Sashe 6
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Inna tace, "don dai kin matsa ne babu yanda zan yi amma wlh da baza ki je ba, har wani ciwon ne sai an je an ganta?" Sai ta ja tsaki tana wucewa
Baba kuwa girgiza kansa kawai yayi, sai kuma ya kalli Arab da ta miƙe zata wuce yace, "bari in koma wajen sana'a na, kafin ki tafi zan dawo sai muyi sallama."
"Sai ka ce wani tsiya za ka bata idan ka dawo ɗin? Aikin banza aikin hofi." Inna tafaɗa bayan ta fito daga ɗaki tana dallawa Baban harara
Baba kuma bai ce komai ba ya wuce ya tafi
"Arab ki zo ki ɗibi abincinki ki ci, sai ki zo ki amso min ƙanƙara wajen Lantana in sa a kunun nan. Na san yanzu zasu dawo tunda sun ce ƙarfe ɗaya zasu gama karatun."
"To ina zuwa." Arab tafaɗa daga cikin ɗaki, kayan makarantarta ta cire ta saka wani doguwar rigan Abaya wanda ya fito mata da kyakkyawar shafe ɗin jikinta, sosai rigan ta kama ta saboda yanda aka matse mata dai-dai jikinta, sai ta ɗaura ɗankwalin Abayan a saman kanta da ke ɗauke da ƙananun kitso da aka yi mata, sun zubo har kafaɗunta, kana gani ka san ta haɗa jiɓi da Fulani saboda yanda gashin suka nannaɗe gunin sha'awa, sai dai ƙarshen kitson duk ya tsefe duk da kuwa kasancewar kwana biyu kenan da Ummu tayi mata, kasancewar ita tana son kitso shiyasa ko yaushe za ka ganshi a kanta duk da gashin nata ba ya zama da kitso, yanzu idan ma ta bar shi kafin sati ya tsefe da kanshi don da kanshi yake tugewa, shiyasa bata da wahalan ta sake wani kitson tunda tana da masu yin mata, har Inna tana yin mata, ita kaɗai ce me son kitso a cikin su, don su Zahra ma bai dame su ba sun fi son barin kansu a haka tunda su ma nasu gashin ba ya son kitso, ko sun yi warware wa yake yi, duk Innarsu suka biyo. Flat shoes ta saka a ƙafanta sannan ta fito
Inna tace, "nace ki bari ki ci abinci sai ki wuce."
"A'a ba na jin yunwa, bari in amso miki, idan su Aunty Ummu sun dawo sai mu ci tare."
"To." Innar tafaɗa tana wucewa kichen ta sauke abincin siyarwan da take yiwa su Ummun
Itama kuma Arab ta sa kai ta fice. Bata jima ba ta dawo tunda a maƙotan su Lantanan take
Time ɗin su Ummu sun shigo su ma. Shiyasa suka zauna suka ci abincin tare
A nan Arab take sanar da su, "zata je gidan Aunty Firdausi."
Zahra tace, "ai da na bi ki kuwa, amma babu hali tunda karatu yayi zafi, sai dai ki gaishe ta, nima zan kira waya in Yi mata ya jikin."
Itama Ummu tace, "Auta ki gaishe ta don Allah, ko zuwa weekend ne zamu zo, amma yaushe za ki dawo?"
"Kwana biyu kawai zan yi, tunda kun ce zaku zo sai in tsaya mu dawo tare."
"Eh hakan yayi, Allah ya kaimu Asabar zamu zo sai mu dawo a ranan."
Inna dai na jinsu bata ce musu komai ba. Sai da ta gama abun da take yi sannan tace, "ga abincin nan na gama don Allah ku tashi ku wuce, kunga har biyu tayi."
