Sashe 35
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Bari in je in duba waye ne, duk da ban yi da wani zai zo ba. Ina zuwa." Sai ta ajiye wayan tana miƙewa tare da zura slippers ɗinta da ke wurin, ta zari mayafin Zahra da ke jikinta ta rufe kanta kasancewar babu komai, daga ita sai doguwar riga Robber brown color; ta fice ta nufi waje. Tana fita ta hangi wata dalleliyar mota har wani sheƙi take yi tsaban kyawu da sabunta, da kallo ta bi motan tamkar idanuwanta zasu faɗo, zuciyarta tana me aiyana, "waye wannan?" Nan da nan sai ta sauya tafiya ta nufi motan kanta tsaye babu ko tsoro bare tunanin wani abu, yayinda ko ƙyafta idanu ba ta yi wajen kallon motan da santin da take yi har da haɗiyar yawu.
[01/08, 8:53 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA ASHIRIN*
_______________Koda ta isa wurin motan sai da ta gama zagaye ta har tana leƙe-leƙe, sai dai ba ta ganin kowa sai na ciki ne zai ganta
Tana cikin dube-duben ne wani matashin saurayi ya fito daga ciki yana murmusawa tare da yin mata sallama
Ta amsa tana kallonsa tare da ƙare masa kallo, "lafiya Malam? Kai ne kake kira na?" Ta furta da mamaki sabida ganin yanayin saurayin kuma a cikin wannan motan, wacce a ƙiyasinta duk da bata gama sanin ire-iren waɗannan tsadaddun motocin ba; amma tabbas wannan zata iya kai wa miliyan takwas ko goma
Saurayin ne ya sake magana sabida ganin tayi shiru hankalin ta ma ba ya wajen sa
Hakan ne yasa ta ɗan yi firgigit tana ɗan waro kyawawan idanuwanta a kansa, tare da ƙirƙiro wannan Shegiyar murmushin nata tana cewa, "ina jin ka Malam, mai kace ne?"
Murmushi yayi yace, "ba suna na Malam ba, suna na Ahmad, kuma Ni ɗan saƙo ne wajen ki, aiko Ni aka yi."
"To fa. Wane ne ya aiko ka?" Tayi maganar tana ɗan gyara tsayuwar ta, tare da ƙara kafa mishi idanuwanta ko ƙyafta su ba ta yi
"Kar ki damu za ki sanshi ai, sai dai shi bai bani damar bayyana miki kansa ba, abun da ya aiko Ni kawai na zo yi, shi uban gidana ne shi ne yace in kawo miki wannan." Sai ya buɗe motan ya ɗauko wata ƙatuwar jaka ja mai kyau da burgewa a ido, ya zagayo yana miƙa mata
Ta saka hannu ta amsa tana bin Jakar da kallo, kana kuma ta mayar da kallonta gare shi
While shima idanuwansa a kanta yana cewa, "wannan shi ne saƙon, sannan akwai waya a ciki idan kika kunna za ku iya magana a ciki don zai kira ki." Sai ya miƙa mata key ɗin mota ya ƙara da faɗin, "sannan wannan ma shi yace in ba ki, motan nan taki ce."
"Ban gane ba?" Ta furta tana zare idanu tare da shiga ruɗu da jin zancen nasa
Murmushi yayi shi kuma yace, "kar ki damu za ki gane ai, Ni dai abun da aka ce in Yi kenan, kuma na aiwatar da aiki na, Ni zan tafi sai kuma wani lokacin."
Da kallo ta bi shi har ya juya ya wuce a ƙafa, ta kasa motsawa sabida mamakin da ya cika ta tare da tunanin waye wannan? Wane ne ya aiko sa? Amma kuma tuna furucin sa na ƙarshe da cewa motan nan nata ne; tuni fuskarta ta sauya nan da nan ta washe baki ta soma zagaye motan tana shafawa, cikin wani irin farin cikin da ya tabaibaye ta har jikinta rawa yake yi ta juya gida da gudu. Tana shiga gidan ta soma kwaɗawa Zahra kira
Zahra da ke wurin inda ta bar ta tana shan waƙa, sai tayi saurin zare earpis ɗin da ta sanya saboda yanda taga ta sukwano wajenta a guje. "Lafiya mene ne?"
Arab ta kasa ma magana sabida yanda bakin ta ya ƙi rufuwa tsaban daɗi, sai yarfa hannu take yi tana son yin magana but ta gaza. Daƙyar ta natsu ta furta, "wlh na yi kamu.. na yi goshi.. na yi kasuwa ne ina tunani."
"Faɗa min mana me ya faru ne don Allah? Kin saka Ni a cakwakiya." Zahra itama ta furta cikin zumuɗi da son sanin abun da ya faru
"Mota... Mota... Mota ce wani ya kawo min Alkur'an, kin ganta ne kuwa? Wayyo Allana! Daɗi zai kashe Ni wlh." Tayi maganar cikin tsantsan farin ciki tare da tura mata Jakar tana cewa, "kinga har da wannan ya bani." Sai kuma ta soma ƙoƙarin buɗewa
Zahra na taya ta da faɗin, "wai wane ne? Waye zai ba ki mota?"
"Nima ban sanshi ba, amma yace min..." Sai kuma tayi shiru sabida ganin abun da ke cikin jakar
Gaba ɗayansu suka ɗauke wuta ganin wannan maƙudan kuɗaɗen da ke cikin jakar. A tare suka kama baki suna zare idanu
Hannu na rawa Arab ta sanya tana shafa kuɗin, yayinda take ɗauka tana mayarwa tare da zaro kwalin wayan da ke ciki. "Kuɗi.. kuɗi ne..." Ta furta cikin ihu da tsananin murna
Wanda hakan ne ya farkar da Ummu da ke cikin ɗaki, ta fito da sauri tana hamma da cewa, "wai ihun me ake yi ne a wurin nan?"
