← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 52

Sashe 34

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daƙyar ya samu ta haƙura tace, "zata zauna. Amma duk ranan da ya sake gaya mata makamancin irin wannan maganar wlh sai ta bar gidan sa, dama ta ɓoye mishi irin ƙaunar da take mishi ne sai a wannan ranan zata bayyana mishi, amma kuma sai ga shi yana zargin ta don kawai ta ba shi haɗin kai wajen jiyar da shi daɗi, to idan ba ta ƙaunar shi taya zata amince ta aure shi? Duk samarinta ace shi kaɗai ne zata iya nuna wa wanda zata aura; duk wannan ba so bane?"

"Wlh na yarda Sahiba, na yarda kina matuƙar ƙaunata, yau na gane haka, tunda Ni kaina ina ta mamakin ya aka yi kika zaɓe ni a cikin dubu duk da irin halin da kike nuna min? ba ki taɓa bani dama ko na minti biyar ne mun yi magana da ke ba, kullum cikin hantara na kike yi, Ni kuma na ƙi yin zuciya na kafe sai ke, duk da na san cewa kin fi ƙarfi na amma gani nake yi kamar wata rana za ki zama rabo na, ashe hakan ne kuwa tunda ga shi Allah ya nuna min wannan ranan, wlh Zainab ban taɓa tunanin kina so na ba sai yanzu, ashe duk da gangar kike yi min haka?"

Dariya tayi masa tana sake shigewa jikinsa tare da ɓoye fuskarta, cikin nuna kunyarta tace, "Ina sonka Ya Sheikh, sai dai na kasa nuna maka hakan ne saboda in gano irin soyayyar da kake min, amma duk abin da nake maka wlh da sani na nayi maka, kuma ga shi yanzu na goge maka tantamar ka, na zama taka yanzu."

"Godiya ga Allah maɗaukakin Sarki." Ya furta cike da farin ciki yana sake rungume ta, "na ji daɗin wannan rana Sahibata, bazan taɓa manta wa da wannan karamcin da kikai min ba, kuma zan nuna miki Ni masoyin ki ne na gaskiya, Allah ya bar mu tare."

"Amin." Ta furta tana dariya, yayinda cikin zuciyarta farin ciki da hamdala take yiwa Allah da ya rufa mata asiri, har ga Allah a yau ne take jin zuciyarta tayi sanyi da tsanar Ya Sheikh, har tana jin cewa zata iya zama dashi har ƙarshen rayuwarta, kuma baza ta sake aikata makamanciyar rayuwar da tayi a baya ba, haƙiƙa Allah na sonta tunda ya rufa mata asiri ya bata Ya Sheikh a matsayin Mijinta, don haka dole ne ta gode masa, ba don haka ba ta san da tuni a yanzu suna tsiya da mijin ko kuma ya sake ta a kan abun da tayi na rashin zuwa da budurcinta, gwara da Allah yasa bata auri sauran Samarin da take bi ba; Allah ya musanya mata da Ya Sheikh, ga shi a yau kaɗai ya shayar da ita farin cikin da bata taɓa sanin zata samu daga hannun sa ba, har ta fi jin gamsuwa ɗari bisa ɗari fiye da sauran ranakun da ta aikata sauran masha'an ta, kuma daɗin da ta ji ya fi na kowanne namiji da ta sani

Shi kuwa Ya Sheikh tunda ya ga ya shawo kanta sai ya ja ta suka koma ciki, sai da suka ƙara shayar da junan su daɗi before suka kwanta rungume da juna cikin tsantsan farin ciki a ransu.

             Bayan kwana biyu da auren ne su Malik suka wuce New York, a can ne zasu yi Honeymoon ɗinsu, daga can kuma zasu sake zaga wasu ƙasashen, basu da matsalar komai tunda a Campanin Mahaifin Malik suke aiki.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           Yau su Arab suna zaune a tsakar gidan su, Inna ta fita zuwa PZ canzo fridge; tunda wanda suka siya yayi ƙarami shi ne Arab ta bada kuɗi tace, "a canza babba zai fi."

Su uku ne kaɗai a gidan a yanzu, Zahra da Arab suna bakin bishiyar gidansu suna hira. While Ummu tana kwance a ɗaki barci ya sure ta tun sanda suka dawo school ita da Zahrah. Labari suke yi a kan saurayin Zahran; Haidar wanda yake ƙasar waje yana karatu, ita Zahra abun ya soma damunta kasancewar tayi masa alƙawarin baza ta taɓa bari wani ya kusance ta ba bayan shi, ga shi tunda ya tafi ya ƙi dawowa, kuma yanzu lamarin yana son ya zame mata matsala tunda a yanzu dai tana matuƙar buƙatar namiji tunda ya ɗanɗana mata abun da ake ji, duk da tana rage zafi da samarin ta amma ta kasa ba wa kowa damar da zai kusance ta idan ba Haidar ba

Shiyasa yanzu Zahra tace, "gaskiya ita ta gaji wlh aure take so, tayi-tayi Haidar ya dawo suyi aure amma ya ƙi, ya zata yi dashi ne?"

Arab kuwa dariya tayi tana cewa, "ke wlh banza ce, meye na wani jiran Haidar ya tafi can ya manta da ke? Ke kin san me yake yi ne a can? Ni ban taɓa ma tunanin ke sakarya bace idan ba yau ba."

