Sashe 18
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Ayya dama nayi tunanin haka, shiyasa nace ku hau jirgi da wannan wahalar, to yanzu ga shi kun samu matsala sai shigan dare yanzu zaku yi, yanzu da karfe tara ta wuce ko zaku samu wajen kwana ne Malik ba na son tafiyar daren nan?"
"No Mummy mun kusa, ki ajiye wayan zan kira tunda ina tuƙi." Ya furta yana zare wayan daga kunnen sa, bai jira abun da zata ce ba ya kashe ya ci gaba da tsula gudu a kan kwalta. Bai sake kallon inda Nawwara take ba balle ya saurare ta
Itama sai ta share shi tana cin magani tunda ta san ba laifi tayi ba, ai ya san halinta a kan kishin sa babu abinda baza ta iya ba, abun baƙin cikin nata ma yanda yake tambayar Zahra number wato yaga kyakykyawa shiyasa yake son ƙulla alaƙa da ita, ina ai baza ta taɓa bari ba, gwara da tayi musu haka bazai taɓa samun wannan damar ba.
********
Ita kuwa Zahra chemist ta wuce sabida yanda jininta ke zuba sosai, ga azaban zafi da yanzu ya addabe ta, shiyasa ta je aka yi mata treating wajen, dama kuɗi ta je ciro ma Innar su da za'a siya fridge dashi, sai kuma ga abun da ya faru, ƙarshe ma sai ta account ta biya me Chemist ɗin ta wuce gida tunda babu kuɗi a tare da ita
Tana zuwa Inna da Ummu suka ga bandage a kanta suka hau tambayar ta hankalinsu a matuƙar tashe
Tsaban takaici ma Zahra ta kasa yin magana, sai da suka ishe ta da tambaya sannan ta sanar musu abun da ya faru
Ai kuwa tana rufe baki Inna ta hau ruwan bala'i, haka take zagin Nawwara ta uwa ta uba tana ƙunduma mata zagi, tace ma Zahran, "su koma wajen ko zasu ga matsiyaciya wlh sai taga uban da ya tsaya mata, sai tayi Shari'a da ubanta tunda ta taɓa ta."
Zahra tace, "ba na tunanin za'a same su Inna don sun rigada sun tafi."
"Ai duk da haka sai mun je, sai naga uban da ya tsaya mata, tashi maza muje ki kaimu wajen, ƴar iska matsiyaciya dan ubanta mu zata nuna ma hauka? Gidanta ta zo yau sai na kakkarya matsiyaciya inga uban da ya tsaya mata." Haka Inna ta tasa Zahra har Ummu suka fito suka tafi kasuwa inda abun ya faru. Sai dai koda suka je basu same su ba amma haka Inna take ta ruwan bala'i tana jifan su da alkaba'i har Malik ɗin, a cewar ta, "dama shi ya kawo ta don ta bugar mata ɗiya, da sun tsaya da sun gane shayi ruwa ne, Allah ya so su, amma duk ranan da tayi tozali da yarinyar komin daɗewa to Zahra ta sanar mata sai ta ɗauki mummunan mataki a kanta."
Haka suka dawo gida Baba na tambayar inda suka je; don ya dawo bai same su ba shiyasa yake tambayar su
Inna sai surfa bala'i take yi tana cewa, "to ko na faɗa maka mai zaka iya yi a ciki? Ga ta nan Zahra CE wata matsiyaciyar la'ananniyar yarinya da uwarta ta haife ta ba ta hanyar sunna ba; ita ta fasa mata kai, ai naso in same ta wlh da sai naga uban da ya tsaya mata, ƴar iskan yarinya kawai har ita ta isa ta fasa ma yarinyata kai? Ai kuwa ta tono tsuliyar dodo don wlh jafa'i da masifa sai ya ƙare mata, sai nayi ta jan mata alkaba'ai yana ƙare mata, in Allah ya yarda sai taga masifa da bala'i dan uban ta..."
"Haba don Allah Harira ki sarara haka mana, mene ne haka ke ba ƙaramar yarinya ba? Kin tambayi ita Zahran ta sanar miki mai ya haɗa su ne haka kawai za ki yi ta zagin yarinya? Komai ai ɗan haƙuri ne mene ne a duniyar? Duka-duka nawa take? Kuma tsautsayi babu inda ba ta faɗawa..."
"Eh dama ai haka zaka ce, shi tsautsayin dan ubanshi bai san inda zai faɗa ba sai a kan yarinyata? Kuma wancan Shegiyar ce zata fasa mata kai? Dama na daɗe da fahimtar ba ƙaunar yaran nan kake yi ba, da Allah Malam idan baza ka iya taimaka mana da komai ba kayi min shiru don ba na son wa'azinka na banza ƙara tunzura Ni yake yi."
"Allah ya ba ki haƙuri." Baba ya furta yana yin gaba ya shige ɗakin sa
Haka Inna tayi ta masifa Ummu na taya ta don sun ƙi haƙura da zancen sam, sai da suka gaji don kansu sannan suka sarara
Ita kuwa Zahra takaici da baƙin cikin abun da Nawwara tayi mata duk sun hana ta saƙat; ko magana ta kasa yi, tana jin dama ace zata sake ganin Nawwara, uhm wlh sai ta kwantar da ita don ita nata mai sauƙi tayi mata, Chemist kawai ta je, but ita gadon asibiti za'a kaita, kuma ƙarshe sai ta ƙwace Malik ɗin a hannunta taga ƙaryan hauka, baƙin cikinta ɗaya bata san inda zata same su ba, ta cije yatsa ya kai babu adadi, da ace ta ba shi Numbanta da shikenan.
✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️
*ABUJA STATE*
Arab ta isa Abuja wajen gabanin magriba, sai ga Drivern Alh. Bashir ya zo ya ɗauko ta ya isa da ita hotel ɗin da Alh. Bashir yake zaune, kasancewar shima kasuwanci ne ya kawo shi nan Abuja but asalin shi ɗan Bauchi ne, a can iyalansa suke zaune but yawon gari-gari yake yi sabida harkan business ɗinsa, har ƙasashen ƙetare yana fita
Alh. Bashir irin mutanen nan ne masu son Mata, har kawalai yake dasu waɗanda suke kawo mishi mata don kawai ya ji daɗi dasu, Matarsa ɗaya da yaransa biyu duka maza. Kasancewar matarsa ta mallake shi shiyasa ya kasa yin mata kishiya; but yana bin matan Banza a waje
Tun da yaga hotunan Arab ya susuce da kyawun ta, ya gaza haƙura shiyasa ya buƙaci, "ta taho nan ta same shi." Daga shi sai Drivern sa wanda ya san sirrin sa shiyasa ya aike shi ya ɗauko ta
Yana kawo ta hotel ɗin ya nuna mata Numban ɗakin da Alh. Bashir yake ciki, ta buɗe ta shiga tana bin ko'ina da kallo, nan idanuwanta suka sauka a kan Alh. Bashir ɗin da ke zaune a saman sofa daga shi sai gajeren wando
Ƙaton Mutum ne don a shekaru zai haura sittin da biyar, Allah yayi mishi jikin girma don lukutete ne, ga shi baƙi babu zubin kyau ko kaɗan a tare dashi, tamkar wani basamude haka yake sai ƙaton tumbi a gaba. Yana ganinta nan da nan ya washe baki tare da miƙewa yana isa wajen ta, hannu yasa ya kamo nata a hankali ya janyo ta ya haɗe ta da jikinsa yana cewa, "welcome My Baby, sannu da zuwa, kin sha hanya."
Murmushi tayi ba tare da ta furta komai ba illa tunanin yanayin Mutumin da take yi a ranta; da kuma yanda zasu kwashe. Yanda ya matse ta a jikinsa ne yasa ta ɗan ɗaga kai tana ƙoƙarin janye jikinta
Hakan yasa ya sassauta mata riƙon tare da riƙe mata hannu gam ya wuce da ita saman kujera, sai da ya zauna sannan ya zaunar da ita a gefen shi yana washe baki cikin murna, "sannu da zuwa Baby; gaskiya ban taɓa tunanin kyawunki ya kai haka ba sai yanzu da na ganki a fili, kina da kyau Baby kin haɗu." Hannu yasa ya shafa fuskarta sai yace, "bari in Yi miki odan abun da za ki ci na san kin gaji, ki soma yin wanka before a kawo miki abinci, what do you want to eat?"
Farr tayi da idanuwanta cike da salon burgewa, tana ɗan yatsina fuska tace, "Whatever is brought I will eat."
"Ok to bari in kira waya." Yayi maganar yana tashi da sauri ya nufi wajen telephone, ɗaukowa yayi ya dawo ya zauna a inda ya tashi yana kiran wayan, babu jimawa suka ɗauka yayi odan abun da yake so su kawo mishi, daga nan ya ajiye wayan yana kallonta fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Are you going to take a shower now before you are brought in?"
Bakinta ta tura gaba tana mishi wani irin kallo me shiga jiki, tare da gantsaro ƙirji cikin jan hankali tana zare gyalenta, a hankali ta miƙe tsaye tana cewa, "ina ne toilet ɗin?"
Jikin sa na rawa ya miƙe yana cewa, "mu je in nuna miki." Yayi gaba ta bi bayan shi tana sake kallon ko ina har suka shiga cikin bedroom
Nan idanuwanta suka faɗa kan damin kuɗaɗen da suke ajiye a saman gado a cikin wani ƙaramin jaka, an barbaza su da alamu ƙirga su yake yi, nan da nan zuciyarta tayi wani fari idanuwanta suka fito waje, haka take zazzare su a kan kuɗin cikin farin ciki a ranta, har wani lanɗe baki take yi ta shagala da kallon kuɗin sabida tsaban taga abun da ke faranta mata, masu kuɗin rana kenan, masu sanya Arab shiga shauƙi, a duniyar nan babu abun da ke faranta mata, babu abun da ke saka ta cikin tsantsan farin ciki da walwala irin kuɗi, tana son kuɗi fiye da komai, zata iya yin komai don su, su kaɗai ne soyayyarta, babu abinda take yiwa biyayya sama dasu
Sai da Alhajin ya juyo yana kallonta don har ya kai bakin toilet ɗin ya buɗe mata ƙofa, sai ya juya ya ga bata biyo shi ba, nan ya hange ta tsaye idanuwanta na kallon wajen gadon shi, sai yace, "Baby taho mana, me kika tsaya yi?"
Da sauri ta dawo cikin hayyacinta tana wayancewa ta ɗauke kanta tana kallonsa; sai ta saki wani malalacin murmushi wanda iyakan shi saman laɓɓanta, har wani sanja tafiya tayi wajen ƙarisowa wajen sa tana wani rangwaɗa kamar zata karye
Lokaci ɗaya kuwa ta janye hankalinsa sai ɓashe baki yake yi, ya kama mata hannu suka shiga toilet ɗin ya haɗa mata komai na ruwan, sai kai mata cafka yake yi sabida ganin har ta cire kaya a gaban shi, ya kasa jurewa ya soma ƙoƙarin shige mata yana shafa ta