Sashe 17
Rudin Duniya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariyan farin ciki ta saki itama tana mishi kallon soyayya. Cike da shauƙi da ƙaunarsa take ƙara narke mishi tana jan shi da hira me shiga jiki
Cikin ƙanƙanin lokaci suka isa Zaria tunda yana zuka gudu, kafin karfe biyar sun kai. Sai ya kira Abokin nashi ya sanar mishi inda suke
Babu jimawa abokin ya taho a motansa. Parking yayi ya fito ya isa wajen motan Malik
Sai shima ya fito daga cikin motan nashi, da dariya a fuskokin su suka cafke hannaye cikin tsananin farin cikin ganin juna
Itama Nawwara fitowa tayi tana kallon su ganin suna gaisawa
Sai Abokin yace, "ah my Man wannan kuma kyakykyawar fa?"
Murmushi Malik yayi yace, "Ƙanwata ce kuma wacce zan aura, Do you remember Nawwara telling you time muna school?"
"Yeah! Yeah! I remember, kana nufin ita ce still?"
"Yes ita ce. Nawwara ga Aboki na, my classmate his name is John."
Hannu John ya bata don su gaisa. Sai ta miƙa mishi nata tana murmushi tare da cewa, "hello."
"I'm glad to meet you. The truth is you are beautiful. My friend deserves to have you."
Duk dariya suka yi, inda ita kuma Nawwara tace, "Thanks." Cike da farin ciki a fuskarta
"Ok amma zaku je gidana ku huta zan ji daɗin hakan, yau ina da manyan baƙi." Yafaɗa yana washe baki
Malik yace, "no John muna kan hanya ne, let sometimes we meet again, I will come especially for you but now we are in a hurry."
"Ok babu yanda na iya ai, nayi farin ciki duk da haka ma." John ɗin yayi maganar yana murmusawa tare da ba shi hannu suka sake gaisawa. Daga nan suka yi sallama ya wuce nashi motan
Su ma suka shiga nasu Malik ya ja suka wuce. "Bari mu nema abinci ko Baby?" Yayi maganar yana kallon Nawwara
Sai ta gyaɗa mishi kai tana cewa, "Yes because I'm hungry now." Hannunta ɗaya a kan cikin ta tana shafawa
"Ok ga bank can, let me withdraw money, I have no money in my pocket." Yayi maganar yana yin parking a gefen titi, "ina zuwa yanzu zan dawo." Ya buɗe motan ya fice zuwa tsallaken titi inda ya ga kamar wajen cire kuɗi ne. Yana zuwa ATM card ɗinsa ya zaro yana shirin tusa wallet ɗinsa da ta biyo baya, sai kuma ta faɗi a ƙasa, juyawan da zai ɗan yi ya ɗauka sai suka ci karo da Zahra da ta taho da sauri tana waya itama bata kula dashi ba, bata san zai dawo baya ba shiyasa suka ci karo har goshin su ya haɗe da juna. Da sauri suka furta, "oshhh!" Suna ɗagowa the same suka kalli juna. Waro idanu sosai Malik yayi yana kallonta saboda ganin yanda lokaci ɗaya tayi mishi kama sak da yarinyar da ya kamu da soyayyarta da bai san inda zai same ta ba, sai ga ta a gabanshi for surprise
Ita kuma Zahra tuni tace mishi, "sorry." Tana ƙoƙarin janye jikinta ta wuce
Sai yayi saurin dakatar da ita yana cewa, "ba ki ji ba don Allah." Lokaci ɗaya ya kai hannu ya kamo nata hannun ba tare da ya san yayi hakan ba
Shiyasa ta tsaya tana kallon shi itama, sai dai bata yi yunƙurin janye hannun nata ba illa kallon kyakkyawar fuskarsa da take yi
Murmushi yayi mata yana janye hannun sa da cewa, "kiyi Haƙuri na taɓa ki."
"No babu komai." Ta furta itama tana murmushin har da canza tsayuwa cikin yanayin jan hankali
Shi kuma sai a lokacin ya gama tantance ba ita bace domin suna da bambanci da wancan, amma tsananin kaman nasu yayi over a jikinsa yana ji duk yanda aka yi suna da alaƙa da juna, kamannin ta sak yake gani a jikin wannan dole suna da alaƙa, zai iya yiwuwa, shiyasa yayi saurin cewa, "idan babu damuwa ki bani Numban ki mana, don Allah kar ki ce na tsayar da ke a kan hakan, and ina son..." Shiru yayi sabida ganin Nawwara a gaban su tamkar kububuwa ko wacce aka hankaɗo
Lokaci ɗaya idanuwanta suka rikiɗe tsaban jaraba saboda duk abun da ya faru tana hange daga cikin mota, shiyasa lokaci ɗaya ta fito ta isa gaban su, kuma bata yi wata-wata ba ta kwashe Zahra da maruka har guda biyu, cikin tsananin kishi da ɗaga murya take cewa, "ke dan ubanki wace ce da har kika samu damar yin magana da Mijina? Karuwan banza karuwan hofi ba'a faɗa miki mijin wata bace...?"
Tsawa Malik ya daka mata yana cewa, "ke Nawwara kina da hankali? Wannan wanne irin hauka ne?"
A zuciye ta kalle shi tace, "hauka kace ko? Dama abun da kake son zuwa kayi kenan shiyasa ka taho damu nan? To asirinka ya tonu wlh zaka ga hauka yanzu." Kafin su farga har ta ciro takalmin ta me tsini ta kwaɗawa Zahra da ke tsaye ƙiƙam al'ajabin abun da Nawwara tayi mata ya cika ta, sai ji tayi ta sake buga mata takalmi a saman goshi
Lokaci ɗaya ta saki ihu tana duƙewa a wajen; nan da nan jini ya soma tsatstsafo mata
Salatin mutane ya karaɗe wurin; har Malik da jikinsa lokaci ɗaya ya soma rawa tsaban ya rikice.
