← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 52

Sashe 11

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

                   Sai da aka kira sallan magriba sannan suka rabu. Ta tafi ta bar shi ya sake wanka sannan ya wuce masallaci, lokacin ma har an idar da sallah. Daga can ne suka haɗu da Sinior suka wuce club.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

           *KADUNA STATE*
          Ranar Asabar sai ga su Ummu sun zo kamar yanda suka yi alƙawari, wajen ƙarfe goma na safe yayi musu a gidan Firdausi

Lokacin ma Nafi'u yana nan bai fita ba, sai da suka gaisa sannan ya fice. Bai jima ba kuma ya dawo musu da siyayyan da yayi musu na kayan abinci, sai fruits ya ajiye musu ya koma

Firdausi tayi murnan ganin su ba kaɗan ba, har ƙwalla tayi a ɓoye don babu abun da ya fi mata ƴan uwanta daɗi, a haƙiƙanin gaskiya sun shaƙu matuƙa a lokacin da take gida. Sai dai kuma tun sanda suka soma zama ƴan mata ne ta gane ƙudirin Innarsu a kansu shiyasa ita Firdausi ta sauya ta nuna, "sam baza ta iya yin irin wannan rayuwar ba." Dalilin da yasa Inna ta tsane ta kenan, komai a sha'anin gidan ta cire ta tamkar ba ita bace babba, hatta da ƙanninta ta so ta shiga tsakanin su sai dai kuma akwai ƙaunar junansu, dalilin da yasa basu biye mata ba kenan suna mu'amala da Yayar tasu sai dai ba kamar baya ba, kuma ba wai bata girma suke yi sosai ba, tunda ko faɗa tayi musu a kan rayuwar da suke yi tana son ta nuna musu hanyar da Innarsu take ƙoƙarin tura su ba mai kyau bane, da yiwuwar zasu iya samun matsala, amma sam ba sa jinta, wani lokacin ma sai su kai ƙaranta wajen Inna, ita kuma ta kama ta ta jibga banza, haka Firdausi zata yi kuka ta share hawayenta babu mai rarrashin ta idan ba Baba ba.

          Ummu da Arab suka yi musu girki, kasancewar Arab tana ƙaunar cooking shiyasa ta shiga suka yi tare. Shinkafa da miya suka yi tare da nama da Nafi'u ya fita ya siyo musu, sai suka yi juice kala biyu

Basu gama ba Arab ta fita ta bar wa Ummu ƙarison. Tana shiga ɗakin Firdausi ta hangi Zahra na zaune ita kaɗai ta buga tagumi, sai ta nufe ta ta zauna a gefen ta tana cewa, "Aunty Zahra tunanin me kike yi ne haka?"

Ɗan ɗago kanta tayi tana jan numfashi, fuskarta ɗauke da damuwa ta kalle ta tare da cewa, "wlh akwai abun da ke damuna ne."

"To faɗa min mana in abun da zan iya taimaka miki ne." Arab ɗin itama tayi maganar tana tsira mata ido

Shiru ta ɗan yi na tsawon daƙiƙu before tace, "yau kimanin wata biyu kenan ban ga period ɗina ba Arab..." Sai tayi shiru kuma ta kasa ƙarisawa

Arab da ko ƙyafta idanu ba tayi a kanta sai tace, "uhm ina jinki, to sabida me kenan?"

"Ke ma kin sani an samu matsala wlh, na rasa wanda zan sanar mishi domin na tabbata ciki ne dani, wlh ina jin tsoro duk hankalina ya gama tashi."

Dariya ne ya ƙwacewa Arab har da tafa hannaye tana ware manyan idanunta sosai a kanta, tare da cewa, "wai kina nufin kin ba wani ƙaton banzan jikin ki Aunty? To kin san da zuwan wannan ranan meyasa ba ki ɗauki mataki ba? Wannan ai ganganci ne."

Hannayenta ta cire daga tagumin da tayi tana tamke fuska da cewa, "ba na son iskanci fa Arab, shawara na zo ki bani tunda naga wannan harkan naki ne ba nawa ba, nima akasi aka samu shiyasa amma wlh ban yi tunanin zan samu ciki ba."

Wani dariyan ta tuntsire dashi har da ɗaura hannu a kan bakinta, but dariyan ya ƙi tsayawa, sosai take mata dariyan mugunta har da hawaye

Wanda hakan ne ya fusata Zahra tace, "Wai ke meye haka? Wanne irin wulaƙanci kike min? Ba na son iskanci fa wlh, nayi dana-sanin sanar da ke sirri na, a tunani na ke ƴar uwata ce za ki rufa min asiri amma kuma kin zauna kina min dariya."

Daƙyar a yanzu ta tsayar da dariyan da cewa, "to naji kiyi haƙuri, amma fa baza ki hana Ni yin dariya ba tunda dai baki na ne ba naki ba, abun naki ne da ban dariya, kina son daɗi amma ba ki shiryawa zuwan wannan ranan ba...." Shiru tayi sabida ganin Zahran ta miƙe zata fice, sai tayi saurin riƙe mata hannu tana murmusawa tace, "i said sorry ha'a, ki zauna sai muyi magana, yanzu ya kike so ayi?"

Tsaki ta ja tana hararanta, kuma bata ce komai ba sai ta dawo ta zauna ɗin tana kumbura fuska

"Ina sauraron ki sanar dani?" Arab tayi maganar tana ɗaura hannunta ɗaya a haɓarta

"So nake yi in zubar dashi kafin mu koma gida, yanzu ki raka Ni muje tunda ke kika san yanda ake yi sai mu zubar don Allah."

Arab tace, "Ni kar kiyi min sharri fa, taya za ki ce na san yanda ake yi? Ko na taɓa ce miki na ɗauki ciki ne?"

