← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 52

Sashe 51

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shahy zama tayi tana zame Hijabin jikinta, sai ga ta daga ita sai wata ƙaramar riga da leggings a jikinta, gashin kanta kuma an saka attachment mai kalan ja. "Nima kun ganni ban santa ba, ganinta nayi a waje tana zaune shiyasa nayi mata magana, kuma tace tana buƙatar wurin kwana ne shiyasa na kawo ta. Ki zauna mana ko tsoro kike ji?" Ta ƙare maganar tana kallon Arab ganin har yanzu tana tsaye

Zama tayi ba tare da tace komai ba, tana zaune a kan carpet ɗin ɗakin, while su kuma suna zaune a saman ƙaton katifan da ya mamaye rabin ɗakin

Sai Shahy ɗin tace, "ki saki jikinki babu wanda zai cutar da ke a nan, Ni sunana Shahida, but ana ce min Shahy ko ƴar lalli, wannan kuma Sha'ira, ita kuma wannan Walida, tare muke kwana a ɗakin nan, za ki iya zama har lokacin da kike son tafiya, ke kuma ya sunan ki?" Ta tambaye ta dukka idanunsu a kanta

A taƙaice ta bata amsa, "Arab."

"Masha Allah, shiyasa na ganki kyakykyawa, alamu ya nuna ke balarabiya ce kenan?" Shahy tayi maganar tana murmusawa

Ita kuma sai tayi yaƙe batare da tace komai ba; bini-bini ta bi ɗakin da kallo

Walida ce tace, "amma gaskiya kin san akwai matsala Shahy, Magajiya idan ta san da zuwanta ba tare da an faɗa mata ba zai zama wata fitinar, kin san halinta ai, bare akwai ƴan sa ido duk da ba zama take yi ba zasu faɗa mata."

"Haka ne, zan faɗa mata bari tayi wanka ta canza kaya, kinga tana buƙatar yin wanka kayanta ya ɓaci, idan ta gama sai in je in faɗa mata." Sai ta kalli Sha'ira tace, "ina butar ruwan zafin nan in saka mata ruwan wankan?"

"Ga shi can saman drower." Ta bata amsa tana nuna mata da hannu

Ita kuma ta tashi ta ɗauko tare da fita, sai ga ta ta dawo da ruwan ta jona a socket tunda akwai nepa

Suna ta surutu amma Arab tana jinsu bata ce komai ba, sabida ganin ba ta son magana shiyasa su ma basu sake tambayarta ba, har ruwan yayi zafi Shahy ta sake mata ta kai mata bayin ɗakin. Ita kuma ta shiga tayi wankan

Bayan ta fito Shahy ta bata kayanta tace, "ga shi nan ki saka waɗannan, kiyi haƙuri da yanayin kayanmu; duk da ban sani ba ko kina sa irin su."

"Ba komai." Cewar Arab ɗin tana amsan kayan, riga da wando ne duk da basu kama ta sosai ba kasancewar Shahy ta fita girma da shekaru

Tunda ta saka kayan suke bin ta da kallo sabida yanda suka yi mata mugun kyau, musamman yanda suka sake ganin diri da tsarin halittar ta da ya ruɗa su

"Wow! Gaskiya ke kyakykyawa ce, Allah ya ba ki kyawu, kin burge Ni." Shahy ta furta tana mata murmushi

Itama murmushin tayi sai dai ta ƙi magana

Sha'ira tace, "amma ga shi ba kya son magana, zamu so mu san inda kike, ko kuma mai ya fito da ke daga gida?"

Zama Arab tayi tana kallonsu, sai tace, "Ni ƴar Zaria ce, na zo Kano ne sai kuma wasu mutane suka biyo ni, daƙyar na samu na ceci kaina."

"Allah Sarki! Maybe irin waɗannan ɓata garin ne, koda yake sun ga kyakykyawa." Walida tayi maganar tana dariya

Su ma duk dariyan suka yi ban da Arab ɗin da tayi murmushi

Sha'ira tace, "gwara ki je ki sanar da Magajiya kar wani magulmacin ya riga ki zuwa wurin ta."

"Ai babu wanda ya ga shigan mu ma, ina zuwa bari in je in dawo." Tayi maganar tana miƙewa ta fice a ɗakin. Bata jima sosai ba ta dawo tana kallon Arab da cewa, "taso mu je in kaiki wurin ta, wai zata ganki."

Miƙewa Arab tayi ta bi bayanta suka fita

"Ki saka takalman nan." Shahy ta nuna mata wasu takalma da ke bakin ƙofa

Haka ta zura suka wuce ɗakin Magajiya da ke can ƙarshen gidan. Suna zuwa suka shiga ciki

Wata Mata suka samu a zaune a kan kujera, gabanta kuma da ƙaramin faranti tana zuƙan taba tana kakkaɓe tokan a ciki. Shigowar su sai ta ɗago kai tana kallonsu a kaikaice tana hura hayaƙin bakinta

Arab kuwa tuni ta rufe hancinta da bakinta har ta soma tari; sabida yanda hayaƙin taban ya cika mata baki ya wuce mata ta maƙogwaro, ɗakin gaba ɗaya ya kaure da hayaƙin ko ganin Mutum ba a yi sosai

"Aunty Magajiya ga ta nan na kawo miki ita, kwana ɗaya tace zata yi gobe zata tafi shiyasa na taimaka mata." Cewar Shahy tana kallonta

Hankalinta na a kan taban tana kashewa tace mata, "ta basu wuri."