"To Inna." Duk suka amsa mata
Yayinda Zahra CE ta soma tashi tayi alwala ta shige ɗaki
Itama Ummu alwalan tayi; tayi sallan sannan suka shirya suka fita
Arab tace, "Inna bari in Yi wanka kawai in wuce, ki bani dubu goma a kuɗin jiya saboda babu kuɗi a hannu na."
"Ki shiga ɗaki ƙasan Matashi na suna nan na ajiye a wajen."
"To." Tace tana wucewa. Sai da ta ɗauki kuɗin ta je ta saka a jaka sannan tayi wanka ta shirya. Riga da wando ta saka masu tsantsi, rigan milk color da flowers a dai-dai setting ƙirjin ta da aka yi da kalan maroon color kalan wandon, wanda shima ƙasan wandon aka yi flowers da milk color, kayan sun yi mata kyau ainun sabida kasancewar ta me sura me kyau wanda duk namijin da ya kalle ta sai kyawunta ya bizge shi, bare uwa uba yayi arba da kyakykyawar cuty face ɗinta, fuskar nan nata ta sha makeup me ɗaukan hankali, bakinta sai shaining yake yi, gyalen kayan ta ɗauka kalan milk ta yafa a kanta sannan ta jefa jelan a gefe da gefen kafaɗunta, sai ta saka takalmi masu shegen tsini white color, sai da ta jefa chewing gum a bakinta domin ita mayyar cin chewing gum ne, ya zama sabon ta ba ta rabo dashi, Hangbag ɗinta ta ɗauka na takalmin shima kalan fari ta rataya, sannan ta fito cikin yauƙinta ta wuce ɗakin Inna
Inna na ganinta ta washe baki saboda farin ciki, "ga farar zinariya alkyabbar Mata, kin kerewa kowacce Mace sai dai su biyo bayan ki, kinga yanda kika haɗu kuwa?"
Dariya tayi tana taunan chewing gum ɗinta ƙas-ƙas-ƙas, sai tace, "na san haka Innata, amma nayi zam-zam ko babu wata mishkila?" Ta ƙare maganar tana juyawa a gaban Innar
Inna tace, "babu abun da yayi saura, ai ke me kyau ce Autana, ko ba ki yi kwalliya ba komai yin miki kyau yake yi, Allah yasa ki samo mana wani me gwaɓi-gwaɓi wanda zai kai ni Makka da Madinah."
Arab tayi dariya tace, "Inna kar ki damu insha Allahu zan cika miki burin ki wata rana."
"Kai Allah ya amsa addu'ar ki Autana, amma ki kula fa don bazan so wani abu ya same ki ba, Allah ya tsare."
"Amin Inna." Sai tayi dariya tana cewa, "to Inna ba ki ce in gaishe da Aunty Firdausin ba?"
Taɓe baki tayi tace, "to har sai na ce? Ai ta san ina gaishe ta".
Sosai Arab take dariya a wannan lokacin, tace, "Innarmu na Aunty, Allah ya bar ku tare, zan ce kina gaishe ta sosai, zan biya sai in Yi sallama da Baba a kasuwan. Babu wani abun da zan kai mata ne?"
"To me nake dashi da zan ba ki? Gaisuwar ma ta isa."
"To Inna na tafi, bye." Sannan ta fice ta shiga ɗakin su, jakarta da ta zuba kayan sakawanta ta ɗauka, ƙaramar Trolley ne, ta janyo ta fito. Har waje Inna ta raka ta suka sake sallama sannan ta tafi.
[07/07, 11:29 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA HUƊU*
_______________ *KADUNA STATE*
Bayan Arab ta sauka a tashan Kawo da ke Kaduna; sai ta kira Numban Nafi'u tunda sun san da zuwanta, time ɗin da Baba ya je kasuwa ya kira ya sanar mishi, "Arab na nan zuwa."