[17/07, 10:35 am] OumƊahirah نفيسة: 🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*RUƊIN DUNIYA!*
🌍🌍🌍🌍🌍🌍
*NA_NAFISAT ISMA'IL LAWAL*
_UMMUDAHIRAH_
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT🧝*
*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION* 🌞
```( WE AIN'T PERFECT, BUT WE'RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS💪)```
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
_________________________
*BABI NA GOMA*
_______________Da sauri Malik ya duƙa yana kamo hannun Zahra cikin tashin hankali, yayinda ya kai dubansa kan goshin ta da ke fitan jini, ya kasa ma furta komai sabida halin da yake ciki illa bin wurin da yake yi da idanu
Nawwara kuma na tsaye a kansu ta ƙi mayar da takalmin sai huci take yi
Yayinda wasu daga cikin jama'ar wurin har sun iso sun tabaibaye su suna faɗin, "subhanallah.. meyasa zata yi mata haka? Me ya faru?" Duk laifin sun ɗaura a kan Nawwara tunda a kan idanuwansu suka ga komai, sai faɗa suke mata a kan, "bata kyauta ba, idan wani abun ya haɗa su ai ba sai ta kai ga haka ba."
Sai dai ita bata damu da jama'ar ba kuma bata damu da surutun nasu ba, baƙin cikinta yanda Malik ya duƙa yana taimakon Zahra, shiyasa cikin zuciya da ya ɗebe ta kamar wata me Aljanu ta soma hauka a kan, "sai ya saki Zahra sun wuce, bai isa ya taimake ta ba wlh." Ta riƙe shi gam tace, "ta rantse da Allah bai isa su wuce ta a nan wajen ba sai dai su tafi su bar Zahra, bazai taimake ta ba." Har da kukan ta
Abun fa ya ba wa mutane mamaki ganin kishin hauka ƙiri-ƙiri da ake yi a gaban su, tamkar bata da tausayi
Shi kuwa Malik da ya san halin Nawwara kuma ya san me zata iya aikatawa, bai yi mamaki ba kwata-kwata, sai dai bai san cewa rashin imani da baƙin kishin nata zai iya rufe mata idanu ta aikata wannan haukan a kan abun da bai kai ya kawo ba, sai ya daka mata tsawa yace, "ta sake shi ko ya illata ta."
But wlh ta ƙi, sai buɗe masa idanu tayi cikin nuna tijara tace, "na rantse da Allah babu inda zaka matsa da ita, baza ka taimake ta ba, kawai ka kama hanya mu tafi."
Zahra taga abun da ya fi ƙarfin ta wajen wannan sheɗaniyar yarinyar, ita abun ma sai ya zame mata t.v don ta kasa kataɓus, yayinda zafin ciwon ma ya dena shigan ta sabida tsananin mamakin Nawwara, ikon Allah kawai take kallo a wajen ta. Ganin abin zai zame musu matsala sai ta ƙwace hannunta da Malik ya riƙe gam ta ratsa mutane ta wuce da sauri, domin idan ta zauna ganin wannan bala'in zuciyarta ce kawai zata buga jininta ya ƙare a banza, gwara ta soma taimakon kanta wajen tsayar da jinin before ya ƙare, a ranta sosai ta ji haushin Nawwara da ta kasa mayar mata da martani ko kuma ta rama abun da tayi mata, tabbas da ace kanta ba ya zuban jini da an kwashi ƴan kallo don baza ta taɓa ƙyale ta ba, faɗa da suke siyarwa ai ta zo gidan ta ne, sai dai kuma arzikin ta ɗaya Malik da yake ta bata haƙuri kamar zai duƙa mata, ba don shi ba wlh baza ta ƙyale Nawwara ba. Haka ta wuce ta bar su a wurin ana ta zagin Nawwara sabida abun da tayi
Malik kuwa tuni ya wuce wajen motan sa ransa a mugun ɓace ya shige, yana ƙoƙarin tayar da motan ya barta a wajen don abun da yayi ninya kenan, amma sai tayi saurin shigowa sabida fahimtar abun da yake ƙoƙarin yi, bai bi ta kanta ba ya ja motan a guje ya bar wurin zuciyarsa na ƙara tafarfasa kamar zai ka dasu a hanya, baƙin cikinsa da bai amshi Numban Zahra ba
Ita kuwa Nawwara ko a jikinta sai ma gyara zama da tayi tana kallon hanya, zuciyarta fari tass domin ta san koda wasa bazai ƙara mata irin haka ba, idan ma yana tunanin yi a gaba to dole zai tuna da abin da tayi mishi yanzu ya fasa, ta tsani a rayuwa ta ganshi tare da Mace kuma dole ne ta riƙa ɗaukar mataki, ita kaɗai ce tashi bai isa yayi mu'amala da wata Mace bayan ita ba
Har suka kama hanyar Kano amma Malik bai yi mata magana ba, kuma bai tsaya a ko'ina ba bare su samu wani abun su ci
Ita kuwa jin yunwa ya ishe ta sai ta soma mishi ƙorafin, "yunwa take ji."
Wani kallo da ya watsa mata sai da hanjin cikinta suka kaɗa. Yana shirin yin magana wayansa tayi ƙara, haka ya ɗauka ya kara a kunne ganin sunan Mummy
Tambayarsa take Yi, "har yanzu basu kai ba?" Saboda ta kira waya can an ce basu je ba
Yanda yake jin mugun ɓacin rai daƙyar ya iya buɗe baki yace, "mun kusa kaiwa Mummy, motan CE ta samu matsala."