← Book details Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 52

Sashe 2

Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

        Ƙaramar ƙanwar su wato Arab, wacce a yanzu tana S.S 2 ne, ita kuma Inna Harira tana mata awara ne da yamma tana siyarwa a can bakin layin su. Gaba ɗaya yaranta ban da Firdausi ta ɗaura su a tirban da take buƙata, kuma su kansu sun tashi idanunsu a buɗe basu da buri sama da su cikawa uwar su burin ta, su kansu suna jin haushi musamman ganin su a gidan ƙasa gidan talakawa, ga ƙawayen su duk yaran masu kuɗi, shiyasa basu da aiki sai ƙarya, idan ka gansu baza kace yaran talaka bane sabida suturun da suke saka wa, kamar baza su taka ƙasa ba don yanga da iyayi. A duk cikin su ukun; Arab ta fi su fitsara da rashin kunya, domin ita halin mahaifiyarta ta ɗauka har ta zarta ta a son kuɗi, dalilin da yasa kenan ta soma ba wa maza kanta tun a wannan lokacin don kawai ta samu abun duniya, ga ta da samari ko ta ina, duk inda ta gibta sai ta samu saurayi, sai dai ita babu aure a tsarin ta a cewar ta, "sai nan gaba, sai ta gama karatu sannan zata yi aure". Dalilin da yasa take gara kan samari kenan, ga shegen wayon; sai ta ci kuɗin saurayi kuma ta hana shi abun da yake so sai ta gama jan mishi rai ko kuma ta gama wulaƙanta shi. Arab kenan yarinya mai zamani wacce take cin duniyar ta da tsinke a yanzu, a duk faɗin tudun Wada da kewaye babu wanda bai santa ba, har kirari ake mata da sunan, 'Arab Matar manya, kin fi ƙarfin Yaro'.

✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

         Yau ma kamar kullum yanda Inna Harira ta saba yiwa Arab awara domin ta fita mata dashi; hakan ne yau tayi mata, sai dai na yau ya fi na kullum yawa saboda ganin yanda ake ciniki sosai, ba ta daɗewa yake ƙarewa idan ta fita dashi, shiyasa tace wa Arab ɗin, "Autana yau da yawa zan yi miki tunda naga kina dawowa da wuri yana ƙarewa."

Arab tace, "ai kuwa Inna dama ina so in yi miki magana ki ƙara yawan shi don naga ba ya isan su suna son awara na wlh."

Baki Inna Harira ta washe ita kuma tana cewa, "ai dole ne su so awaran ki sabida daɗi, Ni na san na iya ai, ko kayan da nake kashe wa wannan awaran dole su riƙa santin shi."

Dariya daga Arab har Ummu da take jin su suke yi

Ummu tace, "Inna ai Ni ina ganin hannun ki ne mai albarka, ko abincin nan da muke fita dashi ba ki ga yanda ake wawa ba wlh, mu ma idan za ki sake yin mana sai ki ƙara yawan shi, ki haɗa ma har da kunun aya don shima ana yawan tambayar mu."

"To shikenan Allah ya kaimu goben za'a ƙara, dama ina ta tunanin siyan fridge wlh, to yanzu tunda kin ce haka kinga ban ga ta zama ba, yanzu ki taso ki shiga kasuwa sai ki siyo min abun kunun mu fara mu gani; Allah ya bamu sa'a."

"Amin AMin." Duk suka amsa daga Ummun har Arab

Sai Inna Harira ta kuma cewa, "yi sauri Auta ki shirya yanzu zan yanka miki ki wuce."

"To Inna." Arab ta amsa tana tashi daga bakin ƙofan da take zaune tana yankan ƙumba, ta wuce cikin ɗakin su, kayan jikinta ta cire ta ɗaura zani daga iya ƙirjin ta, kana ta fito kanta babu ɗankwali ta kamfaci ruwa a rijiya ta shiga wanka. Ta jima kafin ta fito tunda dama haka ta saba yin wankan ta, bayan ta shiga ɗaki ta gama shiryawa ta fito wajen

Ummu ta soma koɗata tana cewa, "iyen ba Ƙanwar mu, kin ga yanda kika tsatso kyau kuwa? Anya wannan baza ki haɗa gosilo a titi ba? Tirƙashi."

Dariya kawai Arab ɗin take yi tana duba jikinta

Yayinda itama Inna Harira sai washe baki take yi tana koɗa ta tana cewa, "ƴan matana ta fi na kowa kyau, iyee! Kin yi kyau sosai Auta na, na san yau akwai kasuwa kenan."

Fari tayi da manyan idanuwan ta tana taunan chewing gum ɗin bakin ta, yayinda ta furta, "sosai ma Inna, sai mun dawo kawai kiyi min addu'a."

"To Allah ya tsare Allah Ubangiji ya bada Sa'a, Allah yasa a samo mana rusheshen me kuɗi wanda zai kai Ni Makka bana."

"Amin AMin innarmu." Duk suka amsa suna dariya

"Ke ma tashi ki shirya ki wuce kasuwan nan kinga yamma tana yi." Tayi maganar tana kallon Ummu

Ita kuma Arab ƙaton farantin da aka jera mata komai, kama daga kan; icce, matsama, ashana, kalanzir, kafi-tankiya da Robbern zuba awaran idan ta tsame, duk suna kan farantin saboda ƙato ne, sai ta riƙe Robbern awaran a hannu tunda shi mai hannu ne, irin bokitin nan ne fari amma ƙato sosai, ta yiwa Innan sallama ta fice a gidan tana ci gaba da taunan chewing gum ɗinta, ƙararas-ƙararas kawai ake ji tana tafiya kamar zata karye tsaban yanga. Sai da ta ɗan yi nisa da gida sannan ta hangi Zahran su a cikin wata ƙatuwar jib ita da saurayin ta, shiyasa ta nufi wajen don ta ƙi wucewa sai ta kwashi rabon ta, tunda ta hangi wannan motan to akwai maiƙo a wajen, shu'umin murmushinta ta saki har da cije laɓɓa; tana wani gyara tafiyar ta cikin tsananin yanga ta nufe su tare da rangaɗa musu sallama

Gaba ɗayan su suka kalle ta suna amsa mata sallaman,
Yayinda Zahran tace, "Ah har kin fito Auta?"

