamkar matar shi har sanda zai dawo, shiyasa yanzu Arab ba ƙaramar mai kuɗi bace don ta fi ƙarfin komai, ta fi ƙarfin Yara kamar yanda take faɗa a koyaushe yanzu burin ta ya cika, babu inda sunan ta bai zaga ba in dai ana zancen gagga-gagga kuma tatattun ƴan duniya ne waɗanda suka shahara a iskanci. Duk wani babban ɗan iska ya santa kuma yana mu'amala da ita. Ta sake sauyawa tayi ƙiba na samun hutu da jin daɗi, ga jikinta da ya ƙara buɗewa ta zama babbar Mace komai ya ji, ƙirjin nan nata sun yi fam breasts a tsatstsaye suna tsole idanun Maza tare da ruɗan su, haka ma zubin dirinta, baza ka taɓa tunanin ƴar 17years bace tsaban yanda ta haɗa waɗannan kayan, sai dai a fuska ne kawai idan ka kalle ta za ka tabbatar da yarinya ce sharaf tunda fuskar Yara gare ta, fuskarta ƴar tsut ce da kyawu da Allah ya bata, tana da circle ɗin fuska da kuma kufan gashi, don duk fuskarta gashi ne har saje take dashi, gashin giranta kuma har sun kusa haɗewa; ga manyan idanu masu ban sha'awa da ɗaukar hankali farare sol a lumshe irin masu shiga jikin nan idan ta kalli Mutum, bakinta ɗan ƙarami sai dogon hanci, skin ɗinta kuma irin mai kyau ɗin nan ne don fara ce sol irin mai ɗaukar hankalin nan, ta ko'ina Arab ta kai Mace wacce kowanne namiji fatansa ace ya same ta, tana da kyau na fizgar hankali shiyasa suke ruɗewa idan suka ganta, ga ta da saurin shiga rai saboda yanda ta iya sarrafa jikinta, tafiyarta ma kanta abun kallo ne idan tana sarrafa jikinta, ga shegen iyayi da yanga kamar ta karye tsaban ta ƙware a bariki. Sai dai kash! Duk wannan kyawun; kyawun ɗan Maciji ne..... Uhmmm mu je zuwa, yanzu ne za a fara kafta wa.....

            **********

            Alh. Ƙasim Ali, shahararren mai kuɗi ne wanda yake zaune a garin Kano, tsohon ɗan siyasa ne wanda ya ci jiya ya ci yau; kuma yana saka ran gobe ma a dama dashi, yanzu haka kujeran senator yake kai, but yana neman takarar gwamna wanda yake son ya zama gwamnan jahar Kano a wannan shekarar. Shi mutane suka sani a yanzu kuma sunan shi babu inda bai zaga ba, Mutum ne mai facaka da kuɗi da taimakon talakawa da nuna musu shi na gari ne don samun jama'a, kuma Allah ya ba shi ɗin don yana da farin jini, duk abun da zai yi yana yi ne don jama'a su yabe shi su kuma so shi. Shi ne wanda ya bayyana a matsayin Mutumin da yake aiko wa Arab da maƙudan kuɗaɗe da kuma duk hidiman da yake mata da sunan yana sonta

Ba ita kaɗai ba, kaf ɗinsu sun yi matukar girgiza da jin Sn. Ƙasim Ali ne wanda yake yiwa Arab duk wannan hidiman, kuma yake burin ya aure ta. Ai su shar abun su domin wannan babban dama ce a gare su

Barin ma Arab da ta watsar da duk wani makamanta na ƙin yin aure yanzu sai a nan gaba, to ta san idan tayi sake da damar ta zata iya kufce mata, namijin da take buƙatar aure ne a yanzu ya zo gare ta, burin ta dama bai wuce ta auri shahararren mai kuɗi ba kuma wanda yayi suna domin itama ta kasance ana damawa da ita; sunan ta ya shiga ko ina ta nunawa duniya itama celebraty ne, kuma shi ne wannan ta samu tunda ga shi kujeran Gwamna sulluguda yake nema, nan gaba kaɗan zata iya zama First Lady, me ya fi mata wannan? Baza ta taɓa wasa da damar ta ba, dole ta amince mishi jiki na rawa, duk da har yanzu bai tako ya zo wajenta ba a cewar sa, "aiki yayi mishi yawa, yanzu haka ma ba ya ƙasan." Ita babu ruwanta wannan bai shafe ta ba tunda bata damu da sai ya zo gare ta ba, in dai zai aure ta to ita mai sauƙi ne tuni ta sallama mishi

