Sashe 24
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Yo aina zai haɗa ku bayan ba ki san inda za ki same ta ba? But ni baƙin cikina da ba ki ba shi Numbanki ba, da shikenan dole zai neme ki kuma dole sai mun ɗauki mataki a kanta; domin wlh sai mun raba ta da saurayin nata da take taƙama dashi, har abada kuwa, sai ta raina kanta sai ta gummace bata aikata miki hakan ba." Sai ta cije baki tana kaɗa kanta
"Ba ki kai Ni baƙin ciki ba wlh, ai nima na so ace na ba shi Numbata da na san dole zai neme Ni."
"Ke bar kayan takaicin nan ki raka Ni shagon can in siya kati." Arab ɗin tayi maganar tana ƙoƙarin laluba aljihun rigan ta
Zahra tace, "ok."
Sai suka nufi bakin shagon yayinda Arab hankalin ta na kan ciro kuɗi
Ita kuma Zahra suna gaisawa da mai shagon cikin faram-faram tunda sun saba, har tana tsokanar shi, "wlh sai ya ba ta chocolate ɗinta tunda ya taɓa mata alƙawari."
Dariya yayi yace, "afwan Zahra, wlh yanzun ma bani dashi don ya ƙare, sai dai in canza miki da wani abun da kike so."
"To shikenan, bani biscuit mai madara."
Dariya kawai yayi yace, "to." Yana nufan cikin shagon zai ɗauko mata
Ita kuma Arab tace, "Shu'aibu bani kati."
"To wanne iri ranki ya daɗe!?" Yayi maganar yana juyowa da biscuit ɗin a hannunsa ya miƙawa Zahra
Ita kuma ta amsa ta soma ƙoƙarin buɗewa tana cewa, "Allah yasa da daɗi."
Arab tace, "MTN zaka bani, kana da ƴan ɗari biyar ne?"
"Eh ina ga akwai."
"Ok bani guda uku, but kuɗi na bai cika ba zamu haɗe a gaba."
"Kai Matar manya akwai matsala fa idan na ba ki katin nan don na san halin ki."
"Wai kana nufin bazan biya ka bane? Kaima ka san ba ma haka da kai tunda ban taɓa cin kuɗin ka na hana ka ba, da Allah miƙo min."
"Shikenan zan ba ki, amma don Allah kar ki daɗe ba ki biya Ni ba sabida ba nawa bane nima, kiyi haƙuri ki taimaka ki biya Ni da wuri." Yayi maganar yana dariya ganin yanda take hararansa
"Don Allah ka sallame Ni sauri nake yi, ka ga mutane sun soma zuwa kar mu tsare musu wuri."
Sallaman wasu ƴan mata biyu ne ya hana Shu'aibu yin magana
Yayinda wasu yara su ma suna tsaye duk sun zo siyayya ne, sai faɗi suke yi, "a basu kaza... A basu kaza..."
Yayinda ƴan matan nan tunda suka zo suke hararan su Zahra ƙasa-ƙasa
Ita Zahra ma hankalin ta na kan biscuit ɗinta tana ci tana tambayar ɗaya daga cikin yaran nan
While Arab ta juya musu baya tana kallon Shu'aibu da ke ɗauko mata kati, sai ji tayi ƴan matan suna dariya da shewa, hakan yasa ta juya ta kalle su, ta gane su ƴan matan layin su ne, don ɗaya ma maƙociyar su ne, kanta kawai ta kawar tana amsar katin da Shu'aibu yake bata, sai dai bata kai ga sawa ba ta ji maganganun da suke yi wanda hakan ne yasa ta ɗaga kai ta kalle su
Ɗaya tace, "ke bar zancen nan idan mun koma gida ma yi don naga munafukai sun soma saka mana idanu."
Hakan ne yasa Arab ta tanka tace, "Ke Zaliha su waye munafukai a nan? Da wa kike yi?"
"Da wa nake yi kuma? Kamar ya da wa nake yi? Wanda ya tsargu ko kinga na saka baki da ke?" Itama tayi maganar cikin ɗaga murya da tsiwa tana hararanta
Daga wayanta har katin zura su tayi a Aljihun rigan nata tana cewa, "ƙwarai kuwa, domin duk wanda yayi zagi a kasuwa ya san da wanda yake yi, a nan dai mu kaɗai ne a wajen nan, sannan ba yau ba naga take-taken ki nema kike yi ki shigan mana hanci da ƙudundune, na rantse da Allah tsab zan faco ki domin ke ƙaramar alhaki ce ba ki isa in zauna ina sa'insa da ke ba, Ni na fi ki hauka jujun da suke kanki ƙanana ne a kan nawa, don haka ki kama kanki duk wani iskanci da kike ji da shi a tafin hannuna kike, na fi ƙarfin a zauna ana min shaguɗe a gabana in ƙyale ina kallo, kin san hali na ba na juran raini bare wulaƙanci."
Har ta dire maganar Shu'aibu haƙuri yake bata yana cewa, "don Allah suyi haƙuri haka nan, Arab ta ƙyale ta." Don ya san ƙarshe mai zai faru, shiyasa yayi saurin shiga tsakani don a rabu lafiya
But Arab bata san ma yana yi ba tsiya ya ci ranta sai rattaba zance take yi, don ƙiris take jira dama tunda tana da cikin Zalihan ba yau ta saba shiga harkan ta ba, yau kuma baza ta iya haƙura ba dole ne ta ɗauki mataki a kanta
Zahra kuma dayake ba tsiyan ne a ranta ba; sai ta riƙo hannunta zata ja ta su tafi domin ta ƙi tankawa ma
Amma ina Arab sabida jin maganganun da Zaliha da ƙawarta suke faɗi
Har Zalihan na cewa, "yo ku da ku ka yi gadon iskanci waye bai san gidan ku ba? Dama dai ace ba'a san halin balbela bane sai tace daga Misra ta fito, to an san halin ku ciki da bai don kin nuna min ke tatacciyar Karuwa ce mai lasisi bazan damu ba...."