Babu jimawa kuwa sai ga Nafi'u ya taho a motan shi, bai sha wahalar hango ta ba, sai ya faka motan nashi ya fito ya nufi inda take tsaye riƙe da waya a hannu tana faman latsawa, kanta na sunkuye tana tauna chewing gum ɗin da ke bakinta. Yana isowa yayi mata sallama
Sai ta ɗago kai tana kallonsa da manyan idanuwanta da suka sha tozali suka sake haske tarr masu ɗaukar hankali, murmushi ta saki tace, "Yayanmu."
"Na'am Autanmu. Barka da zuwa."
Dariya tayi sai tace, "yauwa. Ina wuni?"
"Lafiya ƙalau, ya mutanen gidan?"
"Alhamdulillah duk suna gaishe ku."
"Masha Allah muna amsawa. Mu je to ga motan can, kawo akwatin." Ya saka hannu ya karɓa sannan suka taho wajen motan suna magana suna dariya. Bayan sun shiga ne yake cewa, "bari in kai ki gida inyaso sai in je ɗauko Auntyn naki tunda an sallame ta ma."
"A'a Yaya, mu je tare sai ka ɗauko ta."
Murmushi yayi yace, "ke da kika sha hanya? Ki bari kawai in ɗauko ta ɗin kar ki sake shan wahala, suna tare da Ummana ne ma, bari in kai ki sai in je in ɗauko su."
"Ok shikenan."
Daga haka suka wuce gidan Nafi'un. Ƙaramin gida ne flat ya gina abun shi, bai jima da tarewa ba bayan auren da suka yi. Mahaifiyarsa kuma tana babban gidan su ne tare da kishiyoyinta; tunda Matan Baban Nafi'u su huɗu ne, kuma Nafi'un shi ne kaɗai ɗa a wajen Mahaifiyar sa. Bayan ya kaita ya sauke ta tare da bata makullin gidan, sai ya tafi asibitin
Ita kuma ta shige ciki abun ta, a falo ta samu waje ta zauna tana zare gyalenta ta ajiye. Tsarin gidan take bi da kallo tunda yau ne zuwanta na farko, lokacin da suka kawo Firdausi a babban gidansu aka soma ajiye ta before ya gama ginin sa, babu laifi gidan ya ɗan birge ta, but sai yatsina fuska take yi tana tunanin, "idan ita ce baza ta iya zama a ciki ba, gida kamar kurkuku wai ace a nan zaka ƙare rayuwarka." Sai ta sake taɓe baki tana tashi tsaye ta nufi ƙofofin da ta gani, ta soma buɗewa tana leƙawa, da kichen ne da Toilet, sai kuma ɗakuna biyu masu kallon juna, ɗaya na Nafi'u ɗaya na Firdausi. Ɗakin Firdausin ta shige da akwatin ta, ta shiga toilet ta ɗaura alwalan magriba da aka kira, kasancewar bata yi sallan la'asar ba sai ta haɗa
Tana cikin sallan ne suka dawo gidan. Daga Firdausi sai Nafi'u tunda sai da ya wuce da Ummansa gida sannan suka nufi nasu gidan. Kasancewar ya faɗa ma Umman nashi, "akwai ƙanwarta ta zo." Shiyasa tace, "to ya sauke ta a gida kawai."
Jikin Firdausi da sauƙi sosai, dama ciki ne take dashi kusan watanni biyar kenan, kuma tunda ya fara girma sai ciwo ya sako ta a gaba, ko lokacin da yake ƙarami bata sha wahala irin yanzu ba, sosai take ciwo shi ne har aka dangana ga asibiti, kuma ta tashi hankalin ta tana kukan, "tana son ganin ƴan uwanta ko Innarsu." Gaba ɗaya hankalin ta a tashe yake musamman yanda suka yi watsi da ita kusan seven months basu zo sun ganta ba
Dalilin da yasa Nafi'u ya kira Baba ya sanar mishi kenan. Kuma shi kansa bai yi tunanin zasu iya zuwa ba tunda ya san Innarsu ba ta son shi, amma kuma sai ga shi Arab ta zo