"Ni kike kira sakarya?" Zahran ta furta tana ban ka mata harara

"To idan ba sakarya ba mece ce?" Arab ɗin ta sake cewa tana ware mata idanu da dariyan shaƙiyanci, "kinga fa, Ni ba na tunanin wannan Haidar ɗin zai iya auren ki wlh, kwata-kwata zubin shi na ƴan yaudara ne, zai ci moriyar ganga ne kawai ya yasar da kauren ta, to ban da abun ki ma meye na tunanin aure yanzu? Na san dai abun da kike buƙata bai wuce ɗa namiji ba, kuma kina da su sai wanda kika zaɓa ya jiyar da ke daɗi. But you are still talking about Haidar and you are not sure if he will marry you or not."

"Hmm Arab kenan! Baza ki gane bane, wlh ina matuƙar ƙaunar Haidar, idan ba shi ba ba na jin zan iya auren wani namiji a duniyar nan, sai dai Mutum ɗaya da nake tunanin a cikin su idan na same su tabbas na more, har ga Allah har a cikin zuciyata ina son in Yi rayuwar aure da su."

Arab tace, "Ok kina ma da wani bayan Haidar ɗin kika zauna kina jiran sa? Kin san fa irin gidan Sarautar nan wlh ba lallai su amince da ke ba, ko shi yace zai aure ki iyayen sa baza su yarda ba, tunda zasu ce za'a ɓata musu gida ne, bare kin san yanda muka yi tambari a anguwan nan, ana zuwa za'a basu shedar duk wani halayyar mu, shawaran da zan ba ki kawai ki bar shi ki nemi ɗayan; don na san zai ɗan fi gwaɓi-gwaɓi a kan Haidar."

"That's what you think, bayan shi wannan ɗin ban ma san inda zan same shi ba, ban san komai a kanshi ba, maganar ma da nake miki bai ma san ina yi ba."

Sakato Arab tayi tana kallonta, sai kuma ta kawar da kanta tana ƙoƙarin soka earpis a wayanta tare da cewa, "To wannan kuma daga ina kika samo shi?"

Sai da ta buga tagumi kamar zata yi kuka tace, "ina wannan Likitan Abokin Nafi'u Mijin Aunty Firdausi? wanda muka je asibiti muka haɗu da shi a Office ɗin Doctorn nan?"

Da sauri Arab ta ɗago kanta tana kallonta, yayinda ta furta, "wai shi kike so?"

"Eh. Shi zuciyata ta mutu a ƙaunar shi, Ni kaina wlh mamaki nake yi sabida yanda na kasa manta fuskarsa, abun da nake ji a kan Haidar haka shima nake ji a kanshi, tunani na da burina kawai in ganshi a yanzu, abun farin cikin kuma sunan su ɗaya..."

Dariyan da Arab ɗin ta kwashe dashi; shi ya tsayar da ita daga zancen da take yi. Yayinda ta furta, "haukan Banza, wai wannan Mutumin kike so Aunty Zahra? Ki rasa wanda za ki so sai shi? Amma gaskiya zuciyar ki bata yi miki adalci ba, shiyasa kwata-kwata na tsani soyayya don na san abun hauka yake zama." Sai ta ƙare maganar tana dariya sosai; yayinda ta sanya earpis a kunnenta tana ƙoƙarin latsa wayan da cewa, "to yanzu aina za ki ganshi kenan?"

Shiru Zahra tayi mata tayi banza da ita

Sai ta ɗago ta kalle ta tana cewa, "ya na ji kin yi shiru?"

"To ba dole in Yi shiru ba kin mayar da zance na wasa? I'm telling you my problem but ke kamar bai dame ki ba."

Murmushi tayi tare da zare guda ɗaya earpis ɗin a kunnenta tana cewa, "to na ji, na dena dariyan, amma maganar taki ce akwai ban dariya da kayan haushi, wannan mutumin wlh ba shi da mutunci ko da ganin shi, sannan ma kin san inda muka haɗu dashi taya kike tunanin zai so ki?"

"Leave this conversation alone; tunda dukkan mu bamu san shi ba."

Dariyan rainin hankali Arab ta saki tana cewa, "ke ce ba ki san shi ba, amma Ni kallo ɗaya na gane waye shi, ba kalan Mazan nan da kike tunanin za ki samu cikin sauƙi bane, ban ba ki labari ba ma? Zuwana Abuja da nayi sai da muka haɗu a wani ShopRite."

Zahra cike da ɗoki tace, "haba dai? Don Allah da gaske?"

"Zan miki ƙarya ne?" Arab ɗin tafaɗa tana hararanta

Kafin Zahran tayi magana; suka ji sallaman Yaro yana ta kwaɗawa ko jingirta wa ba yayi

Hakan ne yasa Arab ta ƙunduma mishi zagi tana cewa, "dan uwarka ba kaga mutane bane kake mana ihu aka? Uwar me ka zo yi?"

"Wani ne ya aiko Ni a waje, wai ana kiran Arab."

Arab tace, "wane ne? Kuma a me ya zo?"

"A mota ne."

"Ok. Je ka kace ga Ni nan."

"To." Ya amsa da sauri yana juyawa
Chapter 34 · 0% Book details