Sun sake ruɗewa a sanda ya sake musu wani babban kyautar. Ya biya wa Baba da Inna aikin Hajji wannan banar da ta rage sauran watanni kaɗan. Yanzu ma haka shirye-shiryen azumi ake yi. Yace, "nan da bayan azumi za'a yi musu aure da Arab." Kuma har Inna ta amince tunda ita ce a kan komai yanzu, Baba ma bai da lafiya sosai yana kwance a gida, sai dai a taimaka masa. Kuma a cikin azumin ne dukkan su zasu wuce Umrah

Uhm daɗi har da kuka. Inna faɗi take yi, "yau burinta ya cika, dama ta sani wata rana a ƙashin arzikin ƴaƴanta zata je Makka ta fita ƙasarta na haihuwa, ga shi Allah ya cika mata burin ta, yau haihuwa tayi albarka ga shi ta samu surukin da ya ɗauki duk wani ɗawainiyar su albarkacin ƴarta."

Azumi na zuwa kuwa suka wuce gaba ɗayan su har Baba, tunda ya ɗan ji sauƙin jikinsa, a sanda zasu wuce ne SN. Ƙasim ya zo garin

Arab tayi mamakin ganin tunda ya zo ya tafi kwanansa biyu a Zaria; bai taɓa tunanin taɓa ta ba, don tunda ya sauka yasa aka ɗauko ta ta zo gidan da yake zaune, sai dai suyi hira yana faɗa mata wasu abubuwa nashi amma bai taɓa riƙe ta ba, lokaci ɗaya ta saba dashi tunda Mutum ne mai sakin fuska, har bata labari yayi a inda ya taɓa haɗuwa da ita, tana tare da wani Abokin sa a nan Adamawa zuwan da ta taɓa yi, tunda ya ganta ya kasa sukuni shi ne sai da ya bincika aka nemo mishi ita. Ta sake mamaki sosai musamman yanda ta gane ya san komai a kanta, ya san irin Rayuwar da take yi amma a haka yake son Auren ta, shi kuma ga shi tamkar mutumin kirki ba ya ko yin mata maganar banza, ba ya ƙoƙarin taɓa ta, burinsa kawai suyi hira na nishaɗi ta yanda zata saki jiki da shi. Ai kuwa tamkar sun shekara da sanin juna sun saba sosai, don har waya ya bata suka gaisa da matarsa ta gida, hakan ne yasa Arab ta sake sakin jikinta sosai musamman yanda ta ga matar ta nuna mata kulawa da kirki, itama ga ta kalar shi mai faram-faram. Arab bata da damuwa tunda ba wai don soyayya zata aure shi ba, zata aure shi ne kawai don kuɗinsa da kuma sunan da yayi, amma ita soyayya ba ta gabanta tunda har yanzu bata yarda akwai ta ba, kuɗi na siyan komai a wurinta, komai zata iya samu kuma ga shi tana kan samu ɗin

Sai dai matsalarta ɗaya da ta so samu a wajen Tariq, ya saka ta gaba tunda ya ji zancen auren ta, har kwantawa yayi a asibiti don jin zancen, gaskiya itama ta tausaya mishi kuma ba ta ƙaunar rabuwa da shi saboda kulawar da yake bata, shi kaɗai ne yake iya gamsar da ita tana matuƙar jin daɗin harka dashi, sai dai tace mishi, "gwara ma yayi haƙuri don baza ta taɓa auren sa ba, yayi haƙuri kawai su ci gaba da yanda suke a haka, tayi masa alƙawari suna tare koyaushe, aure bazai sa su rabu ba, duk sanda yake buƙatar ta ya zo inda take zata san yanda zata yi su kasance tare."

Ganin bazai same ta ba tunda da gaske take yi zata kuɓuce masa, dole ya amince da hakan tunda burin sa ace suna tare ɗin, musamman da ta ƙara ƙarfafa masa gwiwan, "wata rana zata iya fitowa ba dauwama zata yi da auren ba, don ita ba ta jin zata iya zama waje ɗaya, in dai da takura to zata fito, idan kuma babu takura zata ci gaba da rayuwarta yadda ta saba yi." Hakan ne yasa ya ji sanyi a ransa har ya haƙura.

              Bayan sun dawo daga Umran ne aka tsayar da ranan aure nan da sati biyu masu zuwa, a cewar sa, "komai shi zai yi musu".
[04/08, 8:39 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

    *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA ASHIRIN DA BIYU*
_______________Ana saura kwana tara bikin Arab; Firdausi ta haihu, ta haifi ɗa namiji
Chapter 37 · 0% Book details