"Zo ki gani, zo ki ga abun mamaki." Zahra ta furta itama tana kai hannu kan jakar kamar zata taɓa sai kuma ta janye hannun, don ta tsorata da ganin wannan kuɗaɗen, don babu shakka ƙila ɗan yankan kai ne ya aiko mata da kuɗin
Itama Ummu zuwa tayi wajen tana durƙusa wa tare da zaro idanu tana mamaki da faɗin, "wannan kuma daga ina? Aina wannan kuɗin ya fito?"
"Wlh Arab ce, Arab ta zo da su." Zahra ta furta cikin tsoro
Arab tace, "Wani ya bani, nima bai faɗa min ko waye ba, yace min idan na kunna waya mutumin zai kira Ni, sannan ya bar min mota a waje yace nawa ne."
"Mota? Amma waye wannan?" Cewar Ummu cikin sake shiga mamaki, sai kuma ta miƙe tana cewa, "mu je mu ganta."
Zahra tace, "wai kun tabbatar ba ɗan cin kai bane? Kar fa mu shiga uku, Ni a tsorace nake wlh."
Tsaki Arab ta ja itama tana tashi da cewa, "ɗan cin kai kuma? Ke ana maganar arziki kar ki kawo mana ta tsiya mana. Uban ɗan cin kai ɗin." Sai ta dubi Ummu tace, "Aunty Ummu mu je ki ganta."
Suka fita a tare da sauri tare da barin kuɗin a nan wurin
Itama sai Zahran ta tashi ta bi su. Sun sha mamakin ganin zazzafan motan nan, tare da mamakin wanda ya aiko da su? Abun ya ɗaure musu kai; musamman da suka shiga ciki suka duba kuɗin wanda ƙiyasin su ya tabbatar musu da One million ne, sannan ga babban wayan da ke ciki ƙirar Samsung, har da simcard a ciki. Koda suka kunna babu komai a ciki bare su kira Number. Sun kasa kataɓus don a wurin suka zauna suka tasa kuɗin a gaba, kowa na kawo nashi tunanin a kan mutumin da ya aiko kuɗin
Ita Arab farin ciki kawai take yi, sai da ta tashi ta taka rawa don daɗi, ita a wurinta ko waye ne wanda ya aiko mata da kuɗin babu ruwanta ko ɗan cin kai ne wlh, kuɗi dai ya zo hannunta baza ta taɓa mayar wa ba, a kan kuɗi babu abun da baza tayi ba, burin ta ma kawai ta ga kiran Mutumin, don ta ƙosa ta san waye ne me yake nema a wajen ta? Me yake so ta ba shi? Amma shiru babu kiran sa
Har Inna ta dawo suka shafa mata wannan daddaɗan labarin, ai daɗi kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha don babu wanda ya fi ta farin ciki, ita gani take yi ƴarta ne tayi goshi, duk yanda aka yi babban Mutum ne wanda ya aiko mata da wannan kuɗin, Shiyasa take ta sake musu huɗubar tsiya ta ci gaba da ɗaura su a kan keken ɓera, tare da sake ba wa Arab shawaran, "duk yanda za'a yi kar tayi sake da duk wane ne ma mutumin? Domin tana ji a jikinta arzikin su ne ya zo, tun yanzu ma sun tashi a sawun talakawa. Ai arziki kashi a wurin su yanzu."
Sai dariya suke mata sabida yanda take ta santi har tana kasafa kuɗin yanda za'a yi dashi
Ita dai Arab ta amshi dubu ɗari biyar a ciki ta ɓoye kayan ta, zuwa gobe zata kai banki ta zuba a account ɗinta. A ranan kasa barci tayi don daɗi, bata taɓa shiga farin ciki kalan wannan ba, Allah-Allah take yi mutumin ya kira ta don ta ƙosa sosai ta san waye shi? Amma shiru har safe tayi babu kiran shi. Tun tana zuba ido haka ta haƙura ta dena tasa wayan a gabanta; daga ƙarshe ta koma harkokin ta
Kusan ƙarfe biyu na rana suka fita da Ibrahim a sabon motan nata, sun sha yawo babu inda basu zaga ba. Sai yamma suka dawo gida suka rabu a kan zai dawo anjima su fita zuwa club. Akwai wani Abokinsa da suke party a can, bayan ya bata labari shi ne tace, "zata bi shi."
Da dare nayi kuwa ya zo ɗaukar ta. Ta ci wanka ta saka riga da wando matsatstsu tace ma su Inna, "zata je party da Bestyn ta." Haka ta fice babu wanda ya damu bare ya saka mata ido
Baba ma bai san da fitan ta ba tunda yana ɗakinsa a lokacin
A sabon motanta suka wuce zuwa club ɗin. Tun a waje za ka tabbatar da wurin babu ɗan kirki
Maza ne da mata suka cakuɗe kowa da shigan banza a tare da shi, daga masu shaye-shaye sai masu casu, haka wurin ke tashin kiɗa ana ta iskanci, duk ƴan duniya ne gogaggu mara sa tarbiyya su ke wurin
Yanda wurin ya haɗu kowa na harkan gaban shi ya burge Arab. Nan fa jikinta ya tsumu tunda ta ji kiɗan nan sai da ta shiga ta taka
Daƙyar Ibrahim ya janyo ta suka fice zuwa wajen Abokin nasa, a nan ya gabatar da ita a cikinsu