Yatsina fuska tayi tana kallon ta tace, "eh wlh na fito, shi ne na hango ki nace bari in zo, dama Inna ce tace idan na ganki in amshi Naira ɗari biyu zan ƙara icce dashi, sannan kuma in siya yaji da sauran."

Zahra tace, "to ai Ni bani da kuɗi, ban fito da kuɗi ba, sai dai ki koma..."

Tun kafin ta ƙarisa zancen saurayin nata yace, "a'a Baby bari in bata." Sai ya sanya hannu a cikin Aljanu cikin sauri ya zaro kuɗi daga ciki, ƙirgawa ya soma yi

Yayinda Arab sai zuba murmushi take yi har tana ƙara leƙawa tana lanɗe baki, idanunta suna ware a waje tana ganin yanda yake sarrafa hannayen nasa wajen ƙirga kuɗin, a zuciya kuma tana taya shi ƙirga

Sai da ya ƙirga dubu goma cif kafin ya miƙo mata yana mata murmushi yace, "yauwa ƙanwata ga shi."

Ta miƙa hannu cike da yanga ta amsa still tana murmusawa tace, "na gode."

Murmushin ya kuma yi ko ƙyafta idanu ba ya yi a kanta yace, "babu komai ƴan mata yiwa kai ne, amma Baby ƙanwar ki ne da gaske?" Ya ƙare maganar yana mayar da idanun sa a kan Zahra

"Eh ƙanwata CE love, ita ce take bina kuma ita ce ƙaramar mu."

"Masha Allah gaskiya kyakykyawa ce, ga kama nan ma na gani sabida duk kuna yanayi ai."

Dariya kawai Zahran tayi,
Inda ita kuma Arab ta lanƙwashe murya tana sake mishi godiya

Yace, "babu komai ki je kawai."

Da haka ta wuce ta tafi; Zahra na mata, "sai ta dawo".

         Tana wucewa saurayin yace, "Baby gaskiya duk ta fi ku kyau wannan ƙanwar taku, wow! Allah yayi halitta a nan."

Haɗe fuska ita kuma tayi tana cewa, "to me kake nufi ne wai kake ta koɗata a gaba na?"

Murmushi yayi yace, "Baby Sarkin kishi, ai saboda tana ƙanwar ki ce nake koɗata a gaban ki, amma babu wani abu a raina, yanzu mu je shan icce cream ɗin ko mu fasa?"

Murmushi tayi tare da cewa, "mu je idan har baza a jima ba."

"No Baby baza mu jima ba wlh, just thirty minutes ma ya isa."

"Ok mu je."

Daga haka suka rufo ƙofofin motan sannan ya ja suka tafi.

_In ana comments za a iya ganin posting koyaushe, so ku ba da haɗin kai please, idan kuma babu wani comments ba na bukatar ƙorafi don Allah, duk sanda ku ka ga sabon update shikenan._
[07/07, 11:26 pm] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍

       *RUƊIN DUNIYA!*

🌍🌍🌍🌍🌍🌍

*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_

*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT 🧝*

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞

```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

                  *P.W.A✍️*

_________________________

*BABI NA BIYU*
______________Wayanta ne ta soma Ring, sai ta ɗan dakata daga tafiyar yauƙin da take yi, tare da ajiye Robbern awaranta ta soka hannun ta a cikin Aljihun doguwar riganta; tare da zaro wayanta tana kallon me kiran. Sunan Besty ne ya fito ɓaro-ɓaro a kai, ba tare da jan lokaci ba tayi peacking tana karawa a kunne da cewa, "ya dai Besty?"

"Lafiya, ke nake jira tun ɗazu gani a wajen suyan ki, ko dai yau baza kiyi bane don naga time yana wucewa?"

Yamutsa kyakkyawar fuskarta tayi cike da yanga irin nata tace, "No gani nan a hanya ai, ina zuwa."

"Ok kiyi sauri da Allah, akwai labari wlh."

"Haba nawan?" Tayi maganar tana ɗan sakin fuskarta kaɗan

"You just have to come and see for yourself. "

"Ok. I'm coming" Sai ta zare wayan a kunnenta tare da zura ta a cikin Aljihun, sannan ta ɗauki Robbern awaran ta ci gaba da tafiya. A haka tana yi kamar baza ta taka ƙasar ba har ta fita layin gidan su, duk inda ta wuce gungun maza kallon ta suke yi, majority wasu gulman ta suke yi, ƙalilan kuma suna mata magana kasancewar mutanen ta ne. Sai dai ta gaisa dasu kawai ta wuce har sanda ta kai babban titi inda take yin tuyan awara

Da sauri Ibrahim her friend; ya taso daga saman wani benci da ke gaban shago a wajen; ya sauke mata farantin saman kanta yana dariya tare da cewa, "Oyoyo my Besty, I've seen you before everyone."

Murmushi tayi tana ajiye Robbern tace, "uhm Ni ban ga alama ba, bayan yau kwata-kwata ban ganka ba sai yanzu, ina ka shige ne?" Ta ƙare maganar tana narkar da manyan idanuwanta a cikin nashi, tare da sauke mishi wani kallo da ke rikitar da duk wanda ta yiwa shi
Chapter 2 · 0% Book details