"A'a ba ki ce min ba, Please be patient but help me."

"Okay fine." Ta furta tana ɗage kafaɗa tare da taɓe baki, sai kuma tace, "Let's finish eating and go to the hospital."

Daga haka suka bar zancen. Arab tashi tayi ma ta fice zuwa kichen ɗin

Lokacin har Ummu ta jera komai a tsakar Falon. Suna tare da Firdausi da ta fito wanka a ɗakin Nafi'u, ta zo ta zauna Ummu ta zuba mata abinci

Zahra itama fitowa tayi duk suka haɗu suka ci abincin suna ta hira suna dariya, abun gunun sha'awa idan ka gansu sabida yanda suke gudanar da rayuwar su, baza ka taɓa cewa ƴan ɗaki ɗaya bane domin tamkar ƙawaye haka suke yi, bare kuma dama ba wani tazaran girman jiki ne dasu ba, duka kansu ɗaya yanzu, har Arab ta kamo su a tsawo sun koma kai ɗaya, sai dai Firdausi ce yanzu da tayi ƙiba tunda tayi auren nan, but dukkan su ba wani jiki ne dasu ba sai diri da Allah ya basu. Shiyasa suka taso cikin shaƙuwar junan su, basu da ƙawaye sai junan su, basu yarda wata ta shigo rayuwar su ba sai dai zaman mutunci da suke yi da jama'a, ko kuma classmates ɗinsu, kuma ba kowanne suke sakar mishi fuska suyi ƙawance da su ba sai ƴaƴan masu kuɗi, don haka zai yi wuya kaga suna mu'amala da yaran talakawa a ganin su sun wuce ajinsu kamar yanda Innarsu ta koya musu wannan ɗabi'ar

Sau tari tana sanar musu da cewa, "su ba sa'annin yaran nan na talakawa bane, sun fi ƙarfin su sun wuce da ajinsu, don haka su sai ƴaƴan manya, su yakamata suyi ƙawance da su, kar ta ji kar ta gani." Wannan shi ne huɗubar ta a ko yaushe, kuma a haka suka taso don gani suke yi sun fi ƙarfin kowa.

          Sai da suka gama cin abincin suka yi sallah, sannan suka shirya Arab tayi wanka tunda bata samu tayi ba sai yanzu da zasu fita. Su dukka biyun shigan baƙar Abaya suka yi, iri ɗaya ce sai dai kwalliya da ya bambanta su, suka yi Rolling da gyalen shi, kana kallon su zaka san ƴan gida ɗaya ne tunda ga kama nan tsagwaronta, sai dai ita Arab duk ta fi su hasken fata ne da kyawu

Suna fitowa Firdausi tace, "Ah ah ina zaku je kuma?"

Zahra CE tace, "aunty ba daɗewa zamu yi ba, zamu ɗan je wani waje ne."

"To ina ku ka sani a nan; kar fa ku je ku ɓace? Arab ke ma da ba ki fita ko nan da can ba taya zaku san gari?"

"Shiyasa ai zamu je mu sha iska yanzu, kinga Aunty ba daɗewa zamu yi ba yanzu zamu dawo." Arab tayi maganar tana gyara agogon hannunta da ta gama ɗaurawa

Ummu tace, "shi ne dan wulaƙanci baku sanar min ba in shirya mu tafi tare?"

"Kuma yanzu ba jiran ki zamu yi ba tunda mun shirya, Aunty Zahra, let's go. Please don't waste time." Sai ta ɗauki jakarta a kan kujera da ta ajiye tana yin gaba

Sallama Zahra tayi musu ta fice ta bar Ummu tana ƙorafin abun da suka yi mata, bata ma tsaya ta saurare ta ba tunda taga Arab ta fice

Kai tsaye titi suka nufa suka samu abun hawa. Suka faɗa mishi, "ya kai su asibiti mafi kusa da nan."

Yace, "ai suna da yawa asibitocin, amma na gwamnati ko na kuɗi wanne kuke so?"

Arab tace, "kai mu na kuɗi." Sai da tayi maganar kuma sai ta kalli Zahra tana cewa, "ai kina da kuɗi ko? Don can zai fi tunda su basu cika tsawwalawa ba a kan irin wannan aikin."

"Eh mu je, ina dashi, sai dai mu cire a POS. Driver aina zamu samu POS?"

"Eh bari mu tsallaka can hanyar za'a samu."

Can suka nufa suka cire kuɗin kamar yanda Arab ta faɗa mata adadin wanda zata cire. Daga nan suka wuce asibiti ya sauke su suka biya shi kuɗin shi. Suka taka zuwa ciki

A reception suka samu wata nurse suka ce mata, "likita suke son gani?"

Sai da ta gama musu wani kallo tana ganin yanayin su, sai kuma tace, "kun san dai ba haka kawai ake ganin likita ba sai an bi layi, don haka akwai waɗanda suke gaban ku sai ku jira."

Jin hakan sai Arab tayi mata wani kallo, sai kuma ta taɓe fuska tana mayar da idanunta a kan Zahra tare da cewa, "ki bata 2k ta nuna mana Office ɗin da zamu ga likita, don na san abun da take buƙata kenan tunda ƴan maula ne."

Maganar yayi ma nurse ɗin zafi, amma kuma ganin yanayin yadda Arab ɗin take gadara wajen yin magana kuma da yanayin zubin ta; sai tayi tunanin dole akwai abun da ta taka ne, shiyasa tayi shiru bata mayar mata da martani ba, bare kuma taji zancen kuɗi. Ai kuwa Zahra na bata kuɗin ta amsa tana wani yatsina fuska itama, sai kuma tace, "to mu je in kaiku." Tayi gaba

Suka bi bayanta har zuwa wani Office
Chapter 11 · 0% Book details