← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 52

Sashe 52

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Magajiya tace, "ki tabbatar kin ɗaura ta a hanya kuma kin shiryata da kyau, na san yanzu Soja zai aiko a ɗauke ta."

"To Aunty." Shahy ta amsa mata da girmamawa. Tana fita daga ɗakin sai ta matso kusa da Arab ta zauna tana cewa, "Arab kina sane cewa wurin wani za'a kaiki? Ko dama kin fito yawon Bariki ne?"

Girgiza kanta tayi tana taɓe baki batare da damuwa a fuskarta ba

"To ke da za ki tafi gobe kuma shi ne za'a kaiki wurin wani? Gaskiya rayuwar bariki bai dace da ke ba Arab, ina ganinki tamkar ƙanwata ce domin kin shiga raina matuƙa, zan so ace muna tare da ke a gidan nan amma Ni ban ga amfanin zaman ki a nan ɗin ba, sabida za ki ɓata rayuwar ki a banza ne, kinga mu bamu da inda zamu zauna ne dole sai nan, dukkan mu da kika ganmu yaudaran ɗa namiji yayi sanadin fitowar mu gida, iyayen mu suka kore mu muka shigo duniya bamu da inda zamu je, sai da wannan rayuwar zamu iya kula da kanmu, amma ke kina da iyayenki sannan kwana ɗaya kika ce za ki yi ki tafi, ban san mene Magajiya ta faɗa miki ba har kika yarda da ita, kin amince ki siyar da mutuncinki a kan ɗan ƙanƙanin kuɗi? Kar ƙaramin kuɗi ya ruɗe ki kiyi tunanin zama a cikin mu."

Murmushi Arab tayi wanda har haƙoranta suka bayyana, maganar Shahy ɗin ne ya bata dariya, inda ta san ita wace ce da bata zauna tana mata wannan ɗan guntun nasihar ba, tun tana ƴar shekara sha biyar ta siyar da mutuncinta, a bariki babu kalan iskancin da bata iya ba, idanunta a buɗe suke sosai fiye da zaton mutane, ita iskancin nata ma ba kalan nasu take yi ba domin sheɗanantan ta ya wuce nasu

Shahy ganin tana murmushi sai tace, "kamar ba ki damu da maganar da nake miki ba, duk da ban san ko ke wace ce ba amma alamu ya nuna min kamar ba ki san komai a harkan nan ba, kar daga taimako na jefa ki cikin bala'i sabida bazan so ta sila na ki shiga bariki ba."

"Kar ki damu babu wata cutarwa a gare Ni, ina buƙatar kuɗin ne domin akwai abun da nake so in Yi dasu, kuma sai ta wannan hanyar kaɗai zan iya samun su." Arab ɗin ta furta mata still tana mata murmushi

Shahy tace, "idan kuɗi ne zan ba ki in har baza ki jefa kanki cikin matsala ba, kuɗin komawa garin ku ne ba ki dashi ko mene?"

Girgiza kanta tayi tace, "a'a ba kuɗin komawa garin mu nake buƙata ba, zan...."

Shigowar Magajiya cikin ɗakin ne yasa Arab tayi shiru suka bi ta da kallo

Ita kuma tace, "ya naga kuna zaune ba ki shiryata ba Shahida? Wannan wanne irin iskanci ne bayan kin san yanzu za'a aiko a ɗauke ta? Maganar ne baza ku iya yi kina shiryata ba sai kun zauna?"

"Kiyi haƙuri Aunty yanzu zan shiryata." Shahy ta furta da sauri tana tashi

"To kuyi sauri ga shi nan ma har ya zo." Tafaɗa tana amsa kiran da aka yi mata a waya, basu ji mai aka ce mata ba sai tace, "ka ƙara haƙuri yanzu zata fito, tana shiryawa ne."

Riga da wando ne sababbi Arab ɗin ta saka, kasancewar kayan Robber ne duk sun ɗame mata jiki, gashinta kuma an gyara mata shi tare da kama mata da ribom, Shahy tayi mata light make-up sannan ta yafa siririn gyale, ko ina na jikinta sai da Magajiya ta bi ta shafa mata turare. Tamkar wawuya haka Arab take bin su ba ta cewa uffan, komai su suka yi mata har suka gama aka bata takalma ta saka

Sannan Magajiya ta ja hannunta suka fice. Cikin gidan shiru sabida kowa ya kwanta a yanzu, duk da wasu ɗakin sakayo ƙofa suka yi amma ba a jin motsin komai kasancewar dare ya ratsa, haka ma waje babu kowa sai haushin karnuka

Motan da aka zo ɗaukar ta tana can nesa da gidan kasancewar wurin lungu ne baza ta shigo ba. Shima Drivern da alamu soja ne domin kayan jikinsa kakin aiki ne, shi ya buɗe mata bayan motan ta shiga sannan suka tafi

Sai da Magajiya ta ga tafiyansu sannan ta koma cikin gidan ta rufe ƙofan

Su kuma tafiya suka yi ɗoɗar a kan titi. Ko tsoro Drivern ba ya ji domin babu wani halitta a waje, maybe don shi soja ne shiyasa, sannan Ogan nasu babba ne shima a soja babu ruwansa duk sanda yake buƙatar Mace a daren za'a je a ɗauko mishi ita, babu ruwan su tunda jami'ai ne su ma bare a tsare su

A wani babban gida ya dakatar da motan yayi horn. Aka buɗe masa Gate sannan ya shige ciki

Arab sai kalle-kalle take yi tana ƙare wa gidan kallo, domin babu ƙarya gidan ya burge ta, ko da gani mamallakin sa yana da kuɗi gaskiya, ya haɗu sosai gidan domin tamkar ginin Turai aka mishi, flat ne mai faɗi. Ba ka jin ƙaran komai a gidan sai kukan tsuntsaye ko ina akwai flowers, har da bishiya da irin masu bin gini kamar macizai. Akwai jami'an tsaro a haraban gidan kowanne riƙe da bindiga suna ta zagaye

Drivern shi ya buɗe ma Arab ƙofan sannan yayi mata jagora har cikin makeken Falon. Suna shiga ya nuna mata wani ƙofa yace, "ki shiga wancan ɗakin yana ciki, sannan kar kiyi wani abun da zai sa mu kama ki, kowanne wuri akwai Camera CCTV; abun da ya kaiki kawai shi za ki yi, ba ma son shishshigi, zuwa asuba zan zo in buɗe miki ƙofa ki bar gidan."

Har ya gama maganarsa bata ce komai ba; sai kallonsa da take yi kamar ta samu t.v

Shi kuma ya juya ya tafi batare da ya damu ba, domin shima ba ya son yayi wani abun da zai yi laifi a wurin Ogan su. Umarnin da yake ba shi kenan ya ɗauko Mace ya kuma kawo mishi ya fita

Rufe ƙofan da yayi ne yasa Arab ta ɗauke ido a kan ƙofan, tare da taɓe bakinta ta soma bin ko ina da kallo. Ta ɗan ɓata lokaci a wurin tana ƙare ma falon kallo, kana ta nufi wurin fridge da ta hango, buɗewa tayi ta ɗauki ruwa a ciki ta sha, sai da ta sha sosai kafin ta rufe ta mayar ta nufi ɗakin kanta tsaye cikin tafiyarta na jan aji. Ƙofan ta murɗa ta ji ya buɗe, sai ta zura kai ciki kawai ba tare da tunanin wani abu ba.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT

This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels
Chapter 52 · 0% Book details