Kafin ma ta ajiye maganar nata tuni Arab ta kafta mata maruka, fau fau haka ta sauke mata su cikin zafin nama da fusatan da tayi
Nan da nan fa sai wurin ya rikice domin tuni Zaliha ta kai mata wawura itama sun soma kokawa
While ƙawarta Jamila sai itama ta soma kai ma Arab ɗin duka suka taru mata
Zahra da ke tsaye ai itama sai ta finciko Jamilan ta hau kima suka soma dambe har da faɗawa shagon Shu'aibu
Ai tuni ya soma ihu yana faɗin, "kai kai zaku yi min ɓanna."
But ko kaɗan ba sa jin sa don yanda suka cakuɗe sai bige-bige ake yi har da cire gyalulluka; ɗankwalai sun yi gefe ana ta tuman juna
Ya rasa yanda zai yi don ya kasa taɓa su ganin mata ne, ganin dai da gaske suna ɓarar mishi da kaya nema suke yi su hargitsa mishi shago sai ya soma ƙoƙarin finciko su yana cewa, "wai meye haka ku fitar min a shago da Allah, zaku yi min ɓanna fa."
Allah da ikon sa sai ga wasu samari sun faɗo shagon tunda suka ga mai ke faruwa, su suka yi ƙoƙarin raba su amma ina sun kasa fincike Arab a jikin Zaliha
Ga shi ita ta fi shan wahala don har yaga mata gaban riga aka yi, babu ɗankwali babu gyalen ta a jikinta, kuma ta ƙanƙame Zalihan ta ƙi saki faɗi take yi, "sai ta koya mata hankali, sai ta nuna mata ita ba sa'ar wasan ta bane."
Ƙarshe dai faɗa yayi tsamari waje ya cika maƙil da Maza sai zuwa kallon su suke yi, bare yanda suka samu abun kallo babu wacce jikinta bai bayyana ba, kar ma ace Arab ta ji, nata ma yayi muni da yawa amma ita ko a jikinta, burin ta kawai ta samu nasaran lallasa Zaliha amma hakan ya faskara don ta fi ƙarfin ta kasancewarta ƙatuwa
Daƙyar wasu Maza suka raba su suka kama Arab ɗin ƙaƙam suka fito da ita a shagon da suka gama hargitsa mishi, nan fa ta soma zagin su tana cewa, "sai sun sake ta ta ƙaddamar mata, wlh baza ta ƙyale ta ba yau sai ta koya mata hankali."
Babu wanda bai san jaraban gidan su ba musamman ma Arab don bata da mutunci ko kaɗan, ba yau suka saba ganin irin wannan damben na tada husuman gari ba, kar ma ace uwar su ta ji. Shiyasa aka yi saurin kiran ƴan sanda don idan ba'a yi hakan ba za'a samu matsala, su kaɗai ne zasu iya tsayar da rigimar nan cikin sauƙi tunda aka taɓo gidan jarababbu.
[22/07, 11:38 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA GOMA SHA HUƊU*
_______________Kafin ƴan sanda su zo har rigimar ta ƙara ta'azzara sabida yanda Arab take zagin mutanen da suka riƙe ta ta uwa ta uba
Kankace me an samu wani wanda ya gwabgwabje ta sabida yanda take zagin su, ya kasa haƙura shiyasa ya same ta ya dinga duka, har da matse mata nonuwa tunda shima ɗan iska ne ya samu na banza a waje, a zuwan yana dukanta haka ya lallatse banza
Ita kuma tun tana ramawa but ƙarfin su ba ɗaya ba, nan da nan yayi mata lilis daƙyar aka ƙwace ta a hannun sa
But bakin ta bai mutu ba haka take ta zagin shi tana kuka. Daga ita har Zahra zagin shi suke yi but ita an riƙe ta ta kasa kufcewa
Motan ƴan sanda na zuwa aka tattara su zuwa police station.
***********
Wani yaro aka samu ya sheƙa da gudu gidan su Arab ya kai musu gulman ana faɗa da su
Ai kuwa nan Inna tayi kiran Ummu tana cewa, "Ummu Kulsum.. Ummu Kulsum."
"Na'am." Ummu ta fito daga bayi da gudu riƙe da buta
"Maza ɗauko min wando na mu wuce station, wai ana faɗa da su Zahra an kai su can, maza-maza ɗauko min mu je mu ji ba'asin abun da ya faru."
Da sauri Ummu ta nufi ɗakin Innan ta ɗauko mata wandon damben ta, dama hakan take yi sau tari idan ana faɗa da ƴaƴan ta da shirin dambe take zuwa wurin, idan ma damben ta kama haka zata tuɓe gyale aba hammata iska, sam Inna Harira bata da ta ido, kowa ya san ta a garin a kan ƴaƴan ta bata da mutunci ko na misƙala-zarratan
Haka suka fice daga ita har Ummu suka tafi station. Suna zuwa kuwa suka hango yanda aka yiwa Arab, duk an farfasa mata baki an ji mata ciwuka, a wurin ma bakin ta bai yi shiru ba shiyasa aka ce cell za'a jefa ta. Dai-dai nan su Inna suka iso wajen