Fita tayi a cikin ɗakin kamar yanda ta buƙata

Ita kuma Magajiya sai da ta gama kashe taban tana kore hayaƙin da ya gauraye ilahirin inda take, shiyasa ko gani sosai ba tayi, sai da ta gama hure wurin yayi ɗan sauƙi sannan ne ta ga fuskar Arab da ke tsaye liƙe da hanci har yanzu, "ke ce baƙuwar da Shahy ta kawo?"

Shiru tayi mata sabida ta ƙi buɗe hancinta da bakinta da ta liƙe bare tayi magana

Tasowa Magajiya tayi ta ɗage labulen sannan ta dawo kusa da Arab tana ƙare mata kallo, sai ta sanya hannu ta cire mata hannun da ke fuskarta ta sake ganin fuskarta da kyau, ita kanta ta jinjina da ganin kyawun Arab ɗin, musamman da ta kama hannunta ta ji taushi, ko da kallon yanayinta ka san akwai hutu da jin daɗi a tare da ita, uwa uba kyawun da take dashi. Sai ta riƙo ta suka zauna a saman kujera tare da cewa, "amma ke bafulatana ce ko?"

"Eh." Ta amsa mata a taƙaice tana zame hannunta a nata domin ji tayi gabanta na faɗuwa sakamakon tunawa da Jameema, kar ya zo itama Magajiyan haka take shiyasa ta sake ja baya cike da fargaba

Murmushi tayi ita kuma tace, "kar kiji tsoro babu abun da zan miki ai, sai dai zubin ki ya nuna min ke ƴar gidan masu kuɗi ne, babu wahala a tare da ke amma kika fito yawon karuwanci?"

Kallon da Arab ɗin tayi mata ne yasa ta sake cewa, "ko ƙarya nayi ne? Ai duk Macen da kika ganta a nan gagaran iyayenta tayi ta taho nan, ke ma ga shi kin taho da alamu guduwa kika yi daga wurin iyayen ki, dama mun sha ganin ire-iren ku da suke zuwa neman mafaka, daga ƙarshe muna basu wuri shikenan sun zama cikin mu, sai su kama haya mu haɗa su da customers, Ke kuma ga shi kin zo a Sa'a domin yau insha Allahu zan haɗa ki da wanda za ki samu kuɗi ba kaɗan ba, Allah yayi miki diri mai kyau, ko Ni Mace na susuce da kyawun halittar ki bare namiji." Sai tayi murmushi ta kama hannun Arab ɗin tare da cewa, "kar ki wani ɗaga hankalin ki domin ke kyakkyawa ce, na tabbata shigowar ki cikin mu tamkar ɗaukaka ce a wuri na, idan kin amince anjima kaɗan idan ƙarfe sha biyu ta cika akwai wani Soja da zai aiko a ɗauke ki, a rana ɗaya 30k yake ba da wa, kawai buƙatar sa a kai mishi Mace ya kwanta da ita, da asuba zai sallame ki da kuɗinki ki dawo, dama irin ku kyawawa yake so na tabbata zai ji daɗin harka da ke, ƙila ma ki samu kuɗin da ya fi haka daga gare shi."

Shiru Arab tayi ta kasa cewa komai but tunani ne a ranta

Sai Magajiyan ta sake cewa, "kin amince kina bukata ko kuwa? Baza ki samu damar da ya fi wannan ba, in dai irin su ne ina da mutanen nan masu kuɗi da yawa, kuma zan haɗa ki dasu, kin kwanta min a rai shiyasa na ji ina son taimaka miki, daga yanzu ma ɗaki na za ki dawo da zama, zan ɗaukaka ki a gidan nan fiye da yanda kike zato."

Arab gani take yi tamkar dama ce ta same ta, duk da ta raina kuɗin amma a yanzu tana buƙatar su, gwara ta amince idan yaso daga can inda za'a kaita sai ta ƙara gaba, baza ta taɓa dawowa gidan nan ba tunda ita irin zaman gidan Karuwai ba burge ta yake yi ba, hasali ma baza ta iya sharing gida da mutane da yawa haka ba, kuma ba ka da ƴancin kanka kana ƙarƙashin wani sai abun da aka ce kayi, ta fi ƙarfin hakan domin ita ba ƙaramar yarinya bace, tana da kuɗin da zata kama gidan kanta ita kaɗai babu takura, sai dai tana buƙatar kuɗi domin barin garin nan, musamman idan ta tuna babu wayanta bare ATM ɗinta a hannunta, komai yana gidan Senator, sannan bata da damar cire kuɗin ta dole sai ta koma banki domin samun mafita yanda zata iya ciran kuɗin ta.

_Tom mai zai faru? Wacce ƙaddaran kuma Arab zata sake koma wa? Yanzu ne za a fara._
[17/08, 9:43 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

     *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝🏼‍♀️*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA TALATIN*
_______________"Na amince." Arab ɗin ta furta tana kallonta

Murmushi Magajiya tayi tace, "yauwa ko ke fa, bari in ɗauko miki kayan da za ki shirya saboda lokaci ya kusa, babu jimawa za ki ga ya turo a ɗauke ki, kar ki bani kunya kinji ko? Duk da dai kin yi ƙanƙanta amma na san zai ji daɗin ganin ki, don Allah duk abun da yace kiyi mishi ban da gardama, da sannu za ki saba, Shahy zata koya miki komai abun da yakamata kiyi, zan kira miki ita ku tattauna." Sai ta tashi ta fita daga ɗakin

Arab ta bi ta da kallo kamar wata sokuwa, sai kuma tayi murmushi kawai, wai yau ita ce za'a koya wa barikanci da yanda zata tafiyar da naMiji? Sai ta kalli kanta kawai tana mamakin meyasa ta kira ta da ƙanƙanuwa? taɓe bakinta tayi tana lashe ƙasan bakinta

Magajiya tare da Shahy suka dawo tare
Chapter 51 · 0% Book details