← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 52

Sashe 29

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yarinyar baya ta shiga suka wuce bayan sun sake sallama da Arab. Babu nisa kuwa tunda tafiyar mintuna biyar ya kaisu kofar gidan, sai da yarinyar ta fita suka yi sallama tare da kissing ɗin juna before ta sauka ya ja motan ya tafi. Su kuma suka shiga gidan

Akwai mutane sosai a gidan wanda zai tabbatar maka da sha'ani ake yi, ga mata nan sai tuƙa tuwon biki suke yi ana ta hayaniya. Yawanci basu kula da shigowar Arab ba tunda kowa harkan gaban shi yake yi, wasu kuma hankalin su ya je gare ta har suna ta kallon ta sabida farin ta ma kaɗai zai iya jawo hankalin ka gare ta bare kyanta

Hakan ne yasa ta gaishe su suka wuce ciki

Har ɗakin Maman Amaryan ta kaita suka gaisa, take ce mata, "in ji Yaya Umar ne yace a kawo ta wajen Aunty Laila."

Maman tace, "ai tana gidan su Safara'u, maza ki kaita can Fatima."

"To." Ta amsa tana miƙewa suka fice tare da Arab ɗin. Can ta kaita kamar yanda Mamansu tace mata, tana zuwa ta hangi Lailan cikin ƙawayenta tunda gidan su kaɗai ne, a nan suke taron su

Suna zaune a falo sai hayaniya suke yi ana ta gardaman ɗaura girkin da ba'a yi ba. Shigowar su Arab da sallaman su duk sai hankalinsu ya raja'a a kanta; suka bi ta da kallo kamar sun samu t.v

Arab babu ruwanta sai taunan chewing gum ɗinta take yi itama tana tsatstsare su da ido kamar yanda suke bin ta da kallon, a ranta tana ayyana wace ce Amaryan tana yatsina fuska; kasancewar yanda ta gansu ba wasu gogaggun ƴan mata bane sosai, kuma duk babu sa'an ta tunda sun girme ta sosai, zasu yi sa'annin Ummun su a yanda ta fahimta

Fatiman ce ta yiwa Lailan bayani sannan ta tafi

Itama Laila ta gane ta tunda yanzu suka gama waya da Umar ɗin yake sanar mata, har tana tsokanar Ƙawarta da tun jiya da suka haɗu da Tariq ta nuna tana sonshi, har sanar mishi tayi don ta kasa haƙura, amma bata samu fuska ba, take ce mata, "yanzu budurwan sa zata zo."

Ita kuma budurwan mai suna Zubaida tace, "zasu ga yanda take ma; idan ta fi ta ne yake mata shan ƙamshi, kuma wlh zai ga wulaƙanci idan ta raina wayon ta."

Ƴan ɗakin sai dariya suke yi

Safara'u na cewa, "ke dai Zuby ban da cika baki sai ta zo muga idanu suna ƙwal-ƙwal don ta fi ki, kin san ƴan Zarian nan akwai iya zaɓen Mata, bare yanda Tariq ya haɗu ko a yanayin sa ma ba kowacce karikitai bane zai iya kulawa."

Suna cikin musun ne kuma suka koma kan abincin da zasu girka kasancewar duk a cikin su an kasa samun masu tashi su ɗaura tukunya, kowa son jiki yayi mishi yawa duk da sun gama tanadar komai hura wuta kaɗai ya rage

Ganin Arab ba ƙaramin shiga taitayin su suka yi ba, don wasu da zummar yin mata shaƙiyanci suke jira. But tun da suka ganta sai suka kama kansu gaba ɗaya don ba wanda zai nuna mata wani abun da ya fi nata, a komai ta kere musu ga kyawunta da ya ɗauke musu hankali, ko a suturan jikinta da yanda take walwali hutu ya zauna mata komai ya ji na surar jikinta; baza ka taɓa cewa ƴar gidan talakawa bane

Laila CE kawai tayi ƙarfin halin yin mata magana, cikin fara'a tace mata, "ta zo ta zauna." Ita da kanta ta kawo mata drinks ta bata

Babu abun da ta sha sai faman yatsina da take yi kamar ta ga kashi, sai ta ciro faskeken wayanta da ya tsole musu idanu sai dannawa take yi tun da ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya

Babu mai bakin magana a cikinsu, tamkar ta kashe musu jiki, kuma babu wacce bata burge a cikinsu ba, daga masu satan kallonta sai waɗanda suka zuba mata idanun ƙura-ratan

While Zubaida sai ta raina kanta sosai don ko kusa baza ta haɗa kanta da Arab ba, ta kerewa sa'ar ta

Laila kuwa sai nan-nan take yi da ita tunda taga kalanta, nan da nan ta soma shige mata har tana tambayar sunan ta?

Murmushi kawai Arab tayi tace mata, "Arab suna na."

"Masha Allah suna mai daɗi, na samu ƙawa gaskiya, zan so ki zama ƙawata don Allah don kin yi min sosai."

"Babu damuwa ai." Ta furta ba tare da ta kalle ta ba

Da haka dai take ta janta da hira duk da ita Arab ɗin ta nuna sam basu a gabanta, maganar ma bai dame ta ba sai taga damar amsa mata, but haka nan take shige mata bata damu ba

Su kansu ƙawayen sai suka soma neman hanyar da zasu shiga jikinta tunda kowa so yake yi ta zama ƙawarta

Babu laifi ta saki jikinta musamman yanda suke ta shishshige mata. Amma dai a yanayin yanda take musu magana zai tabbatar da wulaƙanci da raini a tattare da ita, amma su sam ba sa ganin hakan, a tunanin su don ita ƴar masu kuɗi ne dole ta ja aji tunda class ɗinta ne, musamman da suke tunanin balarabiya ce tunda suka ji sunanta. Har aka gama abinci aka sawo mata ta kasa ci, ƙarshe Laila ta aika aka siyo mata tsire da yoghurt da kayan maƙulashe, ai kuwa ta amshe ta lanɗe kayan ta, da hayaniya ya cika ta komawa wani ɗaki inda Laila ta kaita tayi zaman ta

A can sukai ta waya da Tariq har yake ce mata, "zai kawo mata kayan da zata saka a dinner, but zai shiga super market ɗin zai kira ta video call sai ta duba wanda yayi mata." Har yana cewa, "ko kuma ya zo ya ɗauke ta ta zaɓo?"

But tace mishi, "a'a ba ta jin fita, idan ya je zasu yi videon kawai." Da haka suka yi sallama ta hau WhatsApp suka soma chart da Alhaji Bashir. Shiyasa hankalinta ya ɗauke bata sake fita cikin ƙawayen ba

Duk da ɗakin da take a nan ake yiwa Amarya kwalliya in zata canza kaya, babu mai shigowa sai ita Amaryan da mai kwalliya, sai kuma Safara'u tunda gidan su ne, ita take shigowa ɗaukar wani abun jefi-jefi

Can daga baya kuma sai Arab ta canza shawara ta kira Tariq ta sanar mishi, "ya zo ya ɗauke ta zuwa anjima sai su je ta siyo, daga can hotel zata shirya don ta gaji da zama a nan, baza ta iya kaiwa har dare ba."

Dalilin da yasa ƙarfe biyar da rabi sai ga shi ya zo, ya kira ta ya sanar mata

Bayan ta fito ne take sanar da Laila, "zata tafi."

Laila kamar zata yi kuka tace mata, "baza ta zauna su tafi wajen partyn tare ba? Daga can ne za'a kaita sai su tafi tare ta kwanan mata."

Murmushi Arab tayi tace, "kar ta damu zata dawo insha Allahu, but bata yi mata alƙawarin zata kwana ba amma zata kasance a wajen partyn, yanzu haka jiranta ake yi."

Daga haka suka yi sallama ta rako ta har ƙofar gida ita da sauran ƙawayenta da suke ta shigewa Arab ɗin. A nan suka ga Tariq a cikin motan, sai suka ƙarisa har wajen suka gaishe sa. Sai da suka ga tafiyan su kafin suka dawo ciki suna tsegunta ma Zubaida, "Tariqa ne ya zo ɗaukar ta."

Zubaida duk haushi ya cika ta shiyasa ta bar musu wurin don ta gaji da jin zancen yanda suke koɗa Arab da dacewar ta da Tariq ɗin. Tace, "su bari ba ta so."

Amma sun ƙi bari sai shewa suke yi suna tsokanar ta.

              ******

            Arab kuwa tunda suka fita kai tsaye super market suka wuce, a can ta zaɓo rigan da zata saka a partyn, komai sabo ta siya wanda zata yi amfani dashi, daga nan suka wuce Hotel. Bai jima ba shi ya tafi tunda ana jiran shi, ya ce mata, "zai zo ya ɗauke ta idan an fara."

Tunda ya tafi ta kwanta a saman kujera tana ta chart ɗinta, har ta Kira su Zahra suna ta hira cike da nishaɗi

Sai bayan sallan isha'i sannan ta tashi tayi wanka ta haɗa sallan da ake bin ta ta rama

A lokacin ne Tariq ya dawo yayi musu odan abinci suka ci sannan suka shirya

Arab doguwar riga ne a jikinta light blue, Robber CE kuma tsukakkiya daga sama har ƙasa, hakan yasa ta kama ta ta fito mata da duk surar jikinta da dirinta, babu kwalliya a rigan sai dogon hannu da take dashi siriri, wuyan v ne da ita wadda bakin wuyan aka sanya bakin leshi baƙi, sai tayi using da baƙin takalma masu shegen tsini da igiyarsu, ƙaramin gyale kawai ta ɗaura baƙi shima; sai ta jefa jelan gyalen a gefe da gefe na kafaɗun ta, ana iya ganin kanannaɗaɗɗen gashin kanta irin na Fulani da aka yi mata kitso kuci-kuci ta gaban goshin ta. fuskarta da makeup mai ɗaukar hankali da ya ƙara fito da ainihin kyawun ta, bakin ya sha lipstick tamkar zai zubo, sai ta jefa chewing gum a bakinta

Tunda ta fito sai Tariq ya kasa ɗauke idanuwansa a kanta, ta tafi dashi ainun don daƙyar yake iya haɗiye yawu, sai da ya ji jikinsa yayi wani irin yamm tsigan jikinsa ya tashi tsaye saboda ganin zubin halittan ta da ke kaɗawa, zuciyarsa har hautsinewa take yi yayinda jikinsa na faman rawa ya nufe ta da sauri ya haɗa ta da jikinsa, ɗaura hannu yayi a ƙugunta ya sake matse ta a jikinsa while suna kallon juna ido cikin ido cikin wani irin shauƙi na zallan sha'awa, hannunta ɗaya na a kan ƙirjinsa ta dafa shi. Cikin wani irin yanayi yace, "Baby bazan iya barin ki a haka ki fita ba saboda tsantsan kishin ki da nake yi, kinga yanda kika yi kyau kuwa? Da alamu ina barin ki kika fita zan iya rasa ki don naji hakan a jikina."
Chapter 29 